SHAFI NA SHIDA

193 22 0
                                    

                 *GAMO!*

     *NA: BILLƳ GALADANCHi*

"Bazan taɓa iya tafiya na barki ba khaleesah,  duke abinda zai samemu saidai ya samemu a tare, idan ma mutuwar ce khaleesa  gwanda mu mutu a tare!"

"Amma Nihal kina kallon fa ƙafar nan, kiwane wucewar daƙiƙa ɗaya da tsananin azaba yake wucewa a duniya ta, na tabbatar yau akwai azaba, idan har abinda nakeji ba zafin ɗiban rai bane ba toko tabbas ina tausaya ranar da zan ja in kuma sauke numfashi na na ƙarshe, wlh Nihal ina cin azaba dabansan yaya zan misalta miki ita ba" Hawayen idanta ta share sannan cikin ƙarfin hali tace

"Banaji zamu iya tafiyar nan babu Hakeem acikin ta, ya zamar mana dole mu neme sa, Allah ne garkuwar mu shine makamin mu, gwanda na neme sa akan na barki a wahale, zanyi alama hanyar nan zanɗan zago inga koda zamu haɗu dashi" Cikeda hope ta gyaɗa mata kai kawai ita kuwa gyara mata kwanciya tayi ta nufi jejin, da hannu take alama ta hanyar tuge hakin dake ko ina a zube, idan ta tuke saita wurgar gefe taci gaba da tafiya, a nata hikimar zata gane idan zata juyo. A haka ta kutsa cikin jejin tayi nisa sanda ta fara kiran sunan sa da ƙarfi "HAKEEM! HAKEEM!" Ta kira sunan sa yakai so ɗari, tun tana yi tana kuka har muryan ya dushashe hawayen idan ta ya ƙafe tas! Gaba ɗaya ta dena gane komai tashiga tashin hankali mara misaltuwa. Sai da taga rana ta faɗi tukunna ta nemi hanyar tafiya inda Khaleesa, ta sani yanzu ta fara buƙatar taimakon ta, a hanya sanda ta sama mata mangoro da goba data bishiyar su ta ɗeba tare da yin bismillah kafin ta ɗeba ɗin. Dik iyakar ƙoƙarin Nihal ta rikice a hanyar nan, ta tabbatar tayi shaida amma gaba ɗaya saida ta rabo inda take rabi saita dena ganin tsinkar hakin data tara da alamar inda ta tugeshi, abinda ta fahimta musamman shine inda ta baro ba'ayi ruwan sama ba amma tabbas nan yankin an tsulala ruwa mai yawan gaske, haka ta saka aranta zata gane taci gaba dabin hanyar a sukwane tana fatan ta tarar da khaleesah lafiya.

  A ɓangaren khaleesa kuwa Nihal bata haɗa mintuna 30 da tafiya ba ruwan sama ya sauka tamkar da bakin ƙwarya, tayi ƙoƙarin jan gindi taje ta laɓe ajikin bishiya amma gaba ɗaya saita kasa, dan haka anan take har ruwan ya fara harya ƙare, wani irin azababben sanyi ya kamata, nan take ta shiga makyarkyata, gaba wasu suturun kirki a jikin ta, lokaci daya khaleesa zazzaɓi ya rufe ta, wani mugun ciwon kai ya taso mata, nan take ta soma zubar da ƙwalla. Ganin ruwan ya tsagaita ya sanya ta ɗaga murya ta fara kiran "Nihal! Hakeem" Amma ita ɗinma har duhun dare ya sauka tana nan acikin taɓo da azababben sanyin dake kaɗawa babu wanda yazo ya kawo mata ɗauki. Haka tayi taimama ta dungura sallah, ga zazzaɓi tana ji kamar ta tashi sama. Wannan lokacine na tsananin damuwa awurin khaleesa, batayi zuwan rashin jin magana a ƙauyen ba, hasalima cewa tayi bazata zoba, mahaifiyar ta tace sam dole tazo tayiwa babbar ƙawarta kara ita ba mazauniya garin abuja bace, addu'a dai itace ta saka a bakinta taketa yi har sanda wani ruwan ya kuma ɓallewa, wanda atake ta samu attack na athsma, tun tana gane me ake ciki har ta shafe tatas!

   Nihal kuwa gaba ɗaya bata tunanin kanta sai ƙawarta,  idanta a rufe yake sosai akan khaleesah, ita da khaleesah sunsan junane ta hanyar ƙawarsu Amarya Sa'adatu, amma ba sanin yanzu ba, tuni suma suka ƙulla kawance saidai ba cencen ba. Nihal yarinya ce ƴar ƙwalisa mai asalin ji da kanta, tana da fara'a da kyau na nunawa sa'a gaba ɗayan ta ba fara bace ba baƙa ce irin baƙin nan na afurkawa mai sheƙi da santsi, fatarta sumul take kuma a murje kana kallon ta zakaga asalin ƴar hutu, yanayin zubin idan ta yanayi ne na idon ƴaƴan indiyawa, dan kuwa mashaaa Allah idan ta zube maka idan ta saikaji tamkar ka ruga, manya manya gasu farare tas zagayen baƙin baƙin wuluk, layin ƙasan idanta da kwallinsa yazo bata buƙatar yawan saka kwalli, hanci siriri dogo na usul ga ɗan jinjirin bakinta mai ɗauke da haƙwara farare tatas sedai ƙwaya biyu na gaba sunada tsayi, ilahirin jikinta shape ne mai asalin kyau  tanada tsayi sosai sedai batada cikar ƙirji, a takaice dai Nihal baƙa ce sosai amma me kyau na usul. A ɓangaren halayya tanada isa, son mulki, nuna cewar ita wata ce, raini ɗagin kai uwa uba kuma ji da kai, saidai kuma tanada tausayi sosai musamman akan talakawa, tana son ƙananun yara sannan kuma tana tsananin son yin kyauta, wannan halayyar ta raina mutum ya sanya tun farko Hakeem  ya tsaneta, amma fa tsanar datake masa tafi wacce yake mata dan ita ta damashi ta kuma shanye tatas a ɓangaren ƙiyayyar nan, kallo take masa na Namiji mai ji da isa, wanda baisan darajar mata ba, ita arayuwa bata burin auren mai kuɗi tana kula da yanda mahaifiyar ta ke shiga kewa duk sanda mahaifinta yayi tafiyar wata biyu ko uku, dan haka nema ta zaɓi zaid sama da Hakeem ma'aikaci a NNPC domin tasan zai samu lokaci na tattalin ta kamar yanda mazan novel sukeyi, saɓanin Hakeem dayake ɗan shugaban ƙasar su gaba ɗaya yaron da kafin zuwan mulki  ya taso sosai a gidan masu hali ƴan kasuwa, tin dama cen Hakeem ɗan masu naira ne.

   Hakeem yanda yaga ake tsula ruwa ya tabbatar wa kansa cewar matan nan suna cikin matsala, ga duhu sosai shima kenan dayake da torchlight ta waya inata gasu da gaba ɗaya suke ɗif, hankalin sa ya tashi sosai ya shiga  ruɗu, inda ana ruwan ya tsingo ganyen bishiya masu faɗi ya nannaɗe wayoyin sa ya musu maɓoya a kunkurun sa ya fito neman su acikin ruwan.

    A gida an kammala zaman makokin su duka uku, iyayen su har yau suna ɓaƙin ciki da rashin samun koda gwarsu ne, haka suka haƙura suka ɗauki abin a matsayin ƙaddara, danshi mahaifin Nihal baiko tuna akan basu sanar masa labarin tafiyar taba, tsananin baƙin cikin daya shiga a rayuwa!

   A hankali Nihal take tafiya jin taku a bayanta bayan tsagaitawar ruwan, bataso ta waigo sabida batasan dame zatayi karo ba, babu namun jeji ko ɗaya a jejin tana mamakin wannan wane irin mugun jeji ne! Tsit daga kai ne sai halinka, addu'a takeyi taga hanyar dazata sadata da ƙawarta ko zata samun nutsuwar zuciya, tabbas abokin tafiya ma rahama ne babba, dan kuwa ji take tamkar tayi fukafiki ta tashi a sama kowa ya huta! Takun sosai yake matsowa kusa da ita wannan ya matuƙar gigitar da ita, walƙiya akayi me hasken gaske, ji tayi an cirgo ta bayan rigarta ta faɗa jikin abu, lokaci ɗaya tare da wata iriyar tsawa dats gigita duniyar ta fiye da jan da akayi mata, wata razananniya ƙara da ƙwalla tare da ambatar "Wayyo momy!!!"

Mom Nu'aiym.

*✨TAURARI✨*

*WOOOHOHOOO* A inda ba ƙasa anan gaddamar kokawa🤼‍♀️🤺🤺, Akace Malam yazo salla tazo👩‍🚀. Ina gwanayen ku niga nawa Taurari masu haskawa, marubuta masu alƙalamin lu'u lu'u🖌️🖌️. Haziƙai na masu Fikrah, Shalele na masu amfani da Basira wurin sanya nishaɗi a zukatan makaran ta litattafan su, ina magana akan shahararriyar marubuciyar da akeji da ita me basira kuma fikirarriya  wato SADNAF💃🏻💃🏻. Da kuma Tauraruwar ku  datake baku nishaɗi wato BILLY GALADANCHI💃🏻💃🏻. Sunce a sanar daku cewa wannan karon sunyi tattaki zuwa wani sabon salo domin faɗakarwa da ni'imantar daku, sun ɗaura ɗamarar yaƙi domin nisha ɗantar daku kamar yadda sukayi a litattafan su da sukayi fice suka kumayi zarra a wannan shekarar *NAGA TA KAINA DA KUMA TSINTAR AYA💃🏻💃🏻.

Wannan karon ma sun shirya tsaf domin faranta muku da sababbin litattafai, Inda shahararriya kuma gwanata tace zata baku tukuicin littafin HUDA💃🏻💃🏻💃🏻 carkwai mazaƙwai.  Yayinda Haziƙa BILLY GALADANCHI tace zata baku tukuicin  littafin GAMO Dik akan farashin naira Ɗari biyar a duka biyun💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Sukace a baku wannan sassaukan lissafi.

2 books: 500
1 book: 300
VIP 2 books: 800
VIP 1 book: 500

Oya shake body💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Domin samun damar yin wuf da waɗannan litattafan ku tura kuɗin ku ta wannan lambar Acc ɗin.
2029764071.
First Bank
Nafisa Nuhu.
Shaidar biya ta wannan lambar
08033719070.
Idan kuma katin waya zaki tura,seki tura katin mtn ts wannan  lambar wayar.
07084161619
Shaidar biya ta
07084161619

Muna maraba daku.
Mungode💃🏻💃🏻💃🏻 .

  



GAMOWhere stories live. Discover now