"Larai badai abincin da zanci bane kika bari wannan me suffar aljanu ta taɓa?" A'a ranki ya daɗe yanzun nan ta shigo ma har na kammala komai" itadai Ameerah tsaye tayi tana binsu da ido musamman Larai da jikinta har shecking yake tsabar tsoron Rufaidah,wani dogon tsaki taja tana maida idonta kan Meerah a wulaƙance tace " shishigin ki babu abinda ze ƙara Miki se tsana a xuciyata,idan ma ba kinraina ni bane har yaushe zakizo baki jira na tashi bacci kin gyara min ɗaki ba ,kishigo nan kina abinda ba'a saka ki ba ,ok nasan saboda kwaɗayi kikayi wannan ko wato agama ki kwasa kikaiwa cima kwance iyayenki ko,su sun zauna sun turoki aikatau wayasani ma ko da shegen kyan nan naki zasuyi anfani kun zata ko akwai maza a gidan nan ,to ahir ɗinku ko munada maza sunfi ƙarfin matsiyata irinku"ta ƙarashe tare da kafe Meerah da ido dan ganin duk wannan maganar da ta faɗa mata murmushi ne kwance a fuskanta kamar ma bata fahimci zagin da takeyi mata ba ,ganin tayi shiru ne Meerah ta raɓa zata wuce ta batare da ta furta komai ba , da sauri Rufee ta fizgota ta dawo baya
" Who dere you ina magana zaki wuce ,wato kam ga Mahaukaciya ko?nan ma shiru Meerah tayi tana kallon ta kamar bazatayi magana ba se kuma tace " Ai bansan amsar abinda kika faɗa kike nema ba shi yasa nayi shiru ,amma tunda har kin buƙaci haka inaso kisani ,duk yadda iyaye suke sunan su iyaye, Bara na tambayeki menene ma'anar iyaye? nasan baki sani ba saboda bakisan daɗin su ba ,abinda kika sani kawai ,kinada buƙata abaki kuɗi kiyi ,anfaɗa Miki komai ne kuɗi keyi akwai farin cikin da kuɗi bazasu baki ba ,amma kulawar iyayenki kawai ya wadatar dashi ,kamar yadda kika ce iyayena matsiyata ne to ina so ki gyara kalaminki ,domin mu arziƙin imani kawai da Allah yayi musu ya ishemu alfahari ,kyau da kike magana kuma ,naji daɗi tunda duk rashin sonki gareni ,idonki be rufe ba har seda ya tabbatar miki da Ni ɗin me kyau ce ,Kinga akwai yiyuwar idan gidan da Nazo babu maza to matan ciki su taya ko? Cikin zafin rai Rufee ta ɗaga hannu zata mari Meerah da sauri ta kauce ,tana dariya ta fita daga kitchen ɗin
Ba Larai da tayi mutuwar tsaye ba hatta Rufee ta kasa motsi ,babban baƙin cikinta a gaban Larai Meerah tayi mata wannan iskancin , lalai dole ne ta ɗauki mataki akan ta ,amma zata fara kiran Fatima ta sheda mata kafin suyi shawarar irin tozarcin da zasuyi mata ,dan tayi alƙawarin se tayi nadamar zuwanta duniya.
Meerah kam xuciyarta wasai taketa gyaran ɗakin duk da wani ɓangare na xuciyarta na cikeda tsoron kar Rufee ta koreta, tun kafin ta fara abun da ya kawota ,gashi ma ko maganar Hajia saudah bataji anayi ba bare ta saka ran ganinta ,haka dai ta samu ta kammala komai har toilet ta wanke mata se kanshi ke tashi a ɗakin ta janyo mata ƙofa ta rufe ,har zata sauka se takai dubanta ga ɗayar ƙofar dake rufe ,tanason ta shiga ɗakin duk da zuciyarta na faɗa mata cewar ɗakin Hajia saudah ne ,jin kamar za'a hauro sama ya sakata saukowa da sauri ,sedai a mamakinta Rufee bata falon.