Deep Breath

4 1 0
                                    


Bismillahir rahmanir rahim

        Shigowar raihana gidan kenan da sassarfa kamar wacce aka koro ko sallama babu wacce kana gani kasan da magana muhimmi a bakinta

   "a'ah subahanallahi, raihana lafiya kuwa" faadin umma dake zaune a verandah'n kofar dakin ta tana taje wa ma'u gashin ta datamance rabon data taba shi ma, saidai kawai ta wanke inya bushe a sake kulleshi dan har tsoron taba kan take tsabar cika da kuma tsayin da yake dashi

"yi hakuri umma... Wallahi yanzu ake sanar dani cewa an sake sunayen daliban da sukayi dacen samun gurbin karatu a KASU shine nakeso muyi sauri muje mu duba a cafe " tafada tana dan haki a lokaci daya kuma sai murmusawa take tayi kamar wacce take da tabbacin sun samu ne ma

" ai ho... Wannan da kwana ki kukace kunyi a kamputa yake ne ko menene? "

" eh fa umma shine" ta tarin numfashinta

"to ba sakamakon ya fito ba har kikace boddi na ta samu dari biyu da nawa ma? "

" yauwa umma ai shine, munci jarabawar ai amma bamu samu gurbin karatun ba sai yanzu nasamu labarin an saki sunan daliban da suka samu damar shiga jami'ar " tafada tana ta hararar ma'u kan ta tashi su shiryaa suje

" oh toh.. Allah yasa mu dace, yasa muji alkhairi... Mamana tashi mana kishirya kuje kinga ba a bori da sanyin jiki" dukkansu suka amsa da ameen kafin ma'u ta shige daki danta shirya din kamar yanda umma ta bukata. Batafi 5mnt ba ta fito shirye cikin atamfarta riga da skirt kalar blue da touches din ja hannunta riqe da hijabinta dayasha guga blue colour tana faman saka wa

"toh umma saimun dawo.. " fadar ma'u   dake kokarin fita daga gidan

" tsaya mana mamana haka ake tafiya ne baku karbi kudin abun ba... Nawa ne ake duba wa? "  umma tafada tana mikewa daga zaunen da take

" a'a umma ki bari kawai ai bawani kudi bane bazai wuce dari biyu bafa, zan biya mana"  cewar raihana dake tsye bakin kofa

"toh a dawo lafiya, ku kula da hanya banda rawar kai mamana " ummaa ta fada tana dariya itama dan tasan yadda tsawon shekarunnan ma'u bata cire rai a karatun nan na zamaani ba duk da cewa tasan me biya matan baya doron kasa

" Asma'u Nuraddeen... " taji ma'aikacin cafen ya fada yana tayata murna  dan tasamu admission ta fannin MASS COMMUNICATION Murna a wajensu ba'a maganna daga ita har Raihana sun samu admission din saidai ba course daya bane kamar yadda auka tsammata, amma duk da hakan sun taya juna murna sosai

             A haka suka juyo zuwa gida suna ta murna su kadai kamar wayanda akayiwa albishir da gidan aljanna, ahaka suka rabu da raihana daidai kofar gidan su ma'un a cewarta zataje itama ta sanar da gida tukunna amma zata shigo mata anjima

   "salamu alaikum Ummaaaaaaa.. Umma!! Umma!!!" ma'u keta kwalawa mahaifiyarta kira wanda ko ba a fada ba abun da tazo da shi na alkhairi ne kuma tattare da farinciki

"Na'am... Ni ameena yannan bazata taba girmaba" umma data fito daga bayi hannunta dauke da buta take  fada

"Umma albishirinki... " tafada tana karasowa wajen umman nata

" Goro fari sol boddi am"

"Umma nasamu gurbi karatu a KASU... Da yaar jarida kike magana fa yanzu" tafada yayinda da take riqe da hannun umma cike da zolaya

"Alhamdulillahi mamana... Allah yasanya alkhairi" 

Yinin ranar ma'u tayishi ne cike da walwala kamar wacce aka ce an yafewa zunubanta, ita kadai ta zauna murmushi kawai takeyi kamar ba ma'un da kuka sani ba... Misalin karfe biyar da rabi kuwa saiga Raihana itama tazo aka hadau sai hira ake game da sabuwar rayuwar da za a shige

UADWANWhere stories live. Discover now