page 8

53 7 0
                                    

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
   ( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*
 
    *By*

*FIDDAUSI* *SANI*
      (damsel feedorh)

🅿️:8️⃣

,,,,,,,,Har kofar gida aunty tabiyota sedai koda ta fito ko inuwar Meerah bata ganiba ,haka tadawo cikin gidan jiki babu kwari tare da addu'ah Allah yatsareta

Meerah kam bata tsaya ko ina ba se gidan wata kawarta tafiya tayi sosai a kafa amma kasancewar kamar ba'a hayyacinta take ba shiyasa bata ji nisan ba ,abakin get din gidan ta tsaya tana karewa gidan kallo ,rayuwar ta tabaya ta tuna kafin iyayensu su rasu take taji wani kwallah ya zubo mata ,knocking tayi ,mai gadi ya leko "sannu baba dan Allah Fatima tana nan? Seda yakare mata kallo tukuna yace " ehhh amma waza'a ce mata tazo wurinta " kace mata Ameerah Almustapha ,koma yayi babu dadewa segashi ya dawo ya bude mata kofar ta shiga ,direct main house din ta nufa kasancewar tasaba zuwa gidan kafin rayuwa ta sauya mata ,tana shiga falon taji anyi hugging dinta so tight ko ba'a fada ba tasan Fatima ce ,dariya tayi tace "ashe baki manta da niba tafada tana Jan hannunta suka karasa kun kujerun falon.

Zama sukayi cike da jin dadin ganin ta Fatima tace " nayi zaton shikenan bazan sake ganin ki a idona ba Meerah where all this have you been? " Labari ne mai tsawo kedai bani ruwa nasha tashi Fatima tayi tana fadin " yi hakuri murnar ganin ki ne ya mantar da ni ,juice ta doro tare da ruwa a tire agabanta ta ajiye se kuma ta koma ta dauko snacks tana dariya tace " nasan har yanzu kina nan da shegen rason cin abinci se kayan snacks ,daria kawai Meerah tayi a ranta take fadin ,bakisan yanda rayuwa tayi dani bane yanzu komai nasamu ci nake ,a zahiri kuwa murmushi kawai tayi tare da fadin "tanx

seda ta 'dan sha lemun tukuna tace " nikam wai ina Momy? 

" Momy tafita wai 'yar kawarta zaakawo wa lefe shine suka tafi taron kayan amma ai nasan zata dawo kafin kitafi ,don lokacin kullum se ta tambayeni ke ,nace mata nidai tunda su Ummanki suka rasu bansake sanin ina kike ba tun ina zuwa gidanku a rufe har ranar da natafi nasamu wasu mutane a ciki sukace wai wani ne ya siye gidan yabasu haya ,to alokacin nayi tunanin ko dangin kune suka 'dauke ki inata sa ran ki kirani tunda kinada number din Momy amma shiru

"Bari kawai Fatima yanzu ma tambayarki zanyi nasan kinsan gidan Alh Yusuf tsoho tayi maganar da sigar tambaya " ehhh sosai ma kuwa domin Momy tana aikina gidan uwar gidan da ce kawarta ,wani irin dadi Meerah taji alamun zata samu abunda take nema kenan

"Amma me yafaru kike tambayata ? taimako zakiyi min dan Allah ,cikeda rashin fahimta Fatima tace name fa ? So nakeyi ki samu kusanci da 'yar Hajia Saudah ,zare ido Fatima tayi tace " ki rufan asiri yarinyar da takejin warin mutane ,kinga kuwa irin kallon 'kaskanci da takeyiwa jama'a ,ko ba haka ba ma ni bantaba zuwa sashen su ba bakina bangaren su yaya mu'aiseen shikam sunada kirki har siblings dinsa ,amma ke me nene dalilinki naso na samu kusanci da Rufaidah?  "Ok sunan yarinyar kenan? Meerah ta tambaya " Fatima shin kinsan dalilin kauracemiki da duk sauran 'kawayen mu da nayi to bakomai bane se dan yanzu banda kowa se Allah narasa gatana duk da nasan hakan yana daga cikin jarabawar rayuwa ta ,shiyasa banaso ina kusantarku domin gada jin dadin da kukeyi yasakani butulcewa ubangiji akan jarabtar da yayimin ,kama hannun Fatima tayi tana kuka tace "fatima Hajia Saudah da kike gani ita ce silar shigana wannan halin ,alhakin ahalina yana kanta banso na fada miki ba a kwai sirrin da ko auntyn da ta dauki dawainiya ta yanzu ba tasan dashi ba nabarshi a raina ,tare da da burin fansa

Cikeda tausayi Fatima tace " yanzu idan nasamu kusanci da Rufaidha se me kuma ? Kedai kiyi wanann matakin nasara na farko ne wanann abun banikadai zaki temaka ba wlh Fatima rayuwar yayan mutane da yawa ta lalace duk a sanadin Sauda daga ciki harda yaya Maryam nasan bakisan dalilin mutuwarta ba ,amma kitemaka kimun wannan " namiki alkawari Ameerah zan yi iya kokarina domin ganin namiki wannan bansan dalilin ki ba amma naji ajikina koma menene to mai kyau ne ,domin Meerah da nasani bata sharri ,murmushi kawai tayi tare da fadin " kika sani ko yanayi ya sauyata ,bari natafi gida gada aunty na ta nemeni

"to yanzu a wane unguwa kike " babu nisa inanan tudun wada  "kai amma bakida kirki ,ashe ma kina kusa dani amma shine kika manta ni yanzu dai kibani No dinki duk yanda akayi se na kiraki amsar wayarta tayi tasakamata ,harbakin get Fatima ta rakata tare da yimata godiya " tunda kinki bari Momy tazo taga yanda Meerah slim tazama ,dariya sukayi dukansu.....




Follow me on wattpad@damselfeedo

Yuh can drop ur comment via my watsap no
08039228702

#Real@Bazamfaria

MABARACIYAWhere stories live. Discover now