page 35

130 6 0
                                    

🅰 *S🅰N🅰DIN GROUP*🙊🙊

*Written by*
 
💅💅 *SADNAF*💞

  *PURE MOMENT OF  LIFE WRITERS*

    _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_  *P.M.L*

*A short story based on true life story*

*Page:-* 35

Cak manal ta tsayar da kukan da take,ta zubawa wayar dake hanun Mustapha ido,yana fara ringing gabanta ya hau fad'uwa fitsari mai zafi na Neman zubo mata dan a Handsfree yasa.

Yusuf na kwance dafe da kansa a lokacin sai sallati yake dan kansa ma kamar ba ajikinsa ba,ko bud'e ido ba iya yi,yanaji wayarsa na ringing amma ya kasa tashi ya d'auka,sai da aka mishi Miss call biyar bai iya d'agawa ba,adduoi ya yafara yi Dan gani yake kamar mutuwa  zai yi,ga tunanin su Hanif da yake yi,yana so ya gansu a gefensa ko ya d'anji sanyi a ransa.

Mustapha d'agowa yayi yace "bai d'aga ba tunda kuka ga haka lailai abinda Manal tayi mishi ba k'aramin abune," Abduljabbar da rashin d'aga wayar ya masifar b'ata mishi rai a zuciye ya fara magana yana " to dan Manal ta b'ata mishi rai sai yak'i d'aga waya  wanan ai wulak'anci ne ya korota gida sanan mu kirashi ya k'i d'agawa," Manal kuwa ajiyar zuciya ta ringa saukewa da ta ga Yusuf bai d'aga ba,can kasan zuciyarta kuma tana tunanin irin fushin da Yusuf yayi da ita idan har zai iya ganin wayar Mustapha yayanta yak'i d'agawa lailai tsanar da ya mata ba k'adan bane yanzu tana ji tana gani,zata rabu da Yusuf,kuka ta fashe dashi tana "innalillahi wa inna ilahi rajiun,wayyo Allahna na janyowa kaina 🅰 S🅰N🅰DIN GROUP, Hajja Kaltume kin cuceni kinsa mijina ya tsaneni,Ton G Allah ya isa tsakanina dakai,wayyo Allahna  ina zansa kaina ya zan iya rayuwa babu mijina da 'yayana" su Mustapha sakin baki suka yi suna kallonta,Mallama Rabi ta sulmiyo daga kan kujera tana kallonta Manal kuwa duk batasan a fili tayi maganar ba, Mustapha da maganganun da tayi sun masifar d'aure masa kai d'aurewa yayi yace " kiyi mana bayani wacce hajja Kaltume?,waye ton g ?wane irin cuta kika yiwa mijinki? Kinsamu a duhu ki fito damu haske, Manal a mugun firgice ta ja da baya dan bata tab'a tunanin a fili tayi maganar ba, Mallama Rabi kuwa suman zaune tayi maganganun Manal na mata yawo a kunne,macece ita mai zurfin tunani ahankali ta had'e duk maganar da Manal tayi tasamu amsar da takeso dan ta tabbatar da amsar tace cikin karayar zuciya"Manal muamalla kike da wani  bayan da aurenki"? Ba Manal ba duk wayanda suke Palon sai da gabansu ya fad'i dan sun girgiza da jin abinda Mallama Rabin tace, Manal jikinta ne ya d'auki mugun rawa,ta zaro ido tana kallon Mallama Rabi,Mustapha yanayin Manal da ya gani ne yasa yafara gaskata maganar Mallama Rabi wani mugun tsawa ya d'aka mata yace " Manal yanzu da aurenki kike muamalla da wani awaje, innalillahi wa inna ilahi rajiun,Manal kuwa da ta ga bata da option kuka ta fashe dashi tana "wlh Sharrin shaidan ne ba halina bane,dan Allah Ku fahimceni ban tab'a aikata zina da aurena ba wlh Allah duk abinda nake yi a iya waya ne,Ku taimaka min kar na rasa raina inasan mijina" Mallama Rabi wani irin kukan kura tayi tayi kan Manal ta rufeta da duka tana kuka tana " kin cucemu kin cuci kanki,idan aka ce min zakiyi haka karya tawa zanyi,kinsan mai kika yi kuwa,na Shiga uku ni Rabi mai zan gani haka,Manal ina iliminki da yayanki da komai,kike muamalla da wani namijin a waje, Mustapha zuba mata ido kawai yayi jikinsa na rawa su Babangida kuwa sabida shock d'in abinda ta fad'a sun kasa koda kwakwaran motsi, Mallama Rabi gajiya tayi da dukanta ta koma gefe tana kuka,Mustapha kuwa da zuciyarsa kamar ta fad'o kasa wani irin yunkurawa yayi ya cakumo Manal ya hau dukanta su babangida da Abdullahi ganin ta daina motsi ne kwata kwata yasa suka mik'e da gudu suka rik'e Mustapha, Affan yayi kanta da gudu yana jijjigata, d'agowa yayi yana "shikenan kun kasheta,Aunty Manal ki tashi dan Allah", Babangida shima jijjigata ya fara yi yaga bata motsi,Mallama Rabi kuwa ganin da tayi da gaske bata motsi ne yasa tayi kanta da gudu,itama tana jijjigata,hankali a tashe tace Affan ya deb'o ruwa,affan a guje ya deb'o ruwan ya   kwara mata nan ma bata motsa ba,Mallama Rabi zubewa tayi akasa a sume,Mustapha kanta yayi da gudu shima yana jijigata,ganin itama bata motsi ne yasa ya kinkimeta yayi waje, Abduljabbar ya kinkimi Manal yabi bayansa a mota suka zubesu suka nufi asibiti,tashin hankali iya tashin hankali sun ganshi aranar...........................



*HAUSA NOVELS* 📚
*HAUSA NOVELS* 📚📚
*HAUSA NOVELS* 📚📚📚

A SANADIN GROUPWhere stories live. Discover now