SHAFI NA BAKWAI

220 26 3
                                    

           *GAMO!*

  *NA: BILLY GALADANCHI*!

   7.

Hannun sa yakai ya rufe mata baki sannan a hankali  Kunnenta ya raɗa "Daina magana Nihal, a gabanki akwai karen jeji kinji" Jin muryan Hakeem ya ƙara rikitar da ita, dukda yake ta tabbatar shiɗin ne saidai ta fara tunanin anya ba aljani bane yake mata gizo kamar hakeem? Yaushe yazo nan ɗin? Da sauri sauri take sauke numfashi har zuwa sanda ya saketa da kanshi.... Zabura tayi zata ruga da gudu ya kuma riƙota ta dawo jikin sa, har lokacin ta bayan sa take,

"ki nutsu idan baso kike ki ƙara ɓacewa a jejin nan ba, gaya mun yanzu ina Khaleesah, tunda na kasa mayar da kaina inda kuke yarinyar tayi tsaye a raina, na tabbatar tana shan wuya" Sauke nannauyan ajiyan zuciya tayi cikeda samun sassauci kafin tace

"Mutuwa taketa cewa zatayi, kai na fito nema, dan Allah karka bari ta mutu, wlh inason mu koma gida atare" Hannunta ya riƙe yana mejin zafin zuciyar sa fiye da da,

"Ɓata nayi Nihal, na rasa  hanyan komawa agareku, wlh da ƙyar na sameku a yanzu, ita tana ina yanzu? 

"Nayita neman hanyar komawa gareta ban samu ba, na ɓata nima a jejin nan wlh, gaba ɗaya nashiga matsala banda nutsuwa, khaleesah tana tsananin buƙata na a kusa da ita" Cikin damuwa ya ce,
"To yanzu ina mafita? Muje neman ta kawai" Haka suka rings bi inda suke tsammanin zasu ɓullo amma tafiyar harta kaisu asuba basuga koda mai kamada khaleesah ba, saima burguna da wasu ƙananun namun jeji dake tabbatar musu da cewar sun faɗo wani jejin mai namun jeji ba wancen ba!

   Khaleesat tana kwance acikin taɓo tajiyo wasu muryoyi a saman kanta dabata gane wanne iri bane, ga dai magana rangaɗaɗam amma sam ba hausa bace ba kuma turanci bane kai gaba ɗaya ma ba yarurrukan damuka saba ji bane, da ƙyar ta iya ɗaga ido ta kalle su, mutanen datake yawan gani a film, ana cewa dasu ƴan zindirawa, masu yawi tsirara da ganye kaɗai suke rufe al'aurarsu ta gaba baya ko oho, lumshe idanta tayi bayan ta ƙare musu kallo sannan a ranta ta ayyana

"Lallai ni khaleesa na haukace, yanzu kuma gizo abubuwa suke mun" Tana nan lumshe da ido har suka ɗagata sunata wasu waƙe waƙe suna kiɗa  sukayi gaba da ita, gaba ɗaya bata iya koda guttun motsi, tafiya mai nisa sukayi da ita, batasan inda zasuje da ita, ga bakunan su basu gajiya da waƙe waƙen ba. 

   Da sauri Hakeem ya riƙo hannun Nihal ya mayar da ita bayan sa, tare yi mata alama akan tayi shiru, ganin ƴan zindirawan nan ɗauke da khaleesah suna iface iface suna tsalle tsalle, cikin sanyin jiki ya ce a hankali
"Karkiyi magana dan Allah, wlh mutanen jeji ne sam basuda hankali, zasu iya kisa kai tsaye" Idon tane ya kawo ruwa a hankali ta ce,

"To me zasuwa khaleesah? Kaddai kashe ta zasuyi? Dan Allah kazo muje mu karɓo ta karsu kashe ta Hakeem" Da ssuri yace "Shshhhhhh, ki daina ɗaga murya, sannan kina haukane? Tayaya zamu tinkare su ai yankamu kawai zasuyi" A bayansa ta lafe haka suka ci gaba dabin bayansu cikin sanɗa har suka isa wani wuri mai kamada gari, gari ne ma tunda gashi nan akwai bukkoki da ɗakuna irin kara ba ginar laka ko bulo, agaban wani mutum aka ajiye khaleesa, tana kwance komai jinsa take tamkar a mafarki. Ana ajiye ta mutumin dake kan kujerar nan ya faɗo ya mata sujjada yana wasu surutai dabasu gane kan surutan nasa ba! Nihal da Hakeem kallon juna sukayi suna mamakin wannan al'amarin? Basu gama shan mamaki ba saida sukaga duk mutanen wurin sun taru sun zube suna sujjada! Hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba, Hakeem yace da Nihal

"Waɗan nan mutanen nasan labarin su, shekarun baya a Nigeria an taɓa samun mutane irin su, indai har labarin danaji gaskia ne toko tabbas muna cikin tsaka mai wuya, Abi ne da kansa ya gayamun an samu mutanen dake rayuwa a jeji su abu mai tai suke bautawa indai yakai girman akuya! Abi ya sanar dani idan suka zo abin bautar su ya mutu za'a zauna anata kuka na kwana bakwai, daga nan se a shiga jeji duk abu mai rai da aka haɗu dashi  na fsrko yana motsi shine sabon abin bauta. Nayi tunanin irin su ne saboda yace haka suke yi sunata sujjada wa koma miye, wanka da komai yi suke masa koda dabba ne kuwa, hatta sarki abun yake bautawa. Idan har ba kuskure nayi ba tabbas wancen sarkin ne kuma kinga ya zube yana mata sujjada" Zufa ce t tsatsafowa Nihal a hankali tana kallon sa  tace

"Yanzu ya zamuyi? Idan labarin ka hakane suma haka al'adar tasu yake kuma khaleesah ta faɗa hannun su, kenan dawo da ita hannun mu abune mai matuƙar wahala, bayan haka ko ƙoƙarin guduwa mukayi da ita tabbas zasu kamamu tunda sun fimu sanin kan jejin nan" Shi ɗinma zufa ya sharce a goshin sa sannan ya ce,

"Yanzu dai mu ƙara laɓewa mu barwa zuwan dare komai, yanzu ke ki adana kanki anan, niko zanbi bayan su duk inda suka kaita zan nemota inyaso cikin dare saimu sace ta mu gudu da ita" Jinjina kanta taƴi alamun gamsuwa  sannan ta ce,

"You have to be very very carefull, mutanen nan wlh basuda hankali" Murmushi yayi mata baice komai ba kawai sai gani sukayi an saka wuƙa an fasa ƙafar Khaleesah dake ciwo, take wani jini ya tartse a firgice Nihal ta ƙwalla ƙara abinda ya janyo hankalin ɗaukacin mutan garin dake wurin zuwa ga inda suka jiyo sautin muryar mace, ita ma kanta Khaleesa wata uwar ƙara ta ƙwallah jin anyi mata wannan yankan! Sarki ne cikin yaren su ya ce a duba meyayi ƙara!!!!

*Manage zan sauke wani da yamma, ina typing ya goge wannan kaɗanne karku jini shiru.*

GAMOOù les histoires vivent. Découvrez maintenant