SHAFI NA TAKWAS

187 21 1
                                    

           *GAMO!*

*NA: BILLY GALADANCHI*

*Iittafin GAMO da HUDA na kuɗi ne, dan Allah idan kina buƙatar saya ki tuntuɓi wannan lambar 07084161619.*
    8.

Hannu yakai ya rufe mata baki, sannan ya danƙwarar da kanta sukayi ƙasa, kallon ta yayi yanda take zarar ido a firgice ya girgiza mata kai a hankali alamun karta yi motsi ma, suna nan a duƙe manyan gwarazan maza suka riƙa tsallake kansu suna wucewa da gudu haka ta haɗe jikinta da nasa cikeda tsoro, hannunsa ya ɗaura saman kanta, zuciyar ta sai harbawa take sairi da sauri, tausayin Nihal sosai yake fiƴe da tunanin mai tunani. Haka suka takure saida taku ya ɗauke sannan ya jata da rarrafe suka lafe bayan wata bukkar wacce saida dare ya raba sannan suka shige ciki ganin hadari  ya gangamo. Tsugunawa sukayi har gari ya waye basu rintsa ba suna nan a tsirace dukkan su, bamaiyin magana acikin su.

   Khaleesah har gari ya waye ana mata cure cure a ƙafa, bayan an fasa an tsatse jinin aka bata wasu ruwa tayita aman jini sannan aka rufe ƙafar da wasu ganyaye da mata suka daka! Tabbas ta samu tsananin sassaucin abinda takeji daya danganci azaba amma shin me suke nufi? Waɗan nan mutanen sukuma su waye? Me suke nufi da ita? Addu'ar tane Allah ya amsa tanaga! Ƴaɓ zindirawa basa salla basa salati, basu masan annabi ya kafu ba, haka aka fito da ita da sanyin asuba aka ɗauko wani dutse aka ajiye ta akai. Wadu maza ne suka shiga rabata da kayan jikinta, inda ta fara kokawa tana kakkare jikin ta amma haka ta ƙsrfin tuwo suka rabata da rigar ta da wando suka mata zigidir! Wannan safiyar ma su Hakeem fitowa sukayi daga bukkar nan suka dawo maɓoyar su cikin sanɗa, sedai me suna fitowa suka hango an shiga ciki an fito da wasu kayan dasuka gani a bukkar ajiye an nufi wurin da khaleesah take a zaune tana makyarkyatar tsoro da kuma sanyi! Hakeem ɗauke idanshi yayi daga duban khaleesa yana tsoro idan ba sacrifice zasuyi da itaba, zakara suka ɗakko fari fat suka tsaya asaman kanta suka yankashi jinin yana tsiyaya a saman sumar kanta har zuwa jikinta, bakinta ta buɗe ta soma  karato duk wata addu'a datazo bakinta a sarari cikin murya ƙasa ƙasa. Cikin ƙatuwar tukunya tana tafasa agefe aka wurga zakaran nan sannan aka ɗakko akuya aka wurga ta ciki da ranta!  Haka matasa maza da mata suka zagaye ta wasu suna kiɗa wasu kuma rawa ana zagayar ta ciki hadda sarki. Wata ƙwarya aka ɗakko aka miƙawa sarki ya karɓa ya kurɓa, sannan ya baiwa wata mace itama tasha haka aka riƙa zagaye da ƙwaryar a tsakanin mutanen wurin sanda kowa yasha sannan aka miƙawa khaleesa, kallon ƙwaryar tayi jinine aciki tabbas tayaya zata iya shan jini? Ɓata fuska tayi sannan ta kawar da kanta daga duban ƙwaryar dama mai miƙa mata, sukayi sukayi taƙi karɓa dan haka suka sanya wani ƙato ya riƙe kanta wani ya kafa mata ƙwaryar a baki, tana turjewa yana tirsasa ta.

Hakeem bindon daya ɗakko acikin bukkar nan ya janyo sannan ya rarumo dutse madaidaici ya saita ƙwaryar ya harba! Take ta suɓuce a hannun wanda take hannun sa kuma ta tarwatse a ƙasa jinin ya watse, wani irin razana yayi cikin tsananin tsoro ya zube a ƙasa yana wani surutu da basa ganewa kuma basaji danya musu nisa. Zabgegen takobi wanda suke tunanin shine sarki ya zaro a fusace ya fille masa kai, sannan wanda yake riƙe da kanta ma ya fille kansa, jikin khaleesah ne ya ɗauki ƙyarma, lokaci guda ta saki fitsari a jikinta, gashi an mata tsirara  haka sarki yayi wata magana aka zare ta zuwa wannan bukkar da suke ɓuya kowane dare. Cikin ɗoki Hakeem yace da Nihal

"Yau da dare zamu saceta mu gudu" Tana murmushi tace

"Allah yasa su barta aciki, nizan goyata idan muka sace ta" Batare daya ce komai ba ya ƙura mata ido , a ranshi yace dama Nihal tana dariya, dama kyakkayawa ce haka? Narke fuska tayi a shagwaɓe tamkar zatayi kuka sannan tace tana langwaɓar da kanta

"kanata kallo na meye ne to?" Hannun sa yasa yakai hancinta yaja "A jejin nan idan kikamun rashin kunya miƙaki zanyi awurin maguzawan cen suyi peppersoup dake su cinye" Kallon juna suke har lokacin a narke ta ce,

"Da wannan yunwar daka barni dashi ai gwanda kawai ka miƙa ni a gunsu" Hannunta ya riƙo cikin tausayi "kiyi haƙuri Nihal inshaa Allah yau zan sama miki abinda zakici" Sauke kanta da ƙwayar idanta tayi a ƙasa cikeda jin yunwa
"wasa nake dama, ta yaya zaka samomun tunda yake babu abincin ne" Motsi sukaji kusa dasu da sauri suka waiga atare, wata macece da Namiji suke maƙale ajikin bishiya suna aikata masha'a basu masan dasu Nihal a wurin ba, sai yare suke ƙasa ƙasa cikin sambatu kuma ga alama laɓewa ne sukayi. Hakeem kawar da kansa yayi ganin Nihal.ta tsorata tana sadda kai a ƙasa cikin tsoro! Ganin takobi da kibiya yasa ya zaresu yaja hannunta a duƙe suka bar wurin. Tunda sukaga wannan Hakeem ya kula Nihal tamkar tsoron sa takeji ko kunya, cen bayan garin yajata suka zagaye wani dutse suka zauna, saida ya gama tsudying wurin sosai sannan ya ce,

"Niha zance na nemo miki abinci, ki zauna anan karki kuskura kibar nan wurin" Da sauri ta kalle sa a razane

"Zaka ƙara ɓacemun Hakeem, dan Allah karka barni, ka jirani kawai mu tafi kaji" Idanta ya kalla ta bashi tausayi sannan ya sunkuya kusa da ita yace yana riƙo hannayenta duka biyu

"Nihal ke ƙanwata ce ta kusa sosai, bazan taɓa cutar dake ba har abada, duk wani abu dazai cutar dake bazan soshi ba, ki zauna anan Nihal, hanyar dazan ɗauka ta samomiki abinci mai hatsarin gaske ce, kimun addu'a naje nakuma dawo lafiya kinji, namiki alƙawarin nanda awa ɗaya zan dawo" Jinjina masa kanta tayi alamar gamsuwa sannan ya sake hannayen.ta ya miƙe ya zaga ta hanyar dazata sadashi da wannan garin!

    A hankali ya shiga garin tsit bakajin motsin komai bakuma kajin motsin kowa! Jikin sa yana rawa danshi kanshi yasan hanyar daya ɗakko bamai ɓullewa bace ba ya kutsa har inda ya hango wani  cage cike da kaji kwana biyu da suka wuce. A hankali cikin sanɗa ya buɗe shi ya kamo kaji biyu ya mayar ya rufe sannan ya koma daga baya ta wannan hanyar domin komawa wurin Nihal yaga yanda suke kunna wuta da dutse. Murna yake sosai ya kusa isa wurin Nihal, so yake ya gasa mata su da takobin nan zai yankasu. Gabanshi kawai yaga maguzawan nan susu biyu bamai kalar imani ko tausayi akanshi haka ya duburburce ya rasa inda zai shiga ɗaya daga cikinsu ya cizgo shi saida ya yada kajin nan dama ya haɗe ƙafarsu wuri daya ya ƙille da wani ganye, sukayi gefe guda a haɗe. Wanka masa lafiyayyen mari ɗaya daga ciki yayi saida yaga taurari sannan ya soma yin faɗa cikin yaren da sam Hakeem.baya ganewa! Kansa sukayo su duka biyu tamkar zasu cinyesa ɗanye!

***********
   Nihal tana nan zaune taga shiru shiru bai dawo ba, tasani tabbas ba lafiya ba, a sukwane ta miƙe zataje neman sa saita tuna yace karta kuskura tabar wurin wannan ya sanya ta koma ta zauna! A ranta tana ayyana "anya lafiya kuwa? Saman kanta daga kan dutsen tajiyo wasu muryoyi na maza, a hankali ta ɗaga kanta tana kallonsu, waɗan nan ma kamar waɗancen ne, saidai su da yadi ajikinsu ma'ana bada fure suka rufe tsiraicin suba yadine kamar lailai fari,  kallo ɗaya zaka musu ka tabbatar waɗan nan ƴan ta'adda ne, abinda yafi bata mamaki shine hausa sukeyi rangaɗam! Saidai kuma acikin hausar zaka tsinci harshen fulanin jeji, dankuwa sunayin hausar ne tare dayin sirki da fuƙatanci. Ƙirjinta ta dafe tana ƙara matsewa da dutsen har yau bata manta muryoyin mutanen dasuka wurgota cikin wannan bala'in! Haka taja jikinta ta rakuɓe har zuwa sanda suka gama fitsarin su da rabinsa ya ƙare ajikinta sukayi shirin juyawa, tsananin ƙishiruwa ne ya haddasa wa maƙoshinta ɓushewa inda atake ta ƙware ta soma tari bilhaq! Kallon juna sukayi sannan suka sake kallon wurin tabbas ga ƙafar mutum nan a tare suka juya domin zagawa suga waye yake musu laɓel!! 

    Mom Nu'aiym.

   

9

GAMOWhere stories live. Discover now