💕💕RUSHDAH 💕💕
Page 5
©️ oum zahrah....💞
Kawata kwana biyu shiru ba amo ba labari?
Kedai bari abubuwan ne sai a hankali kinsan zaman abuja babu takamaimain aiki sai a hankali .
A
Haka ne kam , gidan Alhaji ali naje na biyo ta nan mu gaisa.
Kin kyauta gaskiya daman neman abokin shawara nake kan lamarin Azeez,Footsteps ta sukaji shiyasa suka dakata da maganar da suke,
Gaidasu yayi suka amsa ya bude kofar parlorn ya fita .Kawata yaushe danku ya dawo?
Uhmm last week ya dawo kinsan ya kammala karatu , uban sai rawar kafa yake danshi ya xama doctor,
Sama masa aiki yayi nan Nation hospital.
Hmmm Lallai kam keko kina xaune har abin ya kai ga haka ?
Yaxanyi kawata ?Kinsan fah yanda Azeez yake gwara kin tashi tun wuri kin kwatar masa hakkinsa idan ba haka ba yaran matannan duk xasu mamaye komai keda danki ku tashi a tutar babu.
Gabadaya lamarin yaronnan na damuna musamman lamarin shaye shayen nan da biye biyen enmata na yi magana har na gaji ni tsoro na ma kar Mahaifinsa ya gane duk da ba xama yake ba amma wannan dan sa ido ya dawo yanxu.
Sakkowa tayi ta gaida su ,
Amsawa kawar mumy tayi ita ko ko kallo bata ishe ta ba ,
Wucewa tayi xuwa kitchen.
Kawata ina kuka samo wannan bafulatanar?
Uhmm nima tare na ganta da su , daga dai ribado suka dawo tare ina jin yar uwar matar nan ne kinsan ba shiga lamarin ta nake ba .
Gata kekyawa wlhy .
Ina kyau anan abu kamar a hureta ta fadi?
Da alama idan ta samu hutu xata ciko sosai gaskiya da ina da daa namiji da xan naima masa aurenta .
Allah ya sauwake , yaronnan tunda taxo na lura fita hayyacinsa yake idan ya ganta , tsoro na daya kar abinda ya faru da dije ya maimaita kansa ,Ya kuka kare da su iyayenta sun karbi tayinki ne ko basu karba ba? Kema kinsan son kudin mahaifiyarta yayi yawa , karba tayi har da godiya haka maganan ya mutu.
Fitowa tayi dauke ta cooler akan tray ta haye sama xuwa dakin su ,
Bude kofar tayi ta shiga .
Kayane kota ina da alama parking hanan keyi tana sakawa a box dinta ,
Rushdah sannu da kokari kin bi kin xamar da ni laxy komai kawo min kike idan na koma school xan ji jiki.
Murmushi tayi bata ce komai ba taxauna .
Ina black viel dina yake kin gani?
A yana cikin wordrob dinki ta kasa.
Ajiye kayan tayi ta xauna suka fara cin abinci, wayarta ce tayi ringing ,"My cream"
Smiling tayi ta yi picking
Sweetheart
Naam ya kake?
Fyn ya shirin komawa school?
Gashinan muna kai ,
Sai na xo picking dinki up around 5pm ok.
Ok sai ka xo thanks luv u.
Luv u too bye.Kallonta rushdah take cike da shaawa komai hanan tayi burgeta take .
Uhmmm love birds da alama wanan ya saye xuciyar mu ko?
Uhuuu sosai ma , kar ki damu anjima idan ya xo zaku gaisa .Hanan dan Allah aran wayanki xan kira addaji mu gaisa ,
Tunda na xo bamuyi wayaba ,
Mika mata wayar tayi kirar 11 pro karba tayi ta saka wasu numbers .
Ringing yayi bai dade ba aka daga .
Hello addaji 'rushdah ce.
Kishiyata ta kaina yakike ya mamin taki ?Lafyansu lau suna gaisheki.
Hawaye ne ya cika mata ido tuno da muryar umma saboda sak muryarsu daya da addajin.Rushdah yakikayi shiru?
Ina fatan kin kwantar da hankalinki kuma xaki karbi kaddara aduk yanda taxo miki, fatima aduaanki take bukata haka muma lokaci muke jira dan Allah ki sassauta wa kanki ki daina kokekokennan haka.
Kinji ko ?
A naji nagode ki gaida su ameera , xasuji sai anjima Allah ya miki Albarka ya jikan iyayenki.
Ameen nagode sai anjima kashe wayan tayi ta mika wa hanan .
Toh zaki fara sanaa ko ?
Gaskiya xan gayawa mami ta saka ido sosai akan wanan hubby dinki na kukannan.
Share hawayenta tayi ta tattara kwanukan ta fito da rufe kofar.
A corridor ta ganshi tsaya da wani alama fitowa sukayi daga daki ,
Ina wuni ?
Kallonta suke suna kare mata kallo ,
Wucesu tayi saboda batason abinda xai hadata ta shi da alama mayen mata ne.Kai kai kai ! Ita ce wannan?
Yes itace wlhy kwanannan da ita nake mafarki na rasa gane sukunina .
Gaskiya ban sammani takai har haka ba .
Gaskiya ina goyon bayanka ka gwada saanka idan ka samu dama nima kar ka manta da ni , harara Azeez ya ma abokin nasa i cant share her with any one gaskiya gwara ka cire idonka a kanta tun wuri, abin kuma har ya kai mu ga rowa ne?
Na dai gayamaka back off!
Fita sukayi daga gidan .Knocking tayi a dakin mami izini tayimata ta shiga da sallama ta xauna a kasan rog,
Xo nan kusadani ni ki xauna mana .
Tasowa tayi ta xauna kusa da ita ,
Mami akwai aikin da xan miki ne ?
Eh too nan kam babu amma ki taimaka ki share dakin yayan naku .
Toh mami bari in je .
Tashi tayi ta na fatan Allah yasa baya nan don kwanabiyu basu hadu ba,
Tsintsiya da parker sai mopper ta dauko tanufi dakin da take kyautata xato nasa ne,
Turo kofar tayi ta shiga dakin kamshi dakin yake ya tsaru sosai, komai matured babu wani tarkace ko ina neat alama maabocin tsabta ne, a bedside drawer ta ga wani karamin frame mai kyau ,
Hotonsa ne sai mami da hanan sunyi kyau sosai.Gaskiya yaran mami suna da kyau musamman ya ayaan yana burgeta amma matsalarta da shi bai sonta ta rasa gane mey ta masa da ya tsaneta har haka.
Ajiye hoton tayi ta gyara dakin tsab ta yi mopping,
Shiga bayin tayi ta wanke duk da ba wani datti yayi ba , kayan da ta gani a loundry basket ta fitar ,
Jeans ne kala biyu sai top biyu da boxers sai kuma singlet. Tara ruwa tayi ta jika kayan ,
Sai da ta jika kayan ta fara tuhumar abinda tayi shin waya aiketa wanann danyen aikin ?
Idan ya xo yayi fada fa ?
Asanyaye tafara wanke kayan .Horn yayi mai gadi ya bude masa kofa ya shigo .
Parking yayi a lot din gidan ya fito hannunsa dauke da leda mai tambarin H medix ya rufe motar ya nufi cikin gidan a sanyaye , babu kowa a palorn ya haura sama xuwa dakinsa.Bude kofar yayi ya shiga ,
Kallon dakin yayi da alama aikin mami ce wannan .
Ajiye ledar maganin yayi ya ballo daya ya dauko ruwa a karamin firdge dake dakin ya sha maganin , cire shirt din jikinsa yayi ya kwanta a gadon a sanyaye mafita yake nema ma kansa saboda alamu sun nuna maganin ya daina masa amfani kamar da '
gashi yana da ulcer cronic axumi is not an option.
Motsin da ya ji a toilet alamun faduwa abu da karfi shi yasashi tashi ya nufi toilet din .
Bude kofar yayi ,
Yashe take a kansan toilet din xaman yan bori tayi ga kaya a xube da alama tsantsi ne ya debeta ta fadi.
Kuka take saboda ta bugu sosai kugunta ji take kamar ya balle.
