SHAFI NA UKU

239 19 2
                                    

        *GAMO!*

*NA: BILLY GALADANCHI*

     3.

Ummi tana zaune sanarwar faɗuwar jirgi ya bayyana a faffaɗan TVn dake manne a parlor ɗinta, cikin hanzari ta miƙe tsaye tana ambatar sunan Allah wayarta da aketa kwaɗawa kira bata daga ba ta kalla cikin tashin hankali, ko wannan shine dalilin kiran?  Da azama ta ɗaga kiran wayar  tana sallama.

"Your Excelency Barka da wuni" Bata amsa gaisuwar  ba ta ce,

"Jirgi daga sokoto zuwa Abuja akace yayi bundiga  daga sama, babu mutum ɗaya daya rayu" Nisawa Commissioner of information yayi kafin ya ce,

"Wlh yau abinda muka tashi dashi kenan Ur Excelency, jirgin nan ya ɗakko sama da passengers 150, a zuwan ze zube wasu a abuja ya wuce da wasu lagos idan yaƴi juye, aciki akwai Ministan lafiya daya baro gida wato sokoto, akwai kuma kwamishinan jin daɗi na jihar kaduna, akwai mataimakin gwamnan jihar jigawa shikuwa yaje ɗaurin aure, Excelency gaba ɗaya gari ya rikice dan wasu ma yanzu muke samunmlabarin dasu aciki" "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un" ta furta a giɗime

"Wannan labari ne mafi muni a yau, zan kira shi a waya yanzu" Nan da nan ta kirashi adole yace ze dawo a ranar.

****************
   Yunwa ta gama sosai da matsalar su Nihal, gaba ɗaya sun rasa tudun dafawa, sunyi galabaita iya galabai ta har yamma basu kai ga wani gari ba. Neman wata bishiyar kuka sukayi mai kogo suka zauna a kusa da ita suna mayar da numfarfashi, seda aka daɗe sannan suka nemi cin ƴaƴan kukar ta hanyar tsinto wa su fasa su ɗakko ƙwame, haka suka zauna zaman shan ƙwame babu ruwan sha har saida azabar tsotso ya goge saman dasashin cikin bakunan su! Suna nan zaune gari ya haɗe da hadarin gaske tako ina, tsawa aka daka tare da walƙiya me hasken gaske saida suƙa ƙanƙame juna, anan sai ruwa ya fara sauka dama lokacine na tsakiyar damina. Suna nan an soma yayyafi sukaga hayaƙi irin na wutar itace a gefensu, kamar ka kunna wuta amma  ruwan sama yana duka, kusa dasu sukaji muryar ƙaramar yarinya dabazata wuce shekaru goma ba a yanayin muryar ta tana cewa,

"Baba ƙaƙamu mai ƙwame ruwan sama yana shirin kashe miki wutar girkin ki, kuma sannan kinyi baƙi" Kallon juna sukaƴi sannan suka sake baki suna kallon inda maganar ke fitowa amma ba kowa a gaban su! Gaba ɗaya gwiwowinsu sacewa sukayi suka gagara koda motsawa ne daga inda suke. Daga cikin kogon sukaji muryar Babbar mace tana cewa,
"Ai dole nazo in tattare kayana zuwa ciki, baƙi kuma babu ƙwankwasa ƙofa? Basu jira wata fitinar ba suka arce da gudun fanfalaƙi duk iyakar hadari da iskar d akeyi be hanasu ranta a nakare ba, sunyi gudu sama da awa huɗu basu huta ba har zuwa sanda ruwa ya ɗauke suka isa inda ko ruwan ba'ayi da alama ma magrib tayi dan wurin ya ɗan soma duhu, wani fili fallau suka isa suka zube suna mayarda numfarfashi tare da ambatar sunan Allah, Muryar wannan yarinyar suka ƙara ji tana ce dasu,

"Bayin Allah kun jawoni da nisa, Baba Ƙaƙamu tace inzo karɓa mata kuɗin ƙwamen da kuka sha" Daga kwancen dasuke suka soma ja da baya da mazaunan su, basa ganin yarinyar se magana take "Baba fa tace lallai ne in karɓo kafin na dawo, dan idan Kakan mu yazo kunci bashi baku biya ba dik inda kuka shiga saiya nemo ku" kallon juna sukayi acikin ƙaramin hasken dabai gama wadatar wurin ba, da sauri Khaleesat ta zare zoben hannun ta wurga inda take jiyo muryar yarinyar "Bamuda kuɗi amma ga zinare, dan Allah ki dena bibiyar mu" Alamun an ɗauki zobe kawai suka gani, sai iska mai ƙarfi data wuce ta gaban su, da sauri suka ƙanƙame juna, anan sukayi ta addu'a duk wacce suka iya sannan basu shirya ba bacci yayi awon gaba dasu.

******************
   Hakeem ya rigada ya sare da rayuwar sa, sabida tako ina ya tabbatar babu wani mahaluƙi a tattare dashi, amma tunda dare yayi gari ya sske wayewa ya lura cewar tabbas akwai namun jeji masu haɗarin gaske a jejin, dan kuwa idan beyi ƙarya ba tabbas cikin talatainin dare jiya ba komai sai hasken farin wata yaji rurar zaki, shin wai mafarki yake ko gaske ne? Shin Gaske ne tabbas wannan dashi yake Faruwa shi Abdulhakeem kokuwa? Koda wasa bai shiryawa rayuwar sa ƙarewa ajeji  ba! Daga ƙarƙashin wani ƙatoton dutse dayake zaune ya mike tsaye, wurin yakebi da kallo ta ko ina, sannan a hankali ya zaro wayar sa ya kalli agogo, har lokacin babu alamun
Network, taimama yayi ya sallaci sallan asubahi ya jere gwanayen addu'oi sannan ya miƙe yaci gaba da tafiya.

GAMOWhere stories live. Discover now