UADWAN page 6
Bismillahir rahmanir rahim
Sai bayan ta wuce dakinne take ta mamakin kanta da har ta tsaya kuka sabida zai kara aure, share hawayen fuskanta tayi sannan tafara maganar zuci " why am i cyring? Dan zai qara aure? So what in ma auren zai kara... to hell with him and whosoever he's gonna get married to" tana gama wannan tunanin ta fada toilet tai wanka sannan ta fito, mai kawai ta shafa sannan bata yi wani make up ba dan kuwa babu komai a fuskanta bayan glosy lips din data shafa saman labbanta da powder sai kwallai data zanawa fararen idanuwan ta sanna ta wuce closet ta shirya cikin wando plazo dark green da top high neck yellow color dukka na kamfanin D&G sannan tasa flat shoes na valentino green in color sai purse data dauka yellow da scarf green... feshe jikinta tayi da turarukan da suka zame mata jiki wanda ko zufa take kamshinshi takeyi
Bakajin karan komai saina takalman kafanta, da haka ta fito rike da car key a hannunta ta wuce parking tent din ta dau motarta ta fice... bata zarce ko ina ba sai wani dan hall da ya amsa sunan sa wanda mu anan kai tsaye zamu iya kiranshi da club ko bar amma ba club bane saidai yanayin tsarinshi ne kamar na club din... gurin na musamman ne kamar yadda suma suke na musan man. Mayan matane da suka amsa sunansu sukacika hall din wanda dukkan su matan wane da wane ne a wajen ko wacce ji take da kanta, kowacce takama take da matsayi kokuma abunda ta mallaka. Sudai ba yan bariki bane, a a wayewace zallah da kuma naira data zauna musu Kida kawai ke tashi a cikin hall din
Tana shiga ido ya dawo kanta dan a gaba daya taron matan dake wajen itace female lead dinsu bawai dan babu wanda sukafita kudi bane ko wani abu, kawai dai tana da wani class, burgewa dakuma shiga rai, uwa uba nasaba kudi da kuma daukan wanka akarshe kuma gata surkuwa a gidan Alh. Abubakar Duwan shahararren dan kasuwan daya amsa sunan shi bama a iya nan gida nigeria ba..... dogon table ne dauke da kujeru wanda akalla zasu kai 30 a wani sashe na cikin hall din wanda a bangon wajen akwai wani banner da ke dauke da rubutu masu manyan raufa ** ** , kujera taja ta zauna batare da tacewa kowa komi ba akaci gaba da taro , sai bayan ta zauna ta nitsu sannan tai gyaran murya ta fara magana kamar wacce ake tilastawa " so sorry for arriving late... something came up and i had to attend to." Daga nan bata sake cewa komi ba har aka gama taron aka fara dan ciye ciye da dan hirarraki kowani clique da topic din dasuke tattaunawa a kai a haka tana zaune ita kadai batare da ta kula kowa ba dan she was moody bata masan me take tunawa ba, ita dai kawai gata nan ne
Ahaka ta mike ta nufi gida a gajiye, kamar yadda ta tsammata babu kowa a palour'n sai kayan wuta dasuke ta aiyukansu, tana shiga daki ta kwanta batare da ta rage kayan jikin ta ba abubuwa da dama ke yawo akanta wanda batasan dalilan su ba... bawai wani sonshi take ba da har dan zai kara aure hankalinta ya tashi, no she's above that level tunda dai aure zai kara kenan ai bata da amfani ne dan dai gashi ya tabbata bazata iya haihuwa ba, saikuma taja tsaki sannan ta cire dankwalin kanta ta cire takalmanta ta gyara kwanciyarta sai bacci, wanda baccin dagani kasan bawai ta shirya mishi bane
Yau kimanin kwanaki uku kenan da maganar da sukayi dashi wanda tun daga wannan ranar bai sake sata a ido ba dukda cewa duk wani movement nata yana sane dasu amma yana mamakin yadda ta cigaba da rayuwarta kamar babu wani abunda ya faru ... kenan ma shike tayata kishi wajen momma ita ko a jikinta rayuwarta take saima abunda ya karu ..... inda kuma a daya bangaren abdool nata jan ra'ayin shi akan ya amince da shawararshi dan itace kadai mafita a gareshi amma sam yaqi fahimtar hakan gashi yau a kalla anci kwanaki hudu kenan acikin lokacin da momma ta dibar mishi
" yanzu su wayan nan ko kazo gidan nasu ma ba saminsu zakayi daga matar har mijin saikace ba gidan ma'urata ba .... amma wallahi yau ko dame suke takama sai na samu abun fada duk boye boyensu kuwa" tunanin da Ushnah take tayi kenan ita kadai bayan tagama parking motarta a tent din gidan yayan nata, da sallama ta shigo kamar ko da yaushe dai palourn na nan empty kamar ma dai babu mutane a gidan duk da cewa yaudin yakama sunday kenan yakamata ace daga matar har mijin suna gida tunda shi mijin bawai aiki ya fara ba matar kuwa yau weekend ce,
YOU ARE READING
UADWAN
FanfictionMeet the arrogant dr. Outhman Abubakar Duwan, A cardiothoracic surgeon, a guy with pride, cruel, vigorous but above all hearty and always there to do the needful fortunately, she came into his life and be the best decision he could...