page 1

233 13 3
                                    

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
   ( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*
 
    *By*

*FIDDAUSI* *SANI*
      (damsel feedorh)

🅿️:1️⃣

Dan dazon mabarata ne cike da 'kofar wani makeken gida ,dukkanin su a zaune suke ,kamar dahadin baki kuma duk suke tashi taye ga alama mai gidan ne xe fito ,se turereniya sukeyi ,kamar daga sama saiga wata matashiyar yarinya ,kutse kawai takeyi a cikin jama'a ita birinta baiwuce taganta a gaban layiba saboda tasan ta hakane kawai zata kusanci ganin mai gidan ko matar gidan domin bata damu se mai gidan ne zata gani ba ko matar tagani tasan ta wadata.

   tana isowa a gaban sahun se taja ta tsaya ,sedai abun mamaki duka tsofaffine a wurin babu yaro ko daya ,kuma ga Alama ba yaune tasaba zuwa ba domin matan nan babu wacce tayi complain akan abunda yarinyar tayi

sai wani zare ido take kamar wacce tayi karya ,sunfi 30 minutes a wurin sedai babu alamun cewa masu gidan zasu fito ,hakan ne yasaka jikinta yayi sanyi ,sega hawaye masu zafi suna bin kuncinta ,wata tsohuwa da take taye kusa da ita ta dafata "kiyi hakuri Ameerah,ga alama yau ma masu gidan basanan ,amma kekam ina iyayenki da sukabar yarinya kamarke kina yawon bara, ai da sun sani zaunar dake sukayi a gida sukuma sufito ,saboda yanzu duniyar nan babu gaskiya wani ze iya anfani da dukiyarsa ya lalata miki rayuwa ,duk maganar nan da take hankali Ameerah baya gunta domin ta tafi duniyar tunanin hanyar da zata sadata da mai gidan

Saida tsohuwar ta girgizata ,tukuna tadawo hayyacinta ,murmushin yake tayi tace " karki damu Innah gobe ma zan dawo ai mainema baya gajiya ,daga daga haka tajuya da nifin komawa gida ,itadai matar nan da ido kawai ta bita saboda tarasa gane me yarinyar ke nufi itadai idan kaganta bazaka kirata *MABARACIYA* ba domin bata tattre da wahala irin na mabarata ,gashi ita mai tsabtace "ya Allah ka wadatamu abunda ta fada kenan.

Saida Ameerah tayi nisa sosai tukuna ta juyo sedai bata hango kowa ba a bakin gidan ,murmushi kawai tayi batasan me yasa ba ko yaushe tazo wurin zata sami mutane da yawa a bakin gidan ,amma kuma da ta tayi nufin barin wurin se kowa ya watse ko meyasa haka,tambayar da takeyiwa kanta kenan sedai bata da mai bata amsa,wuri tasamu ta sauna tana tunanin wace hanya zatabi shin domin samun cikar burinta ,tabbas bazata dakata ba harse ta cimma manufarta , tacikawa yayarta alkawarin da tayi mata ,kuma dole se ta dauki fans a akan  Saudahhhh....

#shin wacece Ameerah kuma wacece saudah wane burine takeson cikawa

Comment dinku shi ze bani tabbacin labarin yakarbu

#followme on wattpad@damselfeedo

Real@bazamfaria💙

It's ur Feedorh

MABARACIYAWhere stories live. Discover now