*TSANTSAR YAUDARA😭💔*
*'Yar mutan zazzau Naanah M Sha'aban✍🏾*
*Sadaukarwa ga Habibaties💃🏼*
*Ku ta ya 'yar uwarku sharing dan girman Allah🙏🏽*
Shafi na 3
Yau ya kama za'a d'aure auren Abdulrahman da Fad'ima ana ta shirye-shiryen auren ya rage sauran awa d'aya a d'aura auren dan wasu ma har sun fara tafiya masallaci, Abban Abdulrahman ya kira Ummi mahaifiyar Abdulrahman a waya ta matsa nesa da mutane tare da d'aga wayar ba tare da tayi sallama ba ta ce "Alhaji meyafaru kai wai ba za ka dawo a d'aura auren d'anka a gabanka ba, za ka je ka mak'ale a wata k'asar karka manta fa Abdulrahman shine babban d'anka nii ban tab'a".............Cikin yanayin b'acin rai Alhaji Saleh ya dakatar da matarsa Hajiya Saratu da cewa "Kinga ban kiraki dan ki dinga gaya min maganganun banza ba, na kiraki ne dan na fad'a miki cewar an dakatar da d'aura auren Abdulrahman zuwa nan da watanni biyu masu zuwa kuma na fad'awa Kawu Bala ma" Alhaji Saleh yana kaiwa nan a maganarsa ya kashe wayar, Hajiya Saratu kuwa kai ta dafe tare da dura wani irin ashar, nan ta shiga kiran wayar mijin na ta amman a kashe, komawa tayi cikin mutanan tana kuka dan ta san yau Abdulrahman zai iya yin komai idan ya ji an d'aga auren nan, Babbar yayarta ce ta ja ta gefe take tambayarta meyafaru??? Bata b'oye mata komai ba ta fad'a mata abin da Alhaji Saleh ya ce mata, Salati Aunty Hajara ta shiga yi tare da cewa "Meyasa Alhaji zai ce a d'aga d'aurin auren nan??? Duk yadda akayi akwai babban dalilin da yasa ya ce a fasa sai nan da wata biyu" Hajiya Saratu ta kalli Yayarta ta ce "Babu wani dalili wallahi kawai daman baya son farin cikin mu ne, shiyasa ya fara k'irk'iran abubuwa don ya ga an fasa auren nan kuma wallahi bai isa ba sai an d'aura auren nan yau d'in nan babu fashi" Wani irin kallo Aunty Hajara ta watsa mata ta ce "Anya kina da hankali kuwa Saratu?? To idan kin manta yanzu zan tuna miki mijinki ne, kuma yafiki iko a kan Abdulrahman dan haka babu man d'aura auren nan har sai yazo munji dalilinsa da yasa ya ce a d'aga auren kin gane ko?" Aunty Hajara tana kaiwa nan a maganarta ta nufi hanyar da zata sadata da babban falon gidan, ita ma Hajiya Saratu ta bi bayanta jikinta duk a sanyaye zuciyarta kuwa kamar zata fashe saboda bugun da takeyi mata, Aunty Hajara ce ta shiga fad'awa mutanan gidan cewar an d'aga d'aurin auren saboda wani dalili babba, haka kowa ya watse masu gulma nayi masu mamaki nayi aka bar gidan daga Aunty Hajara sai Hajiya Saratu da yaranta su shida, uku mata uku maza Abdulfatah shine d'anta na biyu sai mai binsa Abdul'aziz,Abdullahi,Fanal,Finat sai kuma autarsu Meenal gaba d'ayansu sun yi diploma Abdulfatan,Fanal da kuma Abdullahi sun fara karatunsu na degree a wata babbar makaranta, Meenal,Abdul'aziz da kuma Finat su kuma Alhaji Saleh ya basu babban kamfaninsa mai suna *MAI AMINCI COMPANY* babu abin da ba'a siyarwa a company, Gaba d'ayansu idan ka kalli fuskokinsu za ka ga tsantsar tashin hankali kowannan su da abin da yake sak'awa a ransa game da fasa auren da akayi, Abdulrahman ne ya shigo falon ya sha farar tsadaddiyar shadda da ta sha aiki babbar rigar jikinsa duk ta yamutse, A gaban Hajiya Saratu ya tsaya yana wani irin huci,farar fuskarsa tayi jajawur idanuwansa kuwa kamar an watsa masa barkono, mik'ewa suka yi dukansu suna kallonshi, Hajiya Saratu ta bud'e baki za ta yi magana Abdulrahman ya k'atseta da cewa "Ummi me na yi wa Abba zai yi min haka?? Me yasa zai ce a d'aga auren nan har sai nan da wata biyu, wallahi Ummi daman nasan Abba baya son aurena da Fad'ima, nayi mamaki da naga bai zo ba ashe shi abin da yake shirin ya yi min kenan" Abdulrahman ya yi maganar yana wani irin kuka mai ban tausayi, Hajiya Saratu ta kasa magana ita ma sai kuka da takeyi Aunty Hajara ce tayi k'arfin halin yin magana "Abdulrahman ka yi hak'uri kasan dai mahaifinka ba zai tab'a cewa a d'aga auren nan ba haka kawai saboda jin dad'insa tabbas ni nasan akwai babban dalilin da yasa ya fad'i hakan" Abdulrahman ya kalli Aunty Hajara da rinannun idanuwansa ya ce "Wallahi nasan babu wani dalilin da zai sa ya fad'i haka, kawai son zuciyarsa ne da kuma"..........Wata iriyar tsawa Aunty Hajara tayi masa "Kaii Abdulrahman mahaifin na ka,ka ke fad'awa haka to kayi gaggawar dawowa hayyacinka, karka dinga yin magana kamar wanda bai san abun da yake ba" Hajiya Saratu ce ta kama Abdulrahman ta zaunar dashi su ma suka zazzauna, suna rarrashinsa da maganganu masu dad'i, Amman sam Abdulrahman baya ma jin mai suke cewa dan kuwa ji yake kamar ya kashe kanshi saboda bak'in ciki.
*AMARYA FAD'IMA😂*
Fad'ima anan fad'a mata cewar mahaifin Abdulrahman ya ce a d'aga d'aurin auren sai nan da wata biyu ta fad'i k'asa sumammiya, ana aka d'auko ruwa mai sanyi a fridge aka yayyafa mata, wani dogon numfashi ta sauke take da fashewa da wani irin kuka "Na shiga uku mafarkina ya tarwatse, burina ya lallace meyasa k'addara zata zo mana a wannan ranar, ranar d'aurin aurena ta zamar min bak'ar rana" Ta k'arasa maganar tare da dafe k'irjinta saboda irin yadda ta ji yana bugawa da k'arfi, numfashinta yana kok'arin d'aukewa, Mahaifiyarta Hajiya Lami ta rumgumeta tana bubbuga mata bayanta "Haba Auta ki yi shuru kinji, insha Allahu zamuje mu da Abbanki domin mu ji dalilin da yasa aka ce za'a d'aga auren, indai mu ka ji dalilin bashi da k'arfi sosai to nayi miki alk'awari a cikin wannan satin za'a d'aura aurenki da Abdulrahman ba za mu bari ya kai wata biyu ba" Sai da ta tabbatar ta dawo dai-dai ta kuma yi shuru tana faman sauke ajiyar zuciya sannan suka fita daga d'akin suka barta daga ita sai Ikilima 'yar k'anwar mahaifiyarta shekarunsu d'aya da ita, Fad'ima ta kalli Ikilima ta ce "Sister meyasa Abban Habibina zai yi min haka?? Me na yi masa???" Ta yi magana hawaye na zuba daga cikin idanuwanta, Ikilima ta ce "Ki kwantar da hankalinki tabbas nasan akwai babban dalilin da yasa ya ce haka","Wane irin dalili ne zai saka sai a ranar d'aurin aurenmu zai ce a d'aga auren sai nan da wata biyu??" Fad'ima tayi maganar tana share hawayenta "Nima ban san me zance a kan haka ba" Ikilima tayi maganar tare da zabga tagumi, Fad'ima ta zame ta kwanta tare da lumshe idonta tana fitar da wani irin numfashi mai zafi....................✍🏾💫*To Habibaties Abdulrahman mayaudari zai haukace🤣🤣Ko me yasa Abba ya ce a janye d'aurin auren sai nan da wata biyu??🤔Fad'ima manyan gari ai baki ga komai ba ma😂ku biyoni 'yar mutan zazzau domin jin yadda zata kaya😂*
*Please👏🏽👏🏽👏🏽👏🏽👏🏽👏🏽👏🏽*
*Share it fisabilillahi🙏🏽*
*MRS BREAKER💥💫*
YOU ARE READING
TSANTSAR YAUDARA
RomanceBazan iya fada muku irin cakwakiyoyin da ke cikin littafin nan ba ku dai kawai ku biyoni 'yar mutan zazzau don jin yadda labarin yake