page 7

301 7 0
                                    

🅰 *S🅰N🅰DIN GROUP*🙊🙊

*Written by*
 
💅💅 *SADNAF*💞

  *PURE MOMENT OF  LIFE WRITERS*

    _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_  *P.M.L*

*A short story based on true life story*

*Page:-* 07

Manal suman zaune tayi dan bata tab'a tunanin dagaske ana irin wanan rayuwar ba da aurenka ka ringa shek'a ayarka da wani a waje d'aurewa tayi tace

*Manal*  Admin da baki zab'awa  kanki irin wanan rayuwar ba,in kinsan kina da sha'awa mai k'arfi mijinki baya iya biya miki bukatunki da kin nemi ya sauwake miki,da ki ringa aikata zina da aurenki,kinsan girman zunubin zina kuwa ballantana akai ga matar aure ce ke aikata zina subhanallahi, Admin yanzu kina nufin duk members d'in group d'inan abinda suke yi kenan?


*Hajja Kaltume* "kwarai kuwa Bazaki gane bane, Mom Haneef,amma dan Allah in tambayeki?"

*Manal* "ina jinki"

*Hajja Kaltume* "Mijinki wane irin aiki yake yi?"

*Manal*   "Mijina d'an chanji ne,a abuja,duk weekends yake zuwa"

*Hajja Kaltume*

"hmmm ke kinsan mai yake aikata wa kafin ya dawo? Mazan yanzu duk maha'inta ne,ko mijinka ba matafiyi bane cin amanarka yake,shawara zan baki wlh kibani dama na had'a ki da Baby boy da zai ringa deb'e miki k'ewa idan Mijinki baya nan," a takaice ahaka Hajja Kaltume ta ringa k'awatawa Manal dad'in hark'ar tana nuna mata ta saki jikinta ta more rayuwarta nan gaba sai ta tuba dan tasan Mijinta ma yana can ya cin amanarta"

Manal da shaidan ya Riga ya samu nassara akanta,amma sabida da sauran imaninta cewa tayi mata ita ba Zata iya huld'a da wani namijin ba,gwara tabar grp d'in in yaso zata cigaba  da zama a grp d'in *Manyan Mata Hark'a 1*tunda su chatting kawai suke basa huld'a da wasu mazan,Hajja Kaltume murmushin mugunta tayi aranta dan tasan indai zata yarda ta zauna a grp d'inta wataran zatayi nassara a kanta,Hajja Kaltumen ce mata tayi basai ta bar grp d'in ba ta cigaba da zama kawai ba zata
had'a ta da baby boy ba, Manal da zuciyarta ta gama rabuwa gida biyu,dan hudubar da Hajja Kaltume tayi mata dazun ya d'an samu gurbi a zuciyarta ce mata tayi to shikenan zata cigaba da zama a grp d'in...........................



*HAUSA NOVELS* 📚
*HAUSA NOVELS* 📚📚
*HAUSA NOVELS* 📚📚📚

A SANADIN GROUPWhere stories live. Discover now