THE INCIDENT

36 5 2
                                    

Bismillmillahir rahmanir rahim
     Fitowarta kenan daga dan madaidaicin gidansu misalin karfe 6:30 na safe , sauri take dan taga tasamu abun hawa kada ta makara yayinda tayi zurfi a cikin tunaninta

      Batare da tayi aune ba taji an watsa mata abu kamar ruwa a jikinta, dagowan dazata yi  ne tayi arba da wata mota data faka a gabanta ahankali yake sauke glass yayinda ita kuma bata da burin daya wuce taga mamallakin wannan motar daya mata wannan aika aikan and still have the guts to park in front of her....

      Fitowa yayi daga motar yana binta da kallon kyama da tsana , tsaki tayi tace ko ba'a fada ba nasan ba tarbiyya bace ta ishe ka dan babu.... tasssss taji saukan mari batare da ta shirya ba cikin zafin nama cike da daukar fansa itama ta dauke shi da mari , cike da mamaki yake kallonta , yayinda ya fada duniyar tunani danfa ya girgiza da lamarin.... nuna shi tayi da yatsa cikin fushi tace "and mind u fortunes favours the bold, dan haka ka kula nangaba" Afusace ta juya tabar wajen batare da ta jira mai zaice ba...  juyawa yayi yana kallonta har ta bacema ganishi sannan yaja kafafuwansa da ahalin yanzu suka mishi nauyi izuwa "mercedes maybach execelero " dinshi yabar wajen a 360

      Shigarta ajin islamiyar tasu ne gaba daya ido yadawo kanta, batare da ta kulasu ba tayi sallama ta shige sumsum ta zauna .  Basu suka tashi ba sai kusan karfe 5:30 kamar yadda suka saba, tafiya suke ita da wata dattijuwa wanda a kalla bazata wuce shekaru 39 zuwa 40 ba amma a zahiri inka ganta sai kace tafi hakan ma bakomai yajawo hakan ba sai wahala dakuma kangin da suke ciki . Tafiyarsu suke cike da nishadi da matar da kallo daya zaka musu kagane mahaifiyarta ce "nikam boddi ya akayi kikayi latti yau bayan saida na tasheki kafun nafita "
"Eh umma wllh bacci nasake komawa ne shiyasa" Ma'u kenan ya'a daya tilo a wajen malam Nurah wanda yake haifaffen dan garin kaduna ne karkashi karamar hukumar Birnin Gwari, ainihinsu fulani ne na usuli daga mahaifiyarsa har mahaifinshi, sana'ar kayan gwari yake(kamar su citta, kanamfari, masoro, borkono da dai sauransu) kasuwanci ya kawoshi cikin garin kaduna shida matarsa dan lokacin ma tana amarya.... alhamdullillhi dai allah yasa masa hannu kasuwancinsa ta bunkasa wanda duk abunda da ake cikin nan Allah bai basu haihuwa da wuri ba , tun suna sa rai harsuka cire saidaifa godiyar ta daya bata samu matsala da dangin mijinta ba dangane da rashi haihuwa , saida suka kwashi shekaru biyar kafin suka samu cikin yarsu ta fari murna wajen malam Nura kam ba'acewa komi haka ma danginsa ahaka aka sukayita rainon cikin har yakai watar haihuwa kuma cikin ikon allah ta haihu batare da wata matsala ba ......

              Ranar suna yarinya taci sunan kakar ta ta fannin uba wato Asma'u, anci ansha taro ya watse lafiya kowa sai yabawa yake da kyan yarinyar dan bazama kace sune iyayenta ba duk da dai suma ba baya ba wajen kyau, yayinda kowa ke kiranta da ma'u mahaifiyarta na kiranta da Boddi( kyakkyawa da yaren fullanci) sabida sunan surkuwartace kuma itace mafi soyuwa a ranta. Duk da cewa malam Nura bawai yayi karatun boko bane amma yana da buri yayan shi su yi , haihuwa kuma tun daga kan Ma'u ya tsaya cak , wanda tun suna sa ran samu har suka fidda rai suka rungume kaddara

        Ahaka dai ma'u ta girma har tashiga makarantar primary kuma alhamdullillhi tana da kokari sannan tana fahimta , yayinda da kuma malam Nura da matarsa suka zage damtse wajen tarbiyantar da yarsu mafi soyuwa a ransu.... bayan wasu yan shekaru ne nahango wata yar budurwa da bazata wuce shakaru 17 a duniya ba , farace kyakkyawa siririyace amma ba irin busassun nan ba kallo daya zaka mata ka fahimci cewa itadin ma'abociyar  nitsuwace  dan komi nata cikin sanyi take yinshi kamar wacce kwai ya fashe wa a ciki saidaifa akwaita da tsiwa dan duk wanda y shiga gonarta baya fita ta dadi ma'u ku keji (maganin maza ko matan ma baki barsu ba .... wannan shine kirarinta), tana da dan dogon fuska mai dauke da madaidaitan idanuwa da dan siririn hancinta hade da labbanta wanda sukafi komai daukar hankali a fuskarta....
     
        Tsaye take a filin makarantar sanye da matric gown(graduation gown)dan daga gani zaka gane makarantar ta gomnati ce , biki ake na speech an prize giving day kamar yadda take akowace karshe shakara.... koba ba'a fada ba kasan sune set din da zasu fita ma'ana dai yan ss3 kenan.... biki yayi biki kowa na murna amma babu wanda yakai malam Nura murna dan gani yake daga yanzu zai fara cika burukansa na ganin yar tasa tayi zurfi a karatu amma kash.... kana naka Allah na nashi ranar da daddare suna waje bayan yadawo daga masallaci ne yasamu duk suna filin gidan kamar yadda aka saba, anan ne yake kara taya yartasa murna da gama mataki na farko a karatunta , anan ne take baje masa dukkan kyaututtuka data samu... hakan kuma yamasa dadi, doguwar nasiha yamata wanda yasa duk gabobin jikinta suka mutu daga ita har Umman nata harda hawayensu dan dakaji nasihar zaka fahimci kamar wassiyyace a dunkule saidai abunda yasa basu damu ba shine sun saba jin irin wannan daga bakinshi kawaidai nayaudin ne yayi tsauri dayawa

          Allah mai yadda yaso,  kullu nafsin zaa ikatul maut.... a daren ranar Allah yayiwa malam Nura rasuwa , wanda ba iyasu akayi wa rasuwar hatta mutanen unguwa mutuwar ta shigesu musamman in suka tuna cewa ko a jiya ma tare yayi sallar isha'i dashi a massallaci, a haka dai suka dinga karban gaisu ,abun  burgewar dai shine  tun rasuwarsa bakajin komi sai kyawawan halinsa da ake ta fada.... wannan kenan
        Ahakadai kwanaki suka juye izuwa wattanni , watanni suka juye izuwa shekaru , wanda shekarunsu biyu kenan batare da malam Nura ba. Duk da cewa rayuwa tayi musu tsanani amma ahaka suke jurewa yau dadi gobe akasin hakan, takama yau weekend ne kuma al adar suce zuwa tahfiz daga karfe 7:00 zuwa 5:30 to amma kasancewar gidansu da dan tazara da makarantar yasa suke fita 6:30 su isa 7:00 ...  bayan shigarsu gida ne ta wuce daki tayi shirin wanka bayan ta fito ne ta fada kan dan katifar ta dayaji shimfidi dan ma'u dai ba baya  ba wajen tsafta , bacci takeso tayi amma takasa sai dai tunanin mr. Arrogant(sunan data sawa wannan mara tarbiyyar 😄 😄) take yi , itadai bawai har yanzu tanajin haushi bane saboda ita macece da bata da riqo ko kadan dan tun barinta wajen tamanta da zancen shi ma.. kawai dariya ma ya bata , ace daga ganin mutum kai kayi masa laifi amma harda hadawa da mari? Lallai ma wannan baisan waye ma'u ba.... ahaka dai bacci yayi awon gaba da ita

       Shikuma mr. Arrogant yana komawa gida yafada toilet yayi wanka dan hatta kayan daya saka ma kyankyaminsu yake wanka kuwa ba a magana dan fa ya dirje jikinsa yadda ya kamata 😃 shi adolefa najasa ta shafeshi... huci kawai yake kawai baikara shiga shock ba saida yatuna wai harda marinshi tayi " u bitch, who the hell do u think u are , I'll make sure ur life turns to a living hell... " ahaka dai yafito ya tsaya a gaban mirrow yanata mita, oh my Allah he is damn cute, I can't even start describing how devishly handsome he looked.  He has that signature smirk and also a cute boyish look, he is dark in complexion tall slim and ....Gosh... words can't just explain. all I could say was mashaallah ( tsarki ya tabbata ga wanda y halicci wannan kyakkyawar halittar... lolz)

        Shafe shafe da goge goge ya tsaya har na tsawon 30mnts kai ka rantse macece a gaban maudlin ba na miji ba . Usman Abubakar Duwan kenan, da nafarko kuma na miji tilo a wajen Alhaji Abubakar , Alhaji Abubkar dan asalin jihar katsina ne a cikin unguwar Masanawa dake jihar, sudai bazakace ga dalilin arzikinsu ba dan su za aiyacewa gada sukayi tun iyaye da kakanni kuma haryanzu babu dan familyn DUWAN da zakace talakane koda ace jika ne, awata tafiya da Alh. Abubakar yayine zuwa maiduguri yahadu da hajiya Nafisa wanda take shuwa Arab.... kamardai yadda kuka sani shuwa basa auren talaka wannan ne dalilin dayasa bai sha wahala ba wajen yan uwanta game da maganar aure(bawaifa son kudi bane suke dashi , a a... kawai dai custom dinsu ne ahaka) daga nan ne aka wuce da amarya Nafisa izuwa gidan mijinta dake  unguwar malali dake jihar kaduna... Allah ya azurtasu da yaya biyu , Usman da kanwarsa Ushnah , gata dai babu wanda basu ganiba kyawawa ne na bugawa ajarida .... zama daya zakayi a cikinsu kagane cewa Usman dai is the apple of their eyes , baka hada sonda suke mishi da na ushnah musamman ma a wajen mahaifiyarsa  hakanne yasa tun yana 15yrs aka turashi kasar Germany dan yanada burin zama likitan zuciya wato cardiothoracic surgeon , bayan ya kammalane mahaifinshi ya fahimci cewa tarbiyyar dansa daya tilo na neman rugujewa hakan yasa yana kammalawa ya hadasa aure da yar babban amininsa , cikinsu ma'auratan babu wanda ya taba ganin dan uwansa amma a hakan sukayi biyayya ga iyayensu , itadai matar tasa ta kasan ce babar bariyace (wato kauri by tribe) shidai ganin farko daya mata yaji ta kwanta masa a rai dan shi ma'abocin kamshi ne , da tsafta , dan kwalisa ne  itama kuma haka...wanda a halin yanzu ko wata daya mai kyau ba ayiba da dawowarsa daga Germany 🇩🇪 dan ko hausarma yanaji ne amma baya iya mayar wa dan ko dayake school ma mahaifiyarsa ba ta mishi turanci saidai tace suyi hausa in bahaka ba a fasa wayar amma kuma shida dad dinshi German suke yi jefi jefi suke turanci....

Kadan daga cikin tarihin Dr. UADUWAN kenan

Bayan yagama ne ya game jikinsa da da turaruka daban daban kamarsu shumukh, chanel grand extract, DKNY golden delicious, herms 24, caron poivre,  aduniya inba wannan turarukan ba to bazai shafa waninsu ba sabida tsadarsu da kuma kamshin su dan fa gogan naku is a perfume freak.....  kwanciya yayi daganan bacci barawo ya sace shi, bashi ya farka ba sai misalin karfe 1:30 na rana shima kuma sallah ce ta tada shi, wanka yasake yi ya dauro alwala ya wuce masallaci...misalin karfe 2:00 yashigo gidan yana kwalla ma masoyiyarsa kira  "Badawiyyah tah" yafi sau uku amma shiru kake ji babu amsa ko ba'afada ba yasan bata gidane saboda .....

     This is just the beginning,  wait for it... I know u'll find it super duper interesting readers

Huh! Whats up guys , hope u like it...
Pls ☑ ote, follow and comment

Eid mubarak to y'all

UADWANWhere stories live. Discover now