page 2

110 7 0
                                    

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
   ( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*
 
    *By*

*FIDDAUSI* *SANI*
      (damsel feedorh)

🅿️:2️⃣

,,,,,,napep ta tsayar ta shiga fada masa unguwar da xekaita tayi ,sunyi tafiya me dan nisa ,ta sauka

Wani madai-daicin gida ta shiga da sallamarta ,kai tsaye daki tanufa tare da furta " aunty na dawo ,da sauri wacce takira da aunty ta fito tace "Meerah andace? Ajiyar zuciya ta sauke tace " ankusa dai aunty "kinga Meerah nifa da zakiji nawa da kin hakura kinbarwa Allah komai domin kuwa shi ba azzalumin sarki bane na tabbata yaji kuma yagani da sannu sakayyar Maryam ze biyo baya

Seda ta sauke ajiyar zuciya ,cike da rauni tafara magana " tabbas aunty nasani Allah yanaji baya bacci kuma a addinance ma anbamu damar idan  aka zalunceka bazaka iya yafewa ba ,to karama kwatan kwancin abunda akayi maka ,katseta Aunty tayi da fadin " natabbata idan Maryam na raye zata yafe takuma shafe abun a ranta dan Allah Meerah gada kijamana abunda yafi karfinmu ,matar nan tanada iko fiye da tunani zata iya komai saboda mutuncinta ,shin meyasa ke bazaki hakura ba,takarashe maganar tana kafeta da ido ,cike da kwarin gwiwa tace "aunty ,duk wani gata idan ba na Allah bane to ba dawwamamme bane ,bamuda kowa amma muna da Allah saboda haka shine zai taimakeni ,wlh matukar bandauki fansar 'yar uwata ba ,to bazan sake kiran kaina a cikin a halinku ba ,kedai kixuba ido ,ni yunwa nakeji ina abinci na ,girgiza kai kawai aunty tayi tare da fadin " yana da kin ki nakai miki ,Ameerah bata sake magana ba ta nufi dakinta.

Seda tafara watsa ruwa tukuna ta dauro alola bayan tagabatar da sallah ,se ta dauko wani littafi ,ta dade tana kallon murfin littafin ,kamar zata bude sekoma ta maida ta ajiye ,shiru tayi tana tunani can kuma se ta fashe da kuka, cikin kukan ne take suratai " tabbas baikamata ace har kinkai yanzu ban cika alkawarina ba yaya Maryam ,ke Kadai ce gatana kece wacce ta sadaukar da mutun cinta saboda nawa ,kin kula dani kinhani nayi kukan maraici ,tabbas bazan samu sukuni ba se Sauda ta tozarta ,tabbas zan wulakanta ta a idon duniya ,zansa ta fahimci ba komai ne kudi da mulki ke bayar wa Allah yagafarta miki tafada tana kara sautin kukanta ,seda tayi kuka sosai tukuna ta rarrashi kanta saboda bata son Aunty ta fahimci halin da take ciki hakan ze zama kamar tayi butulci ne da irin kokarin da take mata

Ahaka bacci mai nauyi ya dauketa

Ba ita ta falka ba seda akafara kiran sallahr asr da ciwon kai tafalka saboda kukan da tayi lallabawa tayi tayi sallah ,tukuna tafito don dora girki ,a kitchen ta samu aunty marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace "aunty shine baki tashe ne ba ,murmushi kawai tayi mata " to kawo nakarasa aikin ,se a lokacin aunty tayi magana "aa Meerah nasan kingaji kitafi ki huta kawai " aa haba aunty dan Allah kema ya kamata kihuta hakan tafada tana amsar jajjagen da takeyi dole ta sakar mata ,tana tausayin rayuwar Ameerah gata yarinya mai gata da natsuwa amma saboda rashin adalci da son zuciya irin na wasu yana Neman sauyata ya Allah ka kawo d'oki a ratuwar Ameerah

"Amen taji muryar Ameerah ta amsa ashe a fili tayi addu'ar ba'a zuciya ba ,murmushi sukayi dukansu Ameerah tace " Aunty kinason Ameerah fiye da tunani nikaina a duk lokacin da na tuna dangina nakan samu kaina cikin zubar hawaye naji na tsane duniya baki daya sedai da na tuna Inada ke se naji damuwata ta gushe ya Allah yakara zaman lafiya a tsakaninki da yaya yakawo zuri'ah tagari yabani ikon kyauta ta miki nagode sosai aunty tafada kwallar da ta cika idonta yana subowa ,lakace mata hanci aunty tayi tace "to Mr tears nasan yanzu zaki fara zubar hawayen ai kedai bansan tsakanin ki da kuka ba babu damar ayi maganar arxiki dake sekinyiwa mutane kuka ,maza ki share hawayen indai baso kike aunty tayi fada da MABARACIYAR kanwata ba ,dariya sukayi dukansu





Follo me on wattapad@damselfeedo


#Real@Bazamfaria💙

MABARACIYAWhere stories live. Discover now