page 23

166 4 0
                                    

🅰 *S🅰N🅰DIN GROUP*🙊🙊

*Written by*
 
💅💅 *SADNAF*💞

  *PURE MOMENT OF  LIFE WRITERS*

    _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_  *P.M.L*

*A short story based on true life story*

*Page:-* 23

Girgiza kai tayi da sauri tace mishi bata sha'awa har sai ya dawo,ba rok'onta ya k'ara yi da ta fad'a masa gaskiya tace mishi ba tayi har sai ya dawo,ahaka ya musu sallama ya tafi,Manal kuwa jikinta sai da yayi sanyi, in ta rufe ido,Yusuf kawai take gani lokacin da ya shiga tashin hankali akan wata ta ci amanar mijinta.

Sai da Manal tayi sati bata kula Titi ba Dan ta sha alwashin ta tuba ta daina tun kafin asirinta ya tonu,amma dayake Hajja Kaltume shu'uma ce ita da titi sai da suka San yanda suka yi suka kuma maidata ruwa.


Ton g shirun da yaji ne yasa yace "yana ji kinyi shiru"

Da sauri Manal ta fara girgiza kai tana " kayi hakuri bazan iya aikata zina da aurena ba,wanan ma abunda muke yin bansan mai yasa nake biyewa San zuciyata ba,bazan iya cin amanar mijina ba pls let cut this relationship, tsoron Allah ya shigeni,mu tuba mu daina,Wanda yake da aure Allah in ya aikata zina jifansa zaayi tayi har ya mutu,"

Ton g lashe lebb'e yayi yace inkin San wani ai baki San wani ba Allah sai na d'ana,

Kwantar da murya yayi zai fara tsarata tayi sauri ta kashe wayar, Dan har ga Allah so take ta watsar da kazamiyar rayuwanan tun kafin asirinta ya tonu Yusuf yasan mai take yi,Dan ya masifar yarda da ita, ko kiranta aka yi awaya baya gigin d'agawa ballantana akai ga ya hau mata bincike awaya,ansha turo mata texes wayarta na hanunsa bai tab'a bud'ewa ba.

Ton G ba irin Kiran da bai yiwa Manal ba amma Sam tak'i d'agawa,haka ma Hajja kaltume ke zuba mata kira amma bata d'auka ba Dan indai ta d'auka tasan zasu maidata ruwane.

Hajja kaltume ashar ta dura da ta ji abinda Ton g yace mata cewa tayi" Tj ai bata isa ba wlh sai ka d'ana ai ni burina arayuwa inga na samu partner in crime,partner ma mai wa'azi inta San wata tabbas bata San wata ba bari na gaya maka abinda zaka yi,nidai banjiyo abinda take ce mishi ba Dan k'asa tayi da murya,murmushi Ton g yayi yace shi yasa kike burgeni hajiya kina da kai hakan za'ayi.

A daren ranar ton g kiran Manal kawai yake,da Manal taga ba hak'ura zai yi da kiranta ba d'agawa tayi a fusace zata masa masifa ya kwantar da murya yafara magana "Manal tunda kika min nasiha jikina yayi sanyi nima na tuba na daina",washe baki manal tayi tace yauwa ko kai fa ,alfarma d'aya nake nema agurinki Manal"

"Ina jinka"..........................



*HAUSA NOVELS* 📚
*HAUSA NOVELS* 📚📚
*HAUSA NOVELS* 📚📚📚

A SANADIN GROUPWhere stories live. Discover now