page 18

54 2 0
                                    

dafa kafaɗarta Aunty tayi cikin sanyin murya tace "Meerah bawai ina so na hanaki ɗaukar fansan abinda akayi Miki bane ,saboda addini ma yabamu wannan damar idan har aka cuceka kuma kaga bazaka iya yafewa ba to ka rama daidai da yadda akayi maka ,sedai kituna irin tanadin da Allah yayiwa masu yafiya musamman a inda sukeda halin ramawa, Meerah inajin tsoron faruwar wani abu gareki Hajia saudah da kike gani ba ƙaramar mace ba kuma mijinta ma babban mutum ne na tabbata koda za'a kamata da lefin fasa kauri da yara mata tofa babu wani hukunci da zata fuskanta ,domin su sukeda doka , Allah ne kawai xe iya hukunta su bawai dan'adam ba musamman ke mace karama me rauni ,karkiyi wasa da rayuwar ki bamuda kowa se Allah.

Shiru Meerah tayi tana sauraren Aunty har seda tayi shiru ,alamun ta gama maganarta,murmushi tayi harseda fararen haƙoranta suka bayyana ,cikin salon maganarta tace " Aunty naji daɗi da kika ce Allah ne ce iya hukunta ,ki fahimceni bawai inason yaƙar ta bane ko kuma burin fansa ne kawai a gabana ba , a'a inaso ne na nuɓutar da sauran yaran da take ƙoƙarin halakarwa na kuma bayyanar da ɓoyayyiyar fuskanta wacce take cin amanar addini ,mutane da yawa suna yabonta akan kirkin ta har takan ɗauke wasu daga cikin yaran marasa ƙarfi da sunan zata tallafi rayuwar su wanda babu wanda yasan me take sakasu sunayi ,kasuwanci takeyi dasu

Saboda haka temako ɗaya nikeso kiyimin Aunty shine kitayani da addu'a Allah yabani ikon cin nasara akanta"

tana gama faɗar haka bata jira cewar Aunty ba ,tayi shigewar ta ɗaki, girgiza kai kawai tayi saboda tasan halin Meerah da naci akan bu tunda har tayi niyya to babu wanda ya isa ya dakar da ita.

Washe gari tunda tayi Sallahr asuba bata koma bacci ba dan haka tafita tayi share² sannan tayi wanke² seda ta gama tukuna ta shiga wanka ,bata ɓata lokaci ba saboda saurin da takeyi kar ta haɗu da rashin mutuncin Rufaidah ,yau kam doguwar rigar atamfa ta saka babu lefi da ɗan haske ta duk da ta koɗe amma tafi kayan jiya haske ,ko mai bata shafawa jikinta ba ta ɗauki hijabinta tsoho shima ta saka ,a bakin ƙofa ta haɗu da aunty tana shirin shigowa ɗakin ,ɗan matsawa tayi daga gefe tana murmushi ta gaisheta " bade har zaki tafi ba gashi na makara daga na gishingiɗa bacci ya ɗaukeni" murmushi ta sake yi tace " karki damu Aunty ,ai dama za'a riƙa bani abinci a can yanzu idan nace na tsaya zanbata lokaci ,ga yarinyar batada kirki"to shikenan kide kula dan Allah ,kikama mutuncin ki kuma Allah ya kiyaye se kin dawo "Insha'Allah Aunty Nagode" daga haka ta fita gidan , cikin natsuwa take tafiyar ta kamar yadda ta saba seda tayi nisa sosai kafin ta samu a caɓa ,ka san cewar safiyace sosai,unguwar da xe kaita ta faɗa masa ,babu ɓata lokaci tahau suka tafi.

Koda ta kai sa sashen su Rufaidah a rufe yake alamar bata tashi ba kenan ,tasan ko tayi knocking ba ji xatayi ba saboda haka ta samu wuri daga gefe ta zauna ,takai kusan 30 minutes,kafin taji maganar Larai a kanta ,ɗagowa tayi tana kallonta " Fatima me kikeyi anan baki shiga kin fara aikinki ba?"instead ta amsa mata se tayi murmushi tare da gaisheta, amsawa tayi tana sake maimaita tambayar " wlh Aunty Nazo naga kofar a rufe shine na tsaya nan kafin a buɗe"

Kama hannunta Larai tayi tace " to ai tanan baya zaki shigo ,mutafi kina ɓata lokaci ,bakisan halin me gidan bane"Meerah batace komai ba tabi Larai suka shiga ,tsaye tayi tana tunanin inda zata fara gyarawa ,can dai tayanke shawarar fara gyaran falo kafin  fitinanniyar  can ta tashi ,se ta shiga ta gyara mata ,sunan da ta sakawa Rufee kenan.

Seda ta tabbatar da ta gyara ko ina a downstairs,tukuna ta kai dubanta ga agogon da ke manne a bangon falon karfe 8:30 ya nuna mata ,a fili ta furta " ko ma tayi sallah? sedai tunanin batada me amsa matane ya sakata nufar kitchen wurin Larai " sannu da aiki Aunty" murnushi Larai tayi mata " harkin kammala gyaran kenan " ehhh iya kasanne da ɗakunan da ke ciki ,ina tsoron na haura sama ne bansani ba ko bata tashi bacci ba" cab!ai se 10 zata tashi " taɓe baki Meerah tayi tace " to bara na tayaki aiki kafin ta tashi" a'a wlh da kin barshi ai ma na kusa kammalawa,kunun gyaɗarnan ne kawai yayi saura "ehhh ai ko wanke² ne se nayi Miki ,naga kinyi abincin kashi²,hala duka gidan ke kike musu a binci? " Hmmm ko ɗaya Meerah kinsan musu kuɗin nan sam basu san tattali ba duk wannan da kikaga nayi na Hajia Rufaidah ne ,yanzu ma idan ta gadama zata iya cewa duk babu abinda yayi mata ,sedai na canja wani" cike da mamaki Meerah ta kalli Larai tace " kuma se kin sake ɗin? "to yarnan zamanta nikeyi a gidan nan fa dole na canja idan tace beyi mata ba" can!amma wallahi....bata karasa ba sakamakon tsawar da sukayi from no where,cikeda rashin mutunci Rufaidah tace........

More comments more typing

Idan har comments ɗin ku ya burgeni to zakuci gaba da samun Mabaraciya ko yaushe Insha'Allah

Vote and follow me Dan Allah

Real Bazamfaria❤️

MABARACIYAWhere stories live. Discover now