SHAFI NA BIƳAR

205 20 0
                                    

                     *GAMO!*

     *NA: BILLY GALADANCHI*

   5.

"ki daina magana Nihal, cikin sa ne yake ciwo, yana masa sauƙi zai sake ƙafarki" Addu'a kawai ta somayi shi kuma ya sunkuya ya ɗaure ƙafar khaleesa da rigar sa daya cire, bakinsa ya saka inda akayi saran ya soma tsotse jinin dake wurin yana zubar wa. Nihal tana tsaye tamkar mutum mutumi kanta a sama idan a rufe har sanda taji macijin yana warewa a hankali a jikinta, ta bayanta ya zaga ya wuce da sauri ta dawo bayan sa tana ƙaƙƙame jikin ta a razane,  "dan Allah mubar nan wurin, wlh akwai tsananin tsoro"  baice komai ba har sanda ya gama tsotse iya abinda zai iya, wannan bazai manta ba a film yaga sunayi idan maciji ya sari mutum, a haka suka ja Khaleesa da gaba ɗaya ta gama shiga ɗimau ta suka soma tafiya da zummar barin wurin.
   Sunyi nisa sosai sukaga dare yaƴi musu, ga Khaleesah ta galabai ta, Hakeem ne ya kalli Nihal ya ce da ita,

"Nihal wannan wurin inaga anan ya dace mu kwanta, zuwa safiya saimu kama hanya" A firgice ta kalli wurin sannan ta ce,

"A fili fallau haka, idan ruwa ya sakko fa? Nisawa yayi

"Ya zamuyi to? Yarinyar nan ta gama galabai ta, bazaki gane azabar datake ciki ba wlh, tanama da dauriya sosai, saran maciji ba wasa bane ba, kuma yanada kyau muyi sallan isha" Batace komai ba dama sam ita da Hakeem ba magana sukewa juna ba, idan akwai wutar da zasu wurga juna aciki tabbas dazasu wurga juna kawai kowa ya huta da ganin ɗan uwan sa. Taimama sukayi suka taimakawa Khaleesat tayi sannan suka sallaci isha haɗe da shafa'i dakuma wutiri, Hakeem ya dade yana jere addu'oi sannan ya ɓuge da buɗa murya yana karanto karatun alk'urani mai girma a sarari da murya sama saboda su samu su samu bacci acikin nutsuwa. Gaba ɗaya kasa bacci khaleesah tayi tsabagen azabar da ƙafarta ke mata, gumi take haɗawa na fitina, tana cikin tsananin azaba, ganin duk sunyi bacci gashi kukan ma ya gagare ta ya sanya ta miƙa hannu da ƙƴar   ta bubbuga cinyar Hakeem, a hankali ya buɗe idansa dama dutsen dasuka raɓu dashi ya jingina dashi daga zaunen dayake bacci ya ɗauke sa!! Kallon ta yayi acikin hasken farin watan daya mamaye ilahirin wurin, wartsake idan sa yayi sannan ya matsa kusa da ita, har lokacin gumi take haɗawa cikin tsananin tausayi ya ce yana kallon ta,

"Sannu khaleesa kin kasa bacci ko? Cikin tsananin zafin ciwo ta ce,

"Na kasa bacci hakeem, ku taimakeni banaso in mutu a jejin nan, idan akwai wani abu daka sani na magani ka bani, wlh ina cikin tsananin azaba mara misaltuwa" Wani ƙululun baƙin ciki ya mamaye duniyar sa, wani tausayi dabai taɓa yiwa kowa irin sa ba sai ita ya taso masa daya tilasta masa haɗa ƙwalla mai zafi, saida ya haɗiyi wani yawu mai tsananin ɗaci sannan ya ce,

"Kiyi haƙuri khaleesah, da ikon Allah bazaki mutu ba, kuma zakiji sauƙi, bari gari ya waye naga ma ya soma washe wa, zan ɗebo ganyayen dake nan zan fasa na cura miki inshaa Allah zaki dace kinji" A hankali ta gyaɗa masa kanta ta koma ta kwanta abin tausayi, matsawa yaƴi kusa da ƙafar ya soma yi mata addu'ar samun sassauci danya tabbatar ajaline kaɗai zai bada sassauci raɗaɗin azabar datake ji daga saran maciji, shi tunda yake ma bai taɓa ganin maciji irin wannan ba, kalar sa yellow shar da baƙaƙen idanuwa, shi kansa daurewa kawai yayi baiyi ta kansa ba sanda ya ganshi! A hankali yana tofe ƙafar da addu'a harta samu bacci saidai kana kallonta kasan cewar tabbas acikin baccin ma azaba take sha matuƙa, zama yayi yanata addu'a tsare da ita baiko yi tunanin runtsawa ba tunda ya farka bai kums bar side ɗinta ba har gari ya soma haske, ya tashi yaƴi sallan asuba sannan yaci gaba da Azkhar yana tsare da ita bayaso ko kaɗan ya tashe ta. Sanda Nihal ta farka  ƙura musu ido tayi na wani lokaci kafin ta taso ta maso kusada Khaleesah, ƙafar ta kalla taga yanda yayi wani suntum takai hannu zata tashe ta cikin tausayi da sauri ya riƙe hannun ta suka kalli juna, ɓata fuska yayi ita kuwa ta buɗi baki ta ce,

"Lokacin..... Yatsansa ya dauka  ya ɗaura akan lips nashi tare da yin sautin shshhhh alamar tayi shiru, da mamaki ta kuma buɗe baki zata tambayi dalili cikin tsawa yace "Ke bakyaji ne wai, karki tashe ta mana" Khaleesah ɗan matashin ihun dayaƴi shine ya tashe ta cikin jimami ta farka sannan tayi salati, harara Nihal ta wurga masa cikin takaici sannan taja gajeran tsaki ta miƙe batare data koda kalle ta ba ta soma shirin yin taimamar ta, matsawa da sauri yayi kusa da khaleesa, tausayin ta yakeji kamar me, yana kallon ta da tausayi ɗauke a fuskar sa ya ce,

GAMONơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ