💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .
💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦_Story and writing by_
ZAINAB HABIB
(mom islam)My wattpad momislam2020
My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2
Zainabhabibu713gmail.com
*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION💦*
EPISODE 43 & 44
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Ɗakine rantsatse mai kyau kasancewar makarantar tasu ba a cikin gari take ba shiyasa kuɗin hotel ɗin yayi sauƙi , bayan yayi wanka ya fitoda ragowar ragowar milk ɗinsa da bredi batare da jiran abin haɗawa ba ya hau sha sbda wata masifaffiyar yunwa dake addabarsa , sai da ya cika cikinsa ya yi salolin da ake binsa sanan tunani ya fara yimasa yawo a kwanyarsa , yana da tambayoyi da dama amma yanzu kam bashida mai amsa masa ,dan tunda yazo duniya harya kai ga shiga makarantu dadynsa bai taɓa bari yayi fushi ba yanzu kam kuka ya fara yana cije lips .
Cikin fara'a ya shigo bedroom ɗinta samunta yayi tana duba fuskarta a mudubi kasancewar kanta na kallon abinda ke gabanta ne yasashi shigowa kai tsaye ba tare da yayi magana ba ,kawai ji tayi an rungumo ta a fusace ta juyo da nufin masifa , kwarjinin da yayi mata ne yasata sunkuyar da kai , ɗaukarta yayi cak kamar baby ya maye gurin zamanta ya ɗorata a cinyarsa , wayarsa ce ta fara ruri babu ƙaƙƙautawa tsaki yayi ya ɗauka , da can ɓangaren Sadiq yace " dady ka manta tun jiya mukayi hutu ?da yake shima ɗin ɗan duniya ne Abdallan yace " lla am sorry ai na manta yanzu kana ina ne ?, kuma har ga Allah zuciyarsa bata yimasa daɗi ba tabbas Sadiq zai iya gano komai a dawowarsa hutunnan , Afnan dake gefe yaron ya bata tausayi ta share hawayenta tace " muje mu ɗaukoshi zuwa gobe , duk da zuciyar Abdallah babu daɗi amma hakan bai kasa sashi jin daɗin kalamin Afnan ba , bayan tayi magrib Abdallah yana masallaci sai da tayi isha'i sanan ta kunna whtsapp , ganin wanan number da tafi kowacce ɓata mata rai tayi saƙonni nata shigowa , hankalinta ne ya kar karta gurin ganin hotuna ne ,
Wannan karon taga abinda ya matuƙar girgizata hotonta tagani daga ita sai pant da bra innalilahi Afnan tace " tare da dafe kanta da ya fara sara mata nashiga uku a ina nayi wanan hoton? duba rubutun ƙasan hoton tayi fara karantawa tayi ,
Barka da hutawa matar Alhaji Abdallah kinga wanan hotunan naki ?" to kikayi wasa Abdallah zai gansu da idanunsa garama kibini a hankali Afnan ce ta miƙe ta sakawa ƙofar key kana ta dawo ta zauna taci gaba da ƙarewa hoton kallo tana mamakin har da yaushe ta taɓa wanan shigar , cigaba tayi da karanta saƙon taji budurwar tace " yanzu dai abinda nakeso shine kisa mijinki ya aureni , Afnan jin zancen tayi kamar saukar aradu ,saurin kashe datar tayi tareda dai'daita nutsuwarta takuma shafa powder a fuskarta , jin alamun shigowar Abdallah tayi hakan ya sata ƙara gyara jikinta,Murmishin yaƙe tahau yimasa dan tana tunanin inhr yaga wanan photon to kashinta ya bushe , Abdallah mutum ne mai lura da ankara ,yana ganin Afnan na wanan yaƙen dariya ce kawai baiyi mata ba amma a zahiri baiyi mata kyau ba kuma ya fara tunanin da akwai abinda yake faruwa da Afnan taƙi gaya masa ne , kasancewar da abinda ya dawo dashi ,ya riƙo hannunta tare da rungumota suka nufi kitchen soyayyen dankalin data soya ɗazu ya zubo musu tana rungume a hanunsa suka dawo parlo a baki ya fara bata tanaci tana zuba shagwaɓa ,amma a ƙasan zuciyarta tana fargabar ranar da sharin wanan budurwa zai hau kanta , kawar da zancen tayi kar Abdallah ya ganota."
Kwance yake yanata saƙa da warwara shin ko ya amince da maganar mama na auran Uwani ne ? wata zuciyar ce tace " aikuwa da ka auri ciwon kai , dafe kansa yayi dan yama rasa tunanin me zaiyi wanan wace irin jarabwa ce ? ya tambayi kansa , tashi yayi ya dawo palo kallon palon ya shigayi yaushe rabonsa da shara , tsaki yaja kana ya koma bedroom ɗinsa ya shiga toilet ya watsa ruwa , yana fitowa ya zauna nanma dai tunanin ne ya addabi zuciyarsa , badan yaji ance Afnan tayi aure ba da babu abinda zai hana ya dawo da ita , wasu siraran hawaye ne suka zubo masa , sharewa yayi ya fara shafa mansa mai ƙamshi , bayan ya gyara sumar kansa ya feshe jikinsa da turare , yaje gaban drower buɗewa yayi ya tsaya a gurin yana tunanin kalar kayan da zai sa tuno kalar kayan da Afnan takeso yayi wato farin boyel da farar baƙar hula da takalmi baƙi sai agogo fari , bayan ya sa ne ya dubi kansa a mudubi yai wani murmishi wanda ya ƙara fito da ainihin kyansa can kuma ya dake tare da ɓata rai , to wa nayiwa wanan kwaliyar ? hhhh lol niko nace Uwani ...key ɗin mashin ɗinsa ya ɗauka tare da rufo ƙofar ya nufi waje ,Faty da ta fito daga maƙota ganin Haisam ya tuno mata da Afnan hawaye tabb ƙwayar idonta ta shige gida ,Haisam bai lura da abinda ke wakana ba yaja mashin ɗinsa ya nufi gidansu mama , dan yanason zuwa gurin aiki da wuri.
Da isarshi anguwar tasu ya hango Uwani taci ɗamara tana shirin faɗa da wata budurwa wacce a shekaru ta zarce ta amma tana shirin faɗa da ita taɓɓ , Haisam ne ya jinjina kai kana ya tada mashin ɗinsa ya nufi gida , yana shiga ya sami baba a kan kujera ƴar tsugunno yana shan kunu , baba na ganin Haisam ya hau washe baki yana fara'a , durƙusawa Haisam yayi ya gaida baba amsawa baba yayi yace ka shiga ciki a zubo maka kunun naƙoshi Haisam yace " tare da miƙawa baba dubu biyar , baba zai yi magana Haisam yace" baba kayi shiru kawai ,share hawaye baba yayi kana yace " Allah yayi maka albarka Allah ya baka mata tagari Allah ya yalwata arziƙinka , dajin wanan adu'ar sai da jikin Haisam yayi sanyi sosai,
Saurin miƙewa yayi dan kar mama ta ritsashi a gurin , kasancewar da tazara kaɗan tsakanin gurin da baba ke zaune dakuma ɗakin mata , yasa Haisam wucewa can kukan Uwani ya jiyo da robar ɗibar ruwa yayi gashi robar a fashe ,dariya ce taso kuɓuce masa sai ya gimtse , Uwani ce ta kalli Haisam da yabata haushi a rayuwarta ta tsani abu ya faru da ita aƙi jajanta mata tace "ɗan yaya ɗan gayu wlh kayiwa wanan yarinyar magana dan ni ba sa'ar wasanta bace tamm,
Kallon inda take magana da girgiza yayi bai ce mata komai ba ya nufi ɗakin mama , shiga yayi ya zauna kasancewar ta shiga wanka , Uwani da baƙin ciki ya isheta kasa zama tayi a ɗakin tayo waje , mama ce ta hangota a zaune bakin ƙofa tana bubuga ƙafa alamun masifa , a ' a Uwani me kuma ya faru?" fashewa tayi da kuka tace " ina cikin ɗibar ruwa a famfo shine wata gardiyar budurwa tazo ta janye bokiti na tasa nata ,shine nikuma na janye nata shine suka yimin taron dangi harda fasamun bokiti , Haisam tun yana dariya a ciki ciki bai sani ba ta yanzu harda ƙya ƙyatawa maganar yarinyar na sashi dariya