page 7

65 11 0
                                    

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
   ( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*
 
    *By*

*FIDDAUSI* *SANI*
      (damsel feedorh)

🅿️:7️⃣

Tunda sukaji wannan labarin na Hajia se jikinsu yayi sanyi lallai basuda wani mahita da yawuce su mika wuya a gareta ,sedai zasu mika lamuransu ga Allah domin shine buwayayyen sarki sarkin da baya kwana kuma bayada fadawa shine Wanda ze tseratar dasu yakuma basu mafita "kunyi shiru maganar Binta ya katse musu tunani

Murmushin takaici Maryam tayi tace " aunty muna kai kukan mu ga ubangiji ne ,Wanda muka kiyiwa Hajia biyaya saboda tsoron azabarsa sarkin da yaharamta zalunci a tsakanin mu  ,yahane mu da alfahasha ,natabbata baze bar rayuwar mu ta tafi haka ba ,kifadamana tsarin Hajia zamuyi mata biyayya domin mu a yanzu kamar bayine a gareta ,se abunda takeso zamuyi

Murmushi Binta tayi ,tabbas yarinyar tabata tausayi amma dai tasan ko ta halin yane dole yau da gobe wanann takawar da take nunawa zebar zuciyarta ,pointing din 'dayar tayi tace "ita wannan ko kurma ce har yanzu banji maganar ta ba " karki damu sunan ta Nusaiba itadin 'yar kanin babana ne itace yayata ,haka take bamai yawan magana ba ,na tabba ta yanzu halin da muke cikine yasake taba zuciyar ta Maryam tafada tana kallon Nusaiba

" shikenan dai ni shawarar da zan Baku kawai kuyi abunda Hajia ke bukata ,yanzu zaku iya biyoni mutafi gunta domin tabbatar mata da aikinta ya kammala

"Wai ke Ameerah se yaushe ne zaki cire damuwa da tunani cikin ranki ,I have staying almost 30 minuts ,but yuh don't even know ,let gone by gone yuh have to face ur future pls ,banajin dadin ganin yanda kike a cikin damuwar nan why?

Fashewa Meerah tayi da kuka ,cikin murya irin na waanda yake cikin kunci tace " aunty  have  yuh see what i seen ?do yuh know how aunty Maryam did her life with that prostitute women ,she's destroyed her life all for my on life ,only me know how im feel

Cikin sanyi jiki Aunty tace "who told yuh all this? jefa mata wani book dake hannun ta tayi tace " take it you will understand, kurawa littafin ido aunty tayi ,at the top up the cover book anrubuta ,its confidential ,mi'kawa Meerah tayi tace "me yasa kika karanta bayan Maryam batason kowa ya gani?

" My heart tabata amsa , tareda kara fadin "na dade idanuna suna kallon wanann book din zuciyata nagayamin na duba amma danaga ,warning dinta se naji na ga gara saboda banaso ko bayan ranta ace nasaba wa umurinin ta ,ashe mafita ne zan samu yanzu kam nasamu hanyar da zan tunkari Saudah ,nasamu hanyar da zanbi nasamu kusanci da ita ashe da can duk hauka nakeyi ,a lokacin ma da nasamu ganinta ba lallai nayi nasara ba ,amma yanzu zan jure komai
Zan yaudareta ta hanyar da take yaudarar iyayen yara sun yarda da ita ,xan zambaceta kamar yanda take zambatar mutane suna yimata kallon mutuniyar kirki ,tabbas ba yanzu yakamata na shiga gidanta ba ,aunty takira sunanta tare da kallonta ,cikeda mamakin Meerah tace " inajinki " kudi nake nema sedai bansan ta ina zan fara ba mafita 'dayace wadda zanyi anfani da ita ,badan raina yaso ba ,zankarya maganar yayata karo na biyu tabbas zanshiga gidan Alh Yusuf a matsayin mabaraciya ,daganan zannemi aikatau ,sedai matsalar 'dayace ta ina zan fara gidan da baabarin kowa ya shiga ,shiru tayi kamar mai tunanin wani Abu sekuma tafada 'dakinta da gudu, itadai aunty da kallon mamaki tabita ,tana nan tsaye a inda tabarta ,Ameerah tazo ta wuceta ,da sauri tafara kiranta tare da tambayar ina zata je amma ina ko waigowa batayi ba .....

$Mutum ze iya karantamin labarin amma following ne bazeyi ba ,to  na haramta hakan don Allah idan kinsan bazakiyi following dina ba karki karanta wanann kawai na my followers ne

Follow me on wattpad@damselfeedo


#Real@Bazamfaria

MABARACIYAWhere stories live. Discover now