*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*
*🧕ƳAR HIZBA🧕*
(PAID BOOK)
NA
*MARYAM MUHAMMAD SANI (MUM AMNASH)*
*WATTPAD@mumamnas2486**MAI BUƘATAR WANNAN LITTAFIN ZAI BIYA KUƊIN KARATU 200normal, 300vip, 400special ta wannan account no. 2083460164 Abubakar Abdullahi Zenith bank sannan a turo shaidar biya ta wannan number 07038826617 ko a turo katin MTN ta wannan number*
12/zulhajj/1442 - 22/7/2021
_NI MARYAM MUHAMMAD SANI(MUM AMNASH) INA TAYA ƊAUKACIN MUSULMIN DUNIYA MURNAR BABBAR SALLAH, ALLAH YA KARƁI IBADUNMU, ALLAH YA MAIMAITA MANA, ALLAH YAYI MANA GAFARA DA WAƊANDA SUKA RIGAYEMU BARKA DA SALLAH GA KOWA DA KOWA.
FREE PAGE 3️⃣
"Malam ta yaya zan zama Kwamandan ƙaramar hukumar Tsokumbo?" Murmushi Kwamanda Haruna Bala yayi yace "Laminu ƙwarai haka na ke nufi, bari na yi maka gwari-gwari zan bar wannan ofishin zan koma hedkwata ta Jahar Kadabo."
"Amma Malam..." Katseshi Kwamanda ya yi, ya ɗaga masa hannu yace "Laminu nasan bai wuce kace, zan yi biyu babu ba ko? Kar ka damu, sam a yanzu banida burin zama a wata kujera face burin kare martaba da ƙimar wannan Hukumar, Allah ya datar damu baki ɗaya." A hankali Laminu ya amsa yace "Ameen Malam" Kusan a lokaci guda suka fita daga motar suka shiga ofishinsu, suka cigaba da ayyukansu na yau da kullum.Tun da aka kammala taron suka koma ofishinsu ta zauna girim ba abokin hira, cike take da mamakin irin kallon da wasu daga cikin abokan aikinta suke yi mata, hakan yasa ta miƙe ta nufi harabar Hukumar. Ta tsaya kawai tana kallon shige da ficen mutane.
Hango Malama Saudat da tayi ne yasa ta sunkuyar da kanta, sai da ta ɗan rissina sannan tace "Barka da aiki Mama" Ɗan jim Malama Saudat ta yi sannan tace "Barka kadai Ƴata, maza biyo ni ofis ɗina akwai aikin da zan saka ki" "To" ta amsa a taƙaice tabi bayan Malama Saudat.
Kujera Malama Saudat ta nuna mata, cikin sanyin jiki ta zauna tana satar kallon ƙayatuwar ofis ɗin, ba laifi komai tsaf-tsaf sai sanyin AC da ƙamshin turaren ɗaki da ke tashi.
Da murmushi a fuskar Malama Saudat ta miƙawa Baby wani fiyal (file) sannan tace "Malama Baby ya sunanki ne?" Da murmushi a fuskarta tace "Fatima Usman"
"Yauwa yanzu na ji batu, amma dai da alama ke Ƴar Auta ce, idan ba Ƴar Auta ba yaushe za'a dinga kiranki da wani Baby. Yauwa Malama Fatima taso ki dawo nan ki zauna, ɗauko Fayal ɗin da na baki."
Miƙewa tayi a sanyaye ta kai dubanta kan mazaunin da Malama Sauda ta nuna mata, jiki a sanyaye tace "Mama ai nan ya isa" da murmushi a fuskarta tace "Malama Fatima ki zo ki zauna."
Ba musu ta haye lintsimemiyar kujerar Mataimakiyar Kwamanda ta zauna, a zuciyarta wani daɗi na ratsata, tana Addu'ar Allah ya kai damo ga harawa ko bai ci ba yayi birgima a cikinta.Sai da ta sanya tibaran ƙarin gani sannan ta juyo da na'urar da ke girke saman teburin (laptop) tace "Malama Fatima ina son ki duba min rubutun da ke jikin takardar cikin fayal ɗin hannunki da wanda aka shigar a na'urar nan, idan kinga da matsala sai ki yi min magana. Kwana biyu idanuna ne ke ɗan ciwo, bari na nuna miki yanda za ki yi. Baby ta ɗago kai tace "Mama ai na iya, na taɓa yin diploma a wata center, sannan wasu lokutan nakan taya Yayata" da murmushi a fuskar Malama Sauda tace "Yauwa Ƴar albarka, da alamu, zan yiwa Kwamanda magana ya bar mini ke a nan ki dinga taimaka min." Daga nan kowa ya tsuke bakinshi, cikeda ƙwarewa Baby ta cigaba da sarrafa na'urar Laptop ɗin da ke gabanta, cikin lokuta ƙalilan ta kammala, don gyararrakin babu yawa.
Tana kammalawa ta nunawa Malama Saudat gyare-gyaren da tayi, daga nan ta sallameta bayan ta tilasta mata karɓar cakes da Lemo, har ƙasa tayi mata godiya sannan ta koma can ofishinsu.
Ganin har yanzu ba wanda ya kulata yasa ta bibbisu ɗaya bayan ɗaya ta gabatar da kanta, a lokaci guda kuma tana nazartarsu don ta gane halayya da ɗabi'un kowa, kamar yanda ta gane na Kwamandan Tsokumbo, Mutum mai son girma, faɗa da rashin ɗaukar wargi bata san lokacin da wani murmushi ya ƙwace mata ba.
YOU ARE READING
ƳAR HIZBA(PAID BOOK)
General FictionCakwakiyar labari a kan wata matashiya da ta dira a Humar Hizba ta garin KADABO, ta zo da salo iri iri ciki kuwa harda koyar da mata da maza rawa don samarwa da hukumar kuɗin shiga. Bata soyayya, maza tsoronta suke, tana iya komai akan hukumar. Tsor...