1&2

562 30 5
                                    

*KI YADDA DANI.*
_Kishiya Ko Baiwa_
     _Return_

_Na Marubuciya_
*REAL ESHAA*

_WATTPAD_
*Realeshaa*

_Like my page on Facebook_👇🏻

https://www.facebook.com/REAL-ESHAA-FANS-114689303720405/

*_Ya Allah Ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kajikan duk kan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da imani._*

_Wannan littafin na kudine akan farashi mai sauki Naira Dari biyu se ki turo katin MTN ta wannan number 👉🏼09066936967 tare da turomin da shedar biya ta Wannan number 09068403802.ko kuma ta account dina Abdullahi Aishatu keystone bank 6030406548._

*FREE Page 1&2🖊️*

______________________📖Tamkar saukan aradu aka haka kalaman sa, ya daki zuciya yo yin mu,Musamman ma ni wani irin tsuma jikina keyi tamkar mazari yayin da idanuna suka kada sukayi jawur dasu tamkar garwashi babu abinda yake yawo a kwakwalwar kaina face muryar sa dake furta kalman saki agareni Innalillahi wa'inna ilahi raji'un.shine kalmar danake furta wa acikin raina ko zanji saukin abinda ke yawo acikin zuciya ta Wanda ke barazanan tarwatsamin lissafi.Nakasa ko da dago kaina ne,addu'a kawai nake Allah yasa mafarki nakeyi ba gaskiya ba domin zuciya ta yakasa gaskata min abinda kunnuwa sukaji...
Cikin kunan zuciya dawani irin nadamar kasancewar Ahmad jininsa,Alh Ali yamike tare da kaiwa Ahmad din wani wawan mari,anma ga mamakin sa seyaji anrike hannunsa ta mau tamkar za aballa.Shiru dakin yayi tamkar babu mahalukin dake numfashi aciki. Sakamakon muryan Ahmad daya karade ciki dakin,Cikin hargagi da rashin kunya yace"Wallahi Baffa karkayi Wannan gangancin acikin rayuwar ka,nacewa zaka sanya hannunka ajikina dasunan duka!,nawuce Wannan matsayin azanyu ko wancan ranan daka marini na 'kyaleka ne kawai domin ina ganin mutunci ka,amatsayin ka na wan mahaifina anma badan Wannan ba babu dalilin daze sanya in daga maka kafa.Ayanzu muddin kace zaka sake Wannan gangancin zan baka mamaki fiye da yanda baka zato,yafadi haka asanda yake wurgi da hannun Alh Ali tamkar ze karya.Kallon kaskanci ya watsa musu daya bayan daya kafin yaci gaba dacewa.Wannan rainin wayon naku ya isheni haka kunce nasaki yarinya tunda bazan iya riketa ba,nasaketa anma hakan be ishe Ku ba,ko kuna tunanin dama bazan Iya sakin tabane shiyasa kuka dameni dacewa na saketa to ko 'yar gwal ce 'yar taku Wallahi narabu da ita.!??Hhhh yakece da dariyar renin hankali kafin yadaure fuska yace"me zanyi da Wannan yar taku  irin jaraba,da rashin tarbiya,tunda na aureta nafara tsiyacewa,ashe jangwam na kwasowa kaina bansani ba,saboda bakin mugunta da zalunci kunsan 'yarku gayyar tsiyace anma kuka lika min ita,saboda kunaso in talauce mudawo Dede daku ko!!?Wallahi nayi danasanin hada iri daku.Ni ayanzu ban 'ki Wannan kaddarerren cikin yazube ba kowa yahuta,sannan magana na karshe dazanyi daku shine daga yau,babu ni babu Ku maganan ciki kuma kar wanda yace"ze tun kareni akai domin ba zanyi asaran kudina akan shiba,sannan ko yau ta haihu Ku kawo min abinda tahaifa nizan bashi tarbiyan daya ce, dan banga alamar zesamu wata cikakkiyar tarbiya agidan nan ba....Amatukar fusace Alh Ali yadago kai yace"Ahmad shin kana da hankali kuwa?kasan mekake...Cikin sauri Ahmad yadaura ya tsansa akan bakinsa, tare dacewa shitttt...Bana son jin komai daga bakin ka Baffa idan har Santa kakeyi kabari idan tahaihu takawo min 'Dana ko 'yata seka aureta ina ganin hakan zefi se in tabbatar dacewa kadamu da ita anma base ka tsaya yimin holo ba...Yana gama fadin haka yajuya yafice daga dakin batare daya sake furta komai ba....

kasa dago kai Alh Ali yayi,daga matsananciyar kunyar da Ahmad yasanya shi tun lokacin dayace ya Auri Sukainat yaji tamkar anzare masa laka ajikinsa jiyake inama 'kasa yatsage yashiga da Wannan kunyar daya shiga kamar shi Ahmad ze kalli tsaban idanunsa yace"ya auri matarsa.Hakika Ahmad yabasa mamaki, anya yana cikin hayyacinsa kuwa yatambayi kansa,?wata zuciyar ce tace"yana ciki mana kawai de yadena ganin kimarka ne shiyasa yafada maka abinda ransa keso yakuma tozar taka yatafi.Ahankali yadago jajayen idanunsa dasuka rine da matsanancin bacin rai da kunya dakuma nadamar zuwan da yayi hakika dayasan irin cin mutunci da Ahmad ze masa kenan babu shakka ba abinda ze kawo sa.Cikin raunin murya yace"Dan girman Allah Malam Ahmadu kuyafe min, Wallahi bantaba zaton irin Wannan wulakancin daga wajen Ahmad ba,anma Ahmad ya tozartani acikin mutane,yafada asanda yake hade hannayensa guda biyu waje daya alamar roko tare dayin kasa da kansa...

Ki Yadda Dani Kishiya ko Baiwa returnWhere stories live. Discover now