SHAFI NA BIYU

252 23 1
                                    

                 *GAMO!*
    
     *BILLY GALADANCHI*

           2.

Ummi tana zaune kawai taji wani mummunan faɗuwar gaba ya ziyar ce ta! "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un itace kalmar data furta a hankali, wayar salular ta ta janƴo ta kira His Excelency the president, sedai kamar ta sani bazata shiga a matsayin call ba sedai voice mail later when he is less busy ze kirata. Akalar kiranta ta mayar ta zuwa Hakeem wanda tayita faman kiran wayar sa arufe gaba ɗaya. Dik abinsa akwai layin da sam baya taɓa rufe sa shine layin sa na Family, lokaci yayi daya kamata ace sunyi landing daga lokacin da ƴakira akan zasuyi boading, meye Lagos zuwa  Abuja? Tsaki taja a hankali dannan ta tabar cikin falon tana addu'a Allah ya dawo da Hakeem lafiƴa dan gwara Abi sunyi waya kuma tasan shida Nigeria sae Next month! 

  Dayawa daga cikin mutanen dasuka fara fita a jirgin suna cen suna yawo a saman iska sanda ya tarwatse, matuƙan jirgin sunso sosai su faɗa a ruwa amma kafin sukai ga isa acikin ruwan jirgin yaƴi watsewa mafi muni, Hakeem be ƙara tuna kansa a ko'ina ba, ya sare dama yayi imanin shida rayuwa sedai a lahira idan anayi, shikenan Ummi, Abbi, Yaa mamu, Zuhar ƙanwar sa gaba ɗaya bazai ƙara ganin su ba har abada, Huddyn sa ma wani zata aurah shikenan be bar koda ƙadangaren dazai masa addu'a ba sai ummin sa, Daddy ayƴuka sun masa yawa wataƙila baze wuce shekara ba zai manta dashi, tun yana wannan tunanin har numfashi ya ajiye masa!!!!
  
    Ƙarar saukar bundiga shine abinda ya tashi ɗaukacin matan dasuke je biki daga bacci suka soma neman tseratar da rayuwar su ta hanyar shirin gudu, Nihal dake a ranaze ta kalli Khaleesat tace,

"Munshiga uku khaleesah! Me nake ji a garin nan tamkar ƙarar saukar ruwan harsashi bayaga haka kuma ga kukan mashina, karki gayamun rashin jin maganar Momy na shirin tona asiri na!  Kan khaleesah ta samu bakin bata amsa suka jiyo ƙarar bundiga a kusa da roof na ɗakin dasuke ciki, Muryar wani yana cewa "A duba ɗakin da baƙin ƴan matan suke ciki a fiddo mun su, wacce tace dani ƙurungu sarkin kawuna zanwa ciki ta haifi irina dan uban ta" Ƙirjin sune ya doka suka kalli window ɗakin da suke ciki, dama gini ne na alfarma me irin manyan windows ɗinnan dake ita amaryar ai mahaifinta wanine a Nigeria, faɗawa kawai sukayi suka fita ta window suka nausawa jejin dake bayan gidan a guje..... Allah ya tsare su dan gaba ɗaya  ɓarayin basu lula ta bayan gidan ba. Haka sukayita gudu wanda tun suna gane inda suke wulla ƙafafuwan su har suka soma kasawa suka gajiya. Neman itaciya sukayi suka zauna s gefen ta sunata faman mayar da numfarfashi a wahale, jikin su banda rawa babu abinda yakeyi sun maƙale wa juna tamkar zasu koma ajikin junan su tsabar storo, anan suka yada zango har sanda gari ya waye tatas! Nihal ce ta fara miƙewa tsaye tana ƙarewa wurin da suke kallo, ƙirjin ta ne yayi mugun dokawa tace tana kallon Khaleesah,

"Gaba ɗaƴa gonakin damukayi ta kutsowa banga ko ƙurar suba anan Khaleesah, so nake mu juya mu koma inda muka fito semu bar garin, na tabbatar zuwa yanzu sun gama duk abinda zasuyi a ƙauyen" Khaleesa dake numfashi da ƙyar dama Athsma ne da ita yace tana kallon ta

"Nihal wlh bazan koma ba, kidnappers ne koda rana operation suke yi, muyi nan gaba kaɗan na tabbatar zamu haɗu da wani ƙauye a gaba, inyaso semu nemi hanyar gari mu koma gida" Hawaye ne suka gangaro daga idanuwan Nihal masu tsananin zafi, tabbas ta kawo kanta a halaka, banda hula da doguwar rigar bacci da kuma safa baɓu abinda yake ajikinta ko ɗan kunne ɓata dashi, seko zobe wanda ya zamar mata dole zama dashi dan ta saba, Khaleesa ma kayan bacci ne ajikin ta riga da wando masu santsi amma sunada faɗi se hula da safa, sabida yanayi irin na damina akwai sanyi ya sanya suka saka kaya me yalwa irin haka, dukda dai rigar Nihar gajeran hannu ne da ita. Hannun ta takai ta share ƙwallan sannan ta ce

"Khaleesah Momyna" Itama Khaleesa kuka ta saka ta ce,
"Nima Momyna nakeso naje gunta" Rungume juna sukayi suka hau kukan kusan rabin awa sannan suka haƙura suka kama hanyar dazata ɓulle dasu suke ga!

*****************
   Saukar ruwan saman da ake me ƙarfi ne ya farkar dashi daga dogon suman dayayi wanda a zabure ya farka da salatin annabi a bakin sa, dukda ana ruwa wurin akwai yalwar haske, kallon kansa yayi kafin yabi inda yake zaune da kallo, tabbas kujera ce kuma ta jirgi sedai wannan karon yashe a cikin korayen ciyayi! A hankali ya soma tuna abubuwan dasuka faru dashi daga sanda aka soma sanarwar jirgi yana cikin matsala, ana nufi kenan wannan yayi surviving? Addu'ar dayake ta yi a lokacin da jirgin ke shirin tarwatse wa da gaske kenan Allah ya amsa, to amma wannan wurin inane? Kuma meyasa duk acikin jirgin bega ko turɓar saukar wani awurin ba saishi, kodai lahirar kenan??? Miƙewa yaƴi ya ganshi a tsaye adaidai lokacin kuma ruwa ya tsagaita sosai a wurin koma ace ya ɗauke cak! Wurin ya ƙarewa kallo tabbas shi kaɗai ne to ina sauran? Shidai a matsayin sa na musulmi ya tabbatar mutuwa akwai zafi kuma beji wannan zafin ba dan haka kuwa be mutu ba, amma to wai duk ina sauran passengers sama da ɗari da hamsin da jirgin ya ɗakko?  Yanayin shirun wurin da rashin motsin komai ya tabbatar masa cewar a jeji yake! Aljihun sa ya laluba ya janyo wayoyi ukun sa ya shiga dubawa ɗayar ma ruwa ya shiga jikinta sosai na aljihun bayan wandon sa ƙwaya biyu ne ba abinda ya semesu gaba ɗaya ko alamar network babu awurin, gauron numfashi ya sauke sannan a sukwane ya soma taku batare daya san inda zashi ba, duk kuwa takun dazeyi daya ƴana fahimtar dashi tabbas yana ƙara nitsawa ne a ƙurmin jeji maras gaba ko yamma?!! Hankalin sa fa ya tashi babu wacce ke faɗo masa sai Ummin sa daya laftawa ƙaryar zai je Lagos amma yaje sokoto kuma yana tunanin bashida wata mafita a wannan wurin, haƙƙin saɓawa iyaye kaɗai ya isa a wurgashi wutar jahannama! Taku yaji a bayan sa wanda ya sanyashi saurin waigawa sedai bega kowa ba, wannan ya sanya yace tabbas illusion ne kawai, dan abinda ya sanya yanaso yaji kenan wato ya samu abokin tafiya amma shishi kaɗai fargaba kawai zata turashi lahira!  Wani takun yaji sosai akusa dashi wannan karon wanda ya sanya ya juyo da ƙarfi yana ambatar "A'uzubillahi mina shaiɗanirrajeem" Shiru kuma tamkar beji komai ba, ya kalli ƙasan wurin ba taku sai nashi sannan kuma babu alamun kowa, nannauyan ajiyar zuciya ya sauke ya soma addu'a a hankali kafin ya juya zuwa hanyar dayake ji tamkar itace zata kaishi gari duk da dai yanaji ajikin sa akwai babbar matsala dan kuwa gabs ɗaya ya kula wurin babu wani taku dayake nuna akwai ko dabba dake bi! Shin ina ya nufa?

*****************

      Lokacin da khaleesah da Nihal suka fahimci rana tana shirin faɗuwa basuga koda alamar kiyashi a tafiyar tasu ba sesuka fahimci cewar tabbas suna cikin tsaka mai wuya, idan suka ce su koma inda suka fito ma to bazasu gane hanya ba, sabida sunyi ta sakin hanya, duk inda sukaga kwana ɗauka suke hanyar gari ce sai subi ta kawai! Nihal data gama gajiya ta galabaita ga yunwa ga kishi ruwa ta kalli Khaleesa ta ce,

"Khaleesah ajali shine abinda ya fito damu daga gida gaba ɗaya, khaleesah idan da zamuga gari agaba toda tabbas babu garin dazamu gani babu gonaki a wannan yanayin na damina, amma ki dubafa sai daji muke tsallaka babu alamar gona ko ɗaya, bama wannan ba  haba ɗaya babu alamun mutane kaiko dabbobi banaji sunabi wannan hanyar, ina mukace a haka zamu ta tafiya wlh mutuwa zamuyi" Kallon ta khaleesa tayi dan ita gaba ɗaya ma ta sare cikin tausayin kansu ta ce,

"Nihal muyi addu'a kawai, muci gaba da tafiya, in Allah yaso zamu kuɓuta" Nihal dai shiru kawai tayi tabi bayan ta amma sam bata samu nutsuwa ba.

Mom Nu'aiym ce.

Mai Buƙatar samun ci gaban littafin GAMO da kuma HUDA yayi ƙoƙarin ganin ya  nememu ta wannan hanyar.

07084161619.

GAMOWhere stories live. Discover now