SHAFI NA HUƊU

196 25 0
                                    

              *GAMO!*

*NA: BILLY GALADANCHI*

    4.
Neman hanyar gudu dukkansu sukayi sai kuma suka dakata suka waigo suna kallon juna acikin hasken dabai wadaci idanuwan su ba kasancewar duhun magriba ya rigada ya kunno kai, sun ƙurawa juna ido na wani lokaci kafin daga bisani Nihal tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un! Dan Allah aljanu kuyi haƙuri, bazan ƙara sha muku ƙwame ba, kudena zuwa a siffar mutanen dana sani bazan taɓa aminta daku ba" Juyawa tayi da gudu zata felle tana ƙwallawa ƙawarta kira a hargitse, tsayawa yayi yana kallon ta harta ɓacewa ganin sa 'Me Nihal takeyi a wannan ƙurmin jejin?' ya tambayi kansa a zuci,
'Shin wai anya ba mafarki yake ba kuwa? Amma kuma ta yiyu ba mafarkin bane ba tunda ya tabbatar ya hau jirgin kuma ya tabbatar anyi announcing  cewar jirgi ba laifi har wasu suka saka rigar iska, da sanin sa kuma sanda jirgi ya fashe, ganin sa kan kujerar jirgi a jeji ya tabbatar masa  cewar tabbas ya faɗo ne kuma Allah ya tseratar dashi. 'To kodai Nihal ma tafiyar da akace zatayi sokoto itama taje? kuma tana cikin jirgin daya faɗi dashi?' Ya ayyana a ransa, wannan tunanin kawai ya sanya yabi hanyar dayaga tabi da gudu shima yana kiran sunan ta aranshi yace 'Tabbas kenan akwai wasu mutanen da suma suka faɗo tanan daga jirgin nasu kuma Nihal tana cikin su!

  "Ki tashi mu tafi Khaleesah, nayi GAMO! Nayi gamo da aljani me siffar Sadauki Hakeem, dan Allah badan niba ki tashi mubar nan wurin kyasha ruwan daga baya" khaleesah kwata kwata ma batasan inda kanta yake ba, gaba ɗaya ta gama galabai ta, jijjigata Nihal keyi tana faman kuka har zuwa sanda ya ƙaraso wurin da suke, ganin sa akansu yasa tace "Khaleesah gashinan zai kashe mu, ki daure ki tashi mu tafi" ta ƙarashe msganar a tsaye tana shirin neman hanyar gudu, hannun ta ya riko ya janyota tazo gaban sa, hannayen sa yakai fuskarta ya waigota ta kalle sa sannan yace a hankali

"Nihal  calm down mana, bawani aljani wlh nine Hakeem, badake jirginmu ya faɗi ba daga sokoto? Jin ya ambaci faɗuwar jirgi ya sanya da sauri ta kalle sa tunawa da tayi a daren da abin ya samesu tagani a facebook jirgi ya faɗi daga sokoto zuwa Abuja, tana zare ido ta ce,

"Ban fahimta ba, kaime kake anan to? Ni kidnappers ne sukaje sacemu muka bar ƙauyen damuke muka ɓata bamu gane hanya ba muka faɗo nan" Nannauyan ajiyan xuciya ya sauke sannan ya ce,

"Daga sokoto nake, muka samu plane crash kawai se farkawa nayi na ganni akan single chair na jirgin a jeji, dama ns ɗaure kaina da belt kafin faruwar abun, nayita wahala kusan 4 days ina yawo a jejin nan" A wahale ta ɗaura kanta a kafaɗar sa tana nanata kalmar,

"Alhamdulillah! Alhamdulillah, Allah mun gode maka, dan Allah Sadaukee ka kaini gun momyna wlh tsoro nake ji! A ranshi yace 'Ina fama da kaina ma bare kuma ga mata'

"ki rika addu'a kawai, inshaa Allah zamu kuɓuta, wane hanya ne kika ce ƙauyen yake? Tana share ƙwallan idan ta tace, bazamu iya ganewa ba, kwanan mu uku muna tafiya, kuma tun farko mun sake hanya ne, munso mu koma muma amma bamu gane komai ba" Shiru yayi yama rasa tunanin da zaiyi.  Ruwan sama ne ya ƙwalle tamkar da bakin ƙwarya,  abinda yayi saurin farkar da Khaleesah ta soma buɗe bakinta don tasamu tasha koyaya ruwan yake, hannaye Nihal ta sanya tana cikawa seta sunkuya take bata, bata damu da tsananin dukan da ruwan saman yake mata ba, Hakeem yayi tsaye kawai yana kallon ta, haka tayita bata har sanda ta nuna alamun ya isheta sannan itama tasha. Cikin tausayi Hakeem ya kalle su yace "kuyi alwala an kammala magrib tunda kukaga ruwa yazo an idar da sallah" Ba musu dukkan su sukayi alwala suka fara sallah inda suka laɓe ajikin bishiyar mangoro ys jagorance su. Dukda akwai tsananin sanyi ga dukan ruwan sama sunsha hakan be hanawa khaleesah jin wani masifaffen sanyi a ƙafar taba, sannan daga bisani se wani azababben zafi ya ziyarce ta wanda atake ya haddasa mata haɗa gumi,da ƙyar taga sun idar da sallan ta miƙe a rikice se kuma ƙafar tayi mata nauyi, cikin wata murya me nuna alamar tana shan azaba ta ce,

"Nihal wani abu ya cijeni a ƙafa me tsananin raɗaɗi, ki taimakeni ji nake tamƙar zan mutu" Duhu ya rigada ya sauka sedai ruwan ya lafa, Dukkansu har Hakeem miƙewa tsaye sukayi, ya zaro wayar daya tura a cikin wandon sa na ciki gudun karta jiƙe da ruwan sama ƴa haske torchlight, nan da nan ƙafar tayi wani girma sosai, sunkuya wa yayi yana duba ƙafar ga alama lokacin sallan isha yayi sabida ruwa ya tsagaita se kawai  ya fahimci saran maciji ne, ɗagowa yayi ya kalle ta ya haske ta torchlight, tausaƴi ta bashi sosai yanda take gumi duk sanyin nan, kafin ya damu damar cewa wani abu kawai sai ihun Nihal yaji, da sauri ya kalle ta tare da haske ta a fuska,

"Sanyi sosai wani abu ya laulayemun ƙafata" Haska ƙafar yaƴi shima saida yaja baya, wani ƙatoton maciji ne, ys naɗe mata ƙafa gaba ɗaya bakinsa alamun zekai sara yana kallon babban ɗan yatsan ta,

"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un! Karki motsa Nihal macijine ɗauke numfashi zai dauka da kanshi, shine ya sari khaleesah ma" Ihu suke a tare Nihal bata motsa ba ksrya sareta amma bata fasa kuka ba, khalesah kuma tama rasa me zata ce se juyi take awurin bata ko iya ɗaga ƙafarta, gaba ɗaya Hakeem ya rasa me zaiyi, wazai kama acikin su!!!!

*Am sorry yau nayi busy ne.*

Mom Nu'aiƴm.

*✨TAURARI✨*

*WOOOHOHOOO* A inda ba ƙasa anan gaddamar kokawa🤼‍♀️🤺🤺, Akace Malam yazo salla tazo👩‍🚀. Ina gwanayen ku niga nawa Taurari masu haskawa, marubuta masu alƙalamin lu'u lu'u🖌️🖌️. Haziƙai na masu Fikrah, Shalele na masu amfani da Basira wurin sanya nishaɗi a zukatan makaran ta litattafan su, ina magana akan shahararriyar marubuciyar da akeji da ita me basira kuma fikirarriya  wato SADNAF💃🏻💃🏻. Da kuma Tauraruwar ku  datake baku nishaɗi wato BILLY GALADANCHI💃🏻💃🏻. Sunce a sanar daku cewa wannan karon sunyi tattaki zuwa wani sabon salo domin faɗakarwa da ni'imantar daku, sun ɗaura ɗamarar yaƙi domin nisha ɗantar daku kamar yadda sukayi a litattafan su da sukayi fice suka kumayi zarra a wannan shekarar *NAGA TA KAINA DA KUMA TSINTAR AYA💃🏻💃🏻.

Wannan karon ma sun shirya tsaf domin faranta muku da sababbin litattafai, Inda shahararriya kuma gwanata tace zata baku tukuicin littafin HUDA💃🏻💃🏻💃🏻 carkwai mazaƙwai.  Yayinda Haziƙa BILLY GALADANCHI tace zata baku tukuicin  littafin GAMO Dik akan farashin naira Ɗari biyar a duka biyun💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Sukace a baku wannan sassaukan lissafi.

2 books: 500
1 book: 300
VIP 2 books: 800
VIP 1 book: 500

Oya shake body💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Domin samun damar yin wuf da waɗannan litattafan ku nemi wannan lambar  07084161619.

GAMOWhere stories live. Discover now