Bismillahir rahmanir rahim
Fitowarta kenan da kawarta Raihana sai ganin su dr. Sukayi a tsaye da alama ma isowarsu kenan kallon kallo aka tsaya yi tsakanin dr. Da Raihana wanda kowa da abun da yake rayawa a ranshi game da dan uwanshi, saikuma Abdool da Ma'u da suke tayasu suma suna kallon abun mamaki saikace ma sun san juna ne kokuma da akwai wani abu a tsakanin su nan kuwa babu komi dan thats their first meeting, shi ya fara dauke idonshi daga gareta dan shifa kallon ya mishi yawa kuma ya tsani hakan ( niko nace shikuma da wani idon ya san tana kallonshi...)
Gyaran murya Abdul yayi dan karama bata lokaci suke anan din sukuma basuyi abunda ya kawosu ba , "sannuku dai yan mata ..." ma'u ce tai murmushi harta sami daman ansa mai.... sannan tai musu iso cikin dan madaidaicin gidan nasu da yake a gyare tsaf bako alaman datti, tsaki dr. Yayi ciki ciki yana rayawa a ranshi cewa ba laifi ba kazamai bane he love that.....
Shidai Abdool abun nema ya samu , sai zuba yake shida su Raihana, dr. Kam an barshi da mamaki wato she wannan yarinyar tana surutu haka , he hates that ai babu class a ciki kuma ma wai da na miji sai abun ya kara bashi haushi ( niko nace me nashi a ciki tunda ba da shi ake ba,) saikuma ya mike. Abdool ne ya dago ya kalleshi yagane meyake nufi amma sai yayi burus dashi dan shima wannan miskilancin ya isheshi , csn kuma sai yai murmushi " to yanzu anan wacece patient din namu .... muna dan sauri ne" ma'u ne tafara dariya harda rufe baki , "wai patient, toh dukkan mu ba mara lafiya " Raihana ce ta nuna ma' u cikin neman tsokana " gata nan kaganata... allurance bata so" mikewa ma'u tayi badan taso ba suka dan matsa gefe ..... sa hannu yayi ya daga rigan atamafar da take jikinta, itadai idonta a kulle yake wanda shikuma baimasan tanayi ba hannun shi ya daura zai saukar da skirt din kasa in order to get access to her butts, wani shock din da dukkansu suka ji ne ya sa shi tsayawa da abun da yayi niyyan yi for some seconds sannan kuma sai ya basar abunku da miskili gaba daya ba a taba gane inda ya dosa, lallaba wa yayi ya gama mata sannan suka juyo ita tana kallon bayanshi shikuma yana kallon inda suka bar su Abdool yana mamakin inda suka tafi yanzu yanzu bayan yasan ba zama yazoyi ba
Hanyar fita yayi ita kuma haushinshi takeji tunda yasa taji shoxk dazu kuma ai da gangan yayi gashi yana ta kalle mata jiki, aide daga gobe shike nan ita ma zata huta da wannan jara babben alluran.... yana fita kuwa yaga Abdool da Raihana a tsaye a jikin mota suna ta kyalkyale dariya, haushi yakuma kama shi , wato shi maitan nashi ma bai tsaya a iya manyan mata ba harda wayannan yan tatsitsan yaran da banda raini babu wani abu da zai shiga tsaninsu , to wai mema zaiji a jikin wannan kwailan hmmmmmm shi dole ma yaja mishi layi inzai yi neme nemen matanshi yabari sai yazo shi kadai amma ba dashi ba dan bazai jawo mishi rainiba wllh , duk wannan maganganun da yake yi ya yishine cikin yan mintunan da basu wuce biyu ba , karasawa yayi inda suke ya buda mota ya shiga , Abdul na ganin haka yai saurin sallamar Raihana da cewa sai sun zo gobe tace toh , danshi yasan halin kayanshi. Yanzu sai ya tafi ya barshi ba damuwarshi bane
A maimakon su wuce gida kawai kuma sai yaga sun canza hanya wanda bana gida ba shidai bai tambaya ba dan koya tambaya ma ba fadamai zaiyi ba , a gaban wani shopping mall yaga sun paka ... fitowa sukayi su biyu suka shiga ciki kowa sai gaishesu yakeyi sabida sunsan dr. Baya bane wajen alkhairi dan dai in yazo ma'aikatan wajen suma ranar aljihun su zaiyi nauyi, aikuwa suna suka nemi wani isolated wajen da babu kowa da fancy tables and chairs wajen yasha flower , wani ma'aikacine da yaga shigowansu yayi ciki da sauri can sai gashi kowa na cikin mall din yana fitowa da wayanda suka gama siyayya da wayanda ma basu gamaba, agogon dake daure a hanushi ne ya daga ya duba yaga kusan 5mnts kenan da zuwansu wajen, ya mike kenan zai juya saiga wannan ma'aikacin na dazu ya shigo da surinshi... "sorry sir... all done" ko kallon inda yake baiyi ba ya wuce ya shiga cikin mall din , direct wajen turaruka ya wuce ... turare ya jida kusan guda 12 tun daga kan clive Christian 1872, Eau D'harden annik goutal, caron's poivre, clive Christian's imperial majesty, caron poirre, herms 24, channel grand extrait, shumukh, DKNY golden delicious..... haka dai yaita jidan su yana sawa a basket har zai juya kuma kome ya tuna sai ya nufi wajen kayan mata idonshi ne ya fara sauka akan wani zobe dake cikin box an ajiye shi cikin glass kawai sai yaji ya burgeshi zuwa yayi ya dauka yaga price dinshi 2.5m akayi tagging a jikin glass din shidai bai ma ga tsadarshi ba dan zoben is worth it...
YOU ARE READING
UADWAN
Fiksi PenggemarMeet the arrogant dr. Outhman Abubakar Duwan, A cardiothoracic surgeon, a guy with pride, cruel, vigorous but above all hearty and always there to do the needful fortunately, she came into his life and be the best decision he could...