1-2

1.7K 58 7
                                    

*SIRRIN MU*

*BY*

_✍🏾 NIMCYLUV_

      
   _Jazakillah bilkhair for taking your time to check out my book,I promise you'll never be disappointed. Well..this isn't your usual stories,And I'm loving it more and more with each passing second of my life._
 
    _I'm very thankful to all my fans for their constant love and support I am what i am because of their unconditional love!_

  Habibaties barakallahu fikuuuuuu a kakkaɓe zani so You can share and share and share to all groups fisabilillahi!



EPISODE1️⃣-2️⃣

MAIDUGURI/ BARNO
My first word on my story is SAMBISA Forest, The Sambisa Forest is a forest in Borno State, northeast Nigeria. It is in the southwestern part of Chad Basin National Park, about 60 kilometres (37 mi) southeast of Maiduguri, the capital of Borno State.
Baƙin daji ne mai girma da tsayin gaske, anyi noticing babu wani daji daya kaisa girma da both faɗi tsayi,ga wasu manyan bishiyoyi da kwazazzabe, duhun dake cikin dajin yafi gaban kwatance, kai tsaye bazan iya siffanta muku duhun sa ba, but yaya kake imagine ace ka rufe idanunka wanne kalan duhu zaka gani? To zan iya haɗa hudun cikin idanun mutum da kuma duhun dake ciki dajin SAMBISA, mugwayen dabbobi babu kalan da babu har wacce ba kayi tunanin ganinta a wajan ba zaka sameta, lokuta da dama ko da bamu da masaniya a kan dajin Sambisa but muna jin labarinsa a cikin kafar yaɗa labarai, irin su Redio,T.v, Media, uwa uba idan ka je BBC Hausa news, ko kuma ka kunna tashar aljazira, wasu da dama basu san dajin Sambisa ba, amma faruwar annoba ta farko wata BOKO HARAM, wanda kowa yasan cewa BOKO HARAM ya fara a 2002 zuwa 2009.

(BOKO HARAM Home
Politics, Law & Government
Law, Crime & Punishment
Crime, Terrorism & Counterterrorism
Boko Haram
Nigerian Islamic group
BY The Editors of Encyclopaedia Britannica View Edit History
FULL ARTICLE
Boko Haram, (Hausa: “Westernization Is Sacrilege”) byname of Jamāʿat Ahl al-Sunnah li-l-Daʿawah wa al-Jihād (Arabic: “People Committed to the Prophet’s Teachings for Propagation and Jihad”), from 2015 also called Islamic State in West Africa (ISWA) or Islamic State’s West African Province (ISWAP), Islamic sectarian movement, founded in 2002 by Muhammed Yusuf in northeastern Nigeria, that since 2009 has carried out assassinations and large-scale acts of violence in that country. The group’s initial proclaimed intent was to uproot the corruption and injustice in Nigeria, which it blamed on Western influences, and to impose Sharīʿah, or Islamic law. Later the group vowed to avenge the deaths of Yusuf and other group members, who were killed by security forces in 2009. In 2015 the group pledged allegiance to the Islamic State in Iraq and the Levant (ISIL) and took the name Islamic State (or State’s) West African Province (ISWAP; also known as Islamic State in West Africa, or ISWA). The next year the group split, with one faction retaining that name and the other reverting back to the original appellation).

Wata tafkekiyar bishiya ce,wacce take ɗauke da manyan kogona wajan goma a cikinta , ko wane kogo idan ka shiga zaka samu hanyar ɓullewa a cikin sa, banda kukan dabbobi kala daban-daban babu abinda yake tashi a cikin kogonan. can cikin baccinsa ya ji kamar ana ƙwalla kiran sunansa, kasancewarsa ba mai nauyin bacci ba, yasa ya buɗe dara daran fararen idanunsa wanda suka janye tare da yin jaa sbd tsabar baccin da yake cikin sa, har wani ciwo-ciwo ya ji kansa nayi masa, shiru yay domin yana son ya ƙara tabbatar da abinda kunnuwansa suka jiyo masa a cikin baccinsa, jin shirun yay yawa yasa yay baya kaɗan tare da sauke wata wahalalliyar ajjiyar zuciya,kana ya juya zuwa ɓangaren hagunsa, sannan ya karanta addu'ar neman tsari, ya lumshe idanunsa tare da ƙanƙame pillow dake faffaɗan ƙirjinsa,yana rufe idanunsa ya ji an ƙara kiran sunansa, tamkar mai kiran yana cikin ɗakin nasa, da sauri ya ƙara buɗe idanunsa ya shiga dube-dube amma babu abinda ya gani, lubalun dake saƙale jikin ƙofar bedroom ɗinsa ne ya fara kaɗawa sannu a hankali, harya gama kaɗawa idanunsa na kan labulan, waro manyan idanunsa yay waje saboda baƙar matashiyar buduwar mai masifar kyau da ta bayyana a gabansa, ko kaɗan bai ji tsoron ganin wannan halittar ba,sai dai yanayin baƙin fatar ta da kuma dugun baƙin gashinta wanda yake jan ƙasa kaɗai ya isa ya sanya zuciyar mutum rabewa gida biyu, abinda ya bashi mamaki yadda idanunta ya kasance baƙi sosai kamar yadda fatar jikinta take, sai dai eyes balls ɗinta blue ne sosai, ga eyes lashes ɗinta zara-zara, har taɓa girarta yake, abu mafi ɗaukar hankali a jikinta shine jajayen laɓɓanta masu kauri sosai wanda suka kasance ƙarama ye marasa faɗi, tana sanye da fararen kaya har ƙasa wanda suka rufe kofaton dake jikin ƙafarta, tattausan murmushi ta sakar masa, wanda yasa ya ƙara ware manyan idanunsa a kanta, da ace yana mugayen mafarkai kai tsaye zai iya cewa mafarkin yake, but isn't dream is real, a zahiri yake ganin komai a cikin ɗakinsa kuma a gabansa, ƙara sakar masa Murmushi tayi kafin a hankali ta miƙa masa hannunta, cikin wata murya very cool and slowly tace "zo mu je" juya mata ƙwayar idanunsa yay kana yay mata nuni da shanyayyun ƙafafuwansa, kallon ƙafar tayi sai kuma ta marairaice fuska, kafin a hankali ta taka zuwa gare sa, tana zuwa tasa zanƙalelen hannunta ta dafa ƙafaɗarsa, nan take wata guguwa mai ƙarfin gaske ta lulluɓe su, bai tashi ganinsa ba sai a cikin wannan kogon dake cikin bishiya na dajin Sambisa.

SIRRIN MUWhere stories live. Discover now