💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍*LAMARIN ƘADDARAR AURE NA!!!* .
💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦_Story and writing by_
ZAINAB HABIB
(mom islam)My wattpad momislam2020
My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2
Zainabhabibu713gmail.com
*WANAN LITTAFI GABA ƊAYANSA SADAUKARWA NE GA SHUGABA*
*(ANTY HAUWA MAMAN USWAN)*
*ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA*
*💦AREWA WRITERS ASSOCIATION*💦
EPISODE 33 & 34
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Kasa tsayuwa tayi a gurin saboda wani jiri dake ɗibarta ta durƙusa kan guwaiwar ta tana kuka mai tsuma zuciyar mai karatu oh ni ƴa su ina zansa kai na ,rarrafowa gabansa tare da sunkuyar da kanta ƙasa tace "dan darajar iyayenka ka yafemin wlh ba 'ason...!!! wani wawan mari ya wanketa dashi kana ya miƙe tsaye yace "kar in dawo in samu kina gidannan wlh sai kinyi dana sani , ya fice zuciyarsa na suya , driving yakeyi amma hankalinsa a tashe yake ,ikon Allah ne ya kaishi gida , ko horn baiyi ba ya buɗe murfin motar ya fice tare da buɗe get ɗin , mai gadi dake zaune a wata farar kujera ta roba ganin Abdallah ya shigo a fusace ya miƙe yana cewa Alhji barka dai ywwa kawai yace ."
Bai jira ƙara jin wata maganar ba ya shige ciki , mai gadi ne ya jinjina kai ya ƙwalawa driver kira da sauri ya taho sabda shima ya lura da yanayin Alhajin ."
Wangale get ɗin yayi ya shigo da motar, sukazo suka zauna kafa hirar shigowar uban gidan nasu ,
Bai sameta a palo ba ya nemi guri ya zauna , kashe tv da yaketa ƙararsa shi kaɗai yayi , ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya abubuwan da suka faru tsakaninsa da momyn Sadiq suka fara dawo masa ..
Cikin zuciyarsa yace " ko kaɗan banyi dana sanin rabuwa dake ba dan bansan ko bada ni kaɗai kike taraiyya ba .
Shigowar Afnan ce ta sanyashi katse tunanin tare da faɗaɗa fara'arsa irin karta gane yana cikin wani hali , takowa takeyi cikin isa da ƙasaita ,
kai kace ƴar wani sarkin ce ."Zama tayi gefensa tare da ratayo hanunta a kafaɗarsa tace "lafiya mijina ? naga kamar kana cikin damuwa " a'a Afy kaina ke ciwo yanzu ma so nakeyi na ɗan kwanta ..
Badan ta yarda ba ta ƙyaleshi amma ta fuskanci akwai abinda yake damunsa jikinta a sanyaye tayi bedroom ɗinta ta fashe da kuka ,
jiyo kukan yayi lokacin da zaiyi hanyar bedroom ɗinsa ya dawo zuwa ɗakin nata , dole ya jata gado ya rungume ta yana jijiga ta kamar baby har bacci yai gaba da ita .
Ajiyar zuciya ya sauke can kuma sai wasu zafafan hawaye suka sauko daga idonsa , kallon sa ya kai ga Afnan dake ta bacci hankalinta kwance amma fuskarta duk alamun hawaye gasunan ..
In ya tuna Sadiq ba ɗansa bane sai ya saki wani mahaukacin kuka mai ban tausayi , yana cikin hakan ne yaji ring ɗin wayarsa ..
Kasancewar ya bar wayoyinsa a palo ya miƙe a hankali ya isa gurin wayar da ɗaga warsa, my son yagani sai da yakuma zubar da hawaye sanan ya ɗaga wayar, kafin yayi magana yaji Sadiq yace "dady na koma school fa gashi yanzu banida wasu kuɗi a hanuna , jimm Abdallah yayu can kuma yace "zan tura maka zuwa anjima inna fita , nagode dady Sadiq yace " lokacin da Abdallah ya jiyo ƙarar tafi da dariyaku ya kashe wayar , kirane yakuma shigowa a karo na biyu Abdallah ya ɗaga a fusace yace "wai lafiya ?am dady wayar momy ce tun jiya a kashe dan Allah in kuna kusa ka bata , bana kusa Abdallah ya bashi amsa a taƙaice ya kashe wayar duka ma."
Lefin momynsa yana neman shafarsa ko da yake yanata shawara da zuciyarsa akan ya fito ya faɗawa Sadiq ba shine ubansa ba sai kuma ya kawar da tunanin , ya shafe mimtuna a gurin yanata tunani iri iri amma babu wata mafita da yaga ta dace , kwanciya yayi a doguwar kujerar tare da ɗaga kansa sama , yau ɗinnan a tunani ya ƙare , bayan Afnan ta tashi tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga baƙa mai adon faraten dutsina ba ƙaramin kyau tayi ba , samun Abdallah tayi kwance a palo bacci ya ɗaukesa gashi lokacin ƙarfe shida na yamma , kasa tashinsa tayi kwai ta miƙe tayi hanyar kitchen,
Abinci mai sauƙi ta yi doya da miyar ƙwai dan yau tunda taga mai gidan babu walwala take jinta babu daɗi , tana gamawa ta dawo palo ta zauna gefensa tana shafa fuskarsa a hankali , buɗe ido yayi yana salati "ana kiran sallah fa , oky yace "tare da miƙewa ya nufi hanyar toilet , bin bayansa da kallo tayi tana mamakin sayawarsa daga fitarsa zuwa yanzu , kodai wani ya ɓata masa rai ne ? ta tambayi kanta , dawowarsa ce yasata ɗago kai tare da cewa Allah ya tsare amen yace "yasa kai ya fice....✍️.
Babu sharhi 🤨?.