_This book is for sale it's #500 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616, ga mutan NIGER sai suyi mgn a wannan number 84506476_🆓P
EPISODE7️⃣-8️⃣Mami na barin parlourn Arjun ya sauke numfashi, tare da tura Wheelchair suka nufi cikin parlourn. Granny ce kwance saman bed tayi ɗai-ɗai sai bacci take abinta hankali kwance, da sauri Arjun ya juya ya nufi inda Sheikh yake yana shan coffee a parlour, with much shock Arjun yace "Buddy i don't understand what's going on?" A hankali Sheikh ya zame bakinsa daga kan glass cup ɗin ya ajjiye saman center table ɗin dake gabansa kafin yace "Meke nan?", Arjun yace "na je flat ɗinka na ga Granny ciki tana mopping, har muka gaisa yanzu kuma kace na ɗauko maka zuma a fridge ɗin Granny nai sallama bata amsa, hakan yasa na shiga cikin bedroom nayi expected wahala take, abun mamaki sai na sameta saman gado tana bacci da alama ko sallah asuba ba tayi ba", ya kai maganar yana kallo reaction ɗin Sheikh, sai bai ga komai ba sai ma murmushin da ya ga yanayi "Ohh!! Ni ka maida wawa ko?" da blue eye balls ɗinsa ya kalli Arjun yace "Oh! come on dear me zance maka" Arjun yace "More explanation about two of them" ware ido Sheikh yay yace "Laa adaari" cikin fusata Arjun yace "what the you mean by that?,bayan kana gidan kuma Granny ita take maka komai" taɓe baki Sheikh yay idanunsa a kan cenema yana kallon labarai a Aljazeera yace "La takaffafuu" kai tsaye Arjun yace "wallahi sai ka faɗa min", a ɗan fusace Sheikh ya kalli Arjun domin ya fara kai shi Ƙarshe bai son mita, da kuma nanata magana, calming yay yace "dole ne nasan komai? Ko zaka saka nai bincike akan abinda bana da iko dashi ne? Wallahi Arjun ka kiyayi kanka ka cigaba da shiga sabgar da babu ruwanka, ni nan ƙarya nai maka or what???" SHI ma Arjun yace "Ashe ba zakai hankali ba Imam? Baka tunanin lafiyar ka, ko ka manta situation ɗin da muke ciki, kullum kai ne zaman gida da tsaron Soldiers saboda gudun abinda zai cuce ka da kuma wanda zai sanya ai maka wani abun, amma kake ganin laifi na, wlh if i find out the truth you'll regret my dear" yana faɗin hakan ya nufi flat ɗin Granny da ido kawai Sheikh ya bisa harya ɓace wa ganinsa, Arjun na tafiya ya ci karo da wata farar mage mai kyau gwanin sha'awa ɗauke kansa yay daga kallon magen yaci gaba da tafiya, wayarsa ce ta fara ringing hakan yasa ya tsaya da tafiya kana yay answering call ɗin, yana tsaye magen ta huce da sauri ta nufi flat ɗin Granny, lokacin Granny ta farka tana ta sallami tana faɗin "A'a da mutanan gidan nan Arna za ai, babu tsoran Allah a ransu ace nai ta bacci kamar matacciya babu wanda ya kula da sabgata, kamar dai mara gata? To Allah dai yaga zuciyata ba ina sane naƙi sallar safe ba makara nayi wallahi tallahi, daman ita wacce ba'a gama sanin a wanne ɓangare take ba tuni na sallama ta, shi ma Barista dake gantalalle ne sai ya rabu dani ko na mutu ko nai rai duk uwar ubansu ɗaya, kai Allah gani gareka ni Faɗimatu da miji da mata duk babu na gari gwamma shi ƙarya yake rabtawa, ita kuma kuɗin jama'a take kwashewa tun da dai naji a banki take aiki, kai amma dai anyi gantalallun mutane wlh" tana faɗin hakan tai cikin bathroom, "ni dai wallahi cikina kamar anyi min sata, babu komai sai hanji wannan da shayarwa ne ma sai naji labari", tana shiga bathroom farar magen na shigowa cikin bedroom ɗin Granny, da ido magen tabi Granny da shi, kafin a hankali magen tai girgiza sai gashi ta koma siffar Granny tatasss babu abinda ya siffanta ta, Arjun ne ya shigo yana faɗin "Mrng Granny" kyaɓe Granny tayi tace "bana son gulma da fi'ili meye kuma Munin Ranjun? Kana gani ba'a mai dani komai a gidan nan ba,ai wlh Imamu da babu ni daya shiga uku, bashi da kowa da komai sai ni,Allah gatansan ni ce gatansa bawan Allah kenan", murmushi Arjun yay yace "haka ne fa Granny, kamar yanzu kika tashi ko makara kikai ne??" Wani kallo Granny tayi masa sai kuma tace "Yaushe ka arnantar dani Ranjun? Ka dai dinga jin tsoron Allah wallahj, babu ruwana sharrin da kai min ma ya ishe ka, yoo sharri mana da hankali na da komai shekara wajan 85 ai ba wasa kawai sai na zauna na makara a sallah, ai ni nan lokacin walaha nake jira kawai", jinjina kai kawai yay yace "bari na shige sai anjima na zo kai Buddy gidan Redio", "to to Allah ya kaimu ka gaida Sadiya" yace "za ta ji" yana faɗin hakan ya fice daga cikin bedroom ɗin, da ido ta bisa yana fita ta rikiɗe ta zama magen kamar yadda ta shigo parlon.
YOU ARE READING
SIRRIN MU
Historical Fiction_Duniya makaranta a lokacin da wasu suke shiganta a lokacin ne wasu ke barinta,wasu na zuwa Duniya wasu kuma na barin Duniya, Rayuwa kamar shafin littafi ce,baka sanin abinda yake bangwan baya dole saika buɗe shafin gaba,muna zuwa Duniya ne ba tare...