*INTELLIGENT* *WRITERS* *ASSOCIATION*
(On ward together)*MABARACIYA*
*Story* *and* *writing*
By*FIDDAUSI* *SANI*
(damselfeedorh)🅿️:1️⃣4️⃣
,,,,,,,,Washe gari Rufaida da kanta ta kira Fatima a waya sosai tashiga mamakin ganin kiranta sedai ba ta nuna fa ,daga can Rufaida tace "Fatima ya naji shiru? Murmushi ya subucewa Fatima ba tare da ta shirya wa hakan ba har seda Rufaida taji sautin shi ,cike da mamaki tace" yadai kike dariya ? Dole ne nayi dariya Fatima wai kinsan yarinyar nan taso ta ganeni"wace yarinya ta tambaya ,don ita har ga Allah batasan akan wacce take magana ba
"Mabaraciya ,Fatima tabata amsa a takaice " ok to yanzu ya kukayi da ita " ehhh to kinsan ko cikin talakawan wasu basuda kwadayi da fari yarinyar da mahaifiyar ta kin amincewa sukayi wai ita bazata seda mutunci 'yarta saboda kwadayin abun duniya ba ,shinefa na samu mahaifinta ,na nuna masa irin Alkhairan da zasu samu a cikin aikin nan ,tukuna yayi tsayin daka akan dole se tayi aikatau ,cikeda jin haushi Rufaida tace " wai me suke takama da shi nikaina idan badan saboda na dauki fansa bane me zanyi da aikin ta yanzu ma kawai inaso na koya mata darasine ,idan na fahimta halin uwarta ne ta gado na ganin dede suke da kowanne'dan adam , murmushi tayi mai sauti cikeda jin ita din watace tace " point of correction cox totally akwai distance sosai a tsakanin mu , mabaraciya wacce abunda zataci ma se tayi yawo ta nemo kuma hakan wai iyayenta da ita suka dogara ta zame musu bango ,dole zan nuna mata wacece ni 'yace wacce ko kiran sunan mahaifiyata akayi dole mutum ya natsu domin yasan ta Tara abun duniya despite my father
Shiru itadai Fatima tayi tana sauraren ikon Allah ,a ranta take tunanin wane irin girman kai da takama ne ke damun Rufaida,tabbas rayuwar wasu a kwai gyara ,duk da ta ta'allaka hakan da rashin samun rarbiyar uwa da batayi ba ,kowa yasan Hajia Saudah yakuma san irin Alkhairan ta ,da yanda take taimako da son jama'a ko kadan Rufaida bata gaji halinta ba Farar tukunya kenan mai fidda ba'kin tuwo ,Fatima na cikin wannan tunanin ne tani 'kit alamun ta yankee kiran ,bin wayar tayi da kallo tana tunanin shin wace kaddara ce ke kiran Meerah aiki a karkashin wannan da bata gaji mutum ci ba ,tana cikin tunanin ne wayarta ta sake ringing ganin sunan Meerah ya sakata dagawa ,da sauri ,tambayarta Meerah tayi akan yaushe zata fara zuwa " even tomorrow,tabata amsa jiki a sanyaye ,wani irin dadi Meerah taji ,sosai tayiwa Fatima godiya sanann ta yanke kiran
Meerah na zaune dakinta tayi tagumi ,da alama tunani takeyi ,shigowar aunty ne yasakata dawowa daga duniyar tunanin ,kallonta tayi tasakar mata murmushi tare da matsawa daga gefe saboda ta samu wurin zama " kinga ba zama ne ya kawoni ba ,aikenki nakeso nayi kasuwa,sedai naga yamma tayi ina tsoron kitafi kiyi zamanki nasan halinki " kai aunty se kace wata yarinya ,da zan tafi na zauna a titi ,kedai kikawo sakon kawai yanzunnan zan dawo Insha'Allah " yawwa to kishirya se ki sameni a 'dakina aunty tafada tana fita dakin ,tashi Ameerah tayi kayan jikinta kawai ta sauya daga riga da wando zuwa bakar jalabiya sosai tayi kyau ,kamar ba Meerahn da na Sani ba saboda sak ta fito yar gayunya harta yane kanta da dan karamin vail na rigar sekuma ta sauya zuwa hijab red colour Masha'Allah Allah ,tayi kyau sosai abunda ,cikeda na tsuwa ta shiga dakin aunty ,sakin baki aunty tayi tana kallonta har seda tayi kasa da kanta don taji kunyar kallon da aunty ke binta da shi
Cikeda xolaya Aunty tace " Masha'Allah Meerah kinganki kuwa ,idan a hanya na ganki ai bazanxe wannan Meerah ta bace tafada tana dariya ,Dan turo baki Meerah tayi tace" idan da bansan halin aunty na ba da se tafasan kai ,bani sakon nidai natafi ,dariya kawai Aunty tayi ta dauko kudin sakon tabata tare da fada mata abunda zata siyo ,sallama tayimata sannan ta tafi
Adaidaita sahu ta shiga kasancewar akwai dan tazara tsakanin su da kasuwa ,cikin natsuwa tagama siyan duka abunda Aunty tace ,haka ta riko kayan ta nufi titi don samun abun hawa 'a can tsallaken titi ta hango wani mutum yawuce yama tallan a agwalima ,hannu tafara daga mishi alamar yatsaya sedai da alamu sam be kula da itaba ,ganin da tayi kamar babu motorn da ze wuce kusa yasakata saurin tsallakawa ,sedai tun kafin takai tsakiyar titi ta sake duka kayan hannunta sakamakon wani uban horn da yacika kunnen ta duk tabi ta rude ta kasa yin gaba ta kasa yin baya ,sedai tayi tsaye tare da saka duka hannunta biyu ta toshe kunnen ta ,fitowa mutumin da ke cikin motorn yayi ,fuskar shi a hade da alama tabashi haushi sedai kai tsaye bazaka fahimci hakan ba ,tana nan toshe da kunne sedai taji anja hannunta ,anyi gefe da ita cikeda mamaki ta dago dan ganin waye ,sedai har yayi gaba abunshi yana kokarin shiga motorn shi "am sorry ya tsinkayi siririyar muryarta wacce ke nuna har yanzu acikin tsoro take ,dan waigowa yayi sedai karaf idonsu yahade cikin na juna ,bin junan su da kallon sanin suke sedai sun kasa tuna a ina sukasan juna " she damn cute ya furta can kasan makoshi ,saurin janye idonta kanshi Meerah tayi tafara tattara kayan ta da suka watse.........
#Vote and follow me@ damselfeedo
#Real#Bazamfaria