9-10

396 17 0
                                    


     _Ina ganin masu cewa ko yaya zaman Sheikh Imam hamdan Balarabe da Aljarsa Airah zai kasance??? To kada ko damu you'll be surprised Habibaties kawai a hanzarta payment free pages dai babu yawa😍👌🏾share And share and share_

Pay #500 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment
08119237616 ga ƴan Niger sai su nemi wannan number 84506476




Sheikh Imam bacci yake mai cike da nutsuwa da kwanciyar hankali, da zarar yay mutsi zai ji an ƙara shigewa jikinsa ga wani ɗumi dake ratsa jikinsa seriously zai ce ya daɗe bai yi bacci mai daɗi irinsa ba, bai tashi daga bacci ba sai da yaji muryar Granny saman kansa tana faɗin "Yau na ga abin da yafi ƙarfina ni Faɗimatu, wanne gantalallan bacci ne wannan Fisabilillahi? anayi ana nishi kamar bai zazzaɓin masharshara?" Buɗe idanunsa yay da ƙyar yana ɗan dafe kansa da yaji yana masa ciwo kallo ɗaya yay wa Granny yay saurin ɗauke kansa tare da juyawa side ɗinsa,ganin babu kowa a gefensa yasa ya kalli Granny ya ce "Granny where is she?" Keɓe baki tayi ta ce "meye kuma Shaa? Kaga Imamu babu ruwana da wannan Ingilishin naka maza tashi ka shirya Ranjun yace min yana hanya,yanzu ya kira a sailolar dake palo" shiru yay kawai yana sauke tagwayen ajiyar zuciya ji yay ransa duk babu daɗi saboda da rashin ganinta da bai ba, yana da tabbacin tafiya tayi bayan ta sashi ya yi bacci, Granny ta taimakamasa yay wanka tare da ɗaura alwala, yana gaban dressing mirror Granny na shafawa fatara versiline "haka kurum baka san darajar fata ba kace a shafa maka wani losha,meye ma wani losha fisabilillahi" Shidai bai ce komai ba domin a karo na farko kenan yaji bai ji daɗin yadda Granny ke shafa masa mai ba,ji yay gaba ɗaya yana da bambanci da wanda Airah ta shafa masa da Asuba, comp ta ɗauka ta taje masa sumar kansa ta kwanta sosai har saman goshinsa,kana tai hanyar wardrobe tana faɗin "Uhm kai kaji wani zance Imamu" idanunsu akan madubi yana kallon yadda jikinsa ya ƙara buɗewa sosai kamar wanda yake yin risilin, jin yay shiru bai magana ba yasa Granny ta ce "Idan bakai miskilanci ba ai sai Allah ya ka maka wlh, domin Ubanka Did...," Sai kuma tai shiru ta cikin madubin ya kalleta ya ce "Speak up Granny,meye Did...?" Girgiza kai tayi tace "A'a babu ruwana da gulma haramun ne wlh,daman wani zance nake som tsegun ta maka da naji Barista ya faɗa" gaba ɗaya attention ɗinsa ya bata yana faɗin "Uhm" wani tissue ɗin yadi mai masifar kyau ta ɗauko masa mai manyan zane gashi shara shara domin komai na jikinsa ana iya gani,wajansa ta ƙarasa tare da sunkuyawa ta bashi boxer ya saka sbd daga shi sai pad,tun yana yaro haka ya tasu kakarsa ke masa komai, shiyasa ba yajin akwai abinda zai iya ɓoye mata a jikinsa sai dai tsaraicinsa, farar singlet ta bashi ya zura a jikinsa bakinsa ɗauke da addu'ar sanya kaya,sai kuma wandon yadin shima yasa rigar mai ɗinkin Jamper ta bashi ya saka, sannan ta miƙa masa babbar rigar kayan, girgiza mata kai yay ya ce "No! Granny ban so" Juyawa babbar rigar tayi tace "Wallahi baka isa ba,ba zan wahalar banza ba ka ga yadda kai kyau kamar dai ɗan firazdat ko ɗan sarki? Kai ma sha Allah" Murmushi yay mata yana ɗaga hanunsa saboda parfume ɗin da take saka masa, lokacin ɗaya ƙamshin Arabian Ohud ya cika cikin bedroom ɗin nasa, harami ta ɗauko masa ya ce "bari sai Friday bani jar darata" wata hula ta bashi mai kyau tana ɗauke da gashi,a saman sumar kansa ya ɗura kana ya sanya farin bluetooth da farin glass ɗinsa yay wani kyau he look like king of Saudi Arabia, baƙin covert shoe ta saka masa a farar ƙafarsa, sai da ta gama masa komai sannan ya kalleta ya ce "Jazakillah bilkhair Granny" zama tayi ta ce "Ni dai amana zan gaya maka wlh,idan kaci kai da Allah babu ruwana da shiga hurumin Ubangiji" lumshe idanunsa yay ya ce "Uhm feel free what's is the matter?" Tagumi tai sai kuma ta ce "Barista ya kitsa abu babu shawara fa, wai Gwamna ya nemi a baka auran ƴarsa,kullum tana jin zantukan ƙaryar da kuke a redio,sai ta kamu da sonka hankalinta duk ya tashi hakan yasa Gwamna ya ce ta gaya masa tace ai Sheikh Imam hamdan take so, to ashe ma ya san Ubanka Barista shine fa ya ce da Barista yana neman sa a govmat house,to Ubanka dai ya yarda ni da waccan ɓarauniyar kuma bamu amince ba" Kallonta kawai Sheikh yake sam bai mamaki ba domin Arjun ya faɗa masa cewa ana yawan kiransa ace Imam ake nema kuma macace,wani lokacin messages harta email ɗin Arjun,to babu mamaki yarinyar ce, Granny tace "banda gantalewa ta yaran zamani yaushe mace take cewa tana son Namiji? To wlh zamanin mu sai an kaika ɗakin mijin kake sanin wa kake aura,kaga ina da shekara 9 akai min aure hatta nono wannan a ɗakin Mijin na samesa" wani ƙawataccen Murmushi Sheikh yay yace "Am hungry" Granny tace "Me kace?" Idanunsa ya mayar bakin ƙofa ya ce "yanzu 12 past 23 yunwa fa" miƙewa tayi bayan ta gama gyara wajan kana ta tura Wheelchair ɗin zuwa tsakiyar haɗaɗɗan parlour'n gidan, har gaban dinning ta ajjiyesa kana ta shiga zuba masa abin breakfast ɗin, Arish ne da meat shawarma sai tea da yaji kayan ƙamshi da na'a na'a tai tashin ƙamshi yake, bisimillah yay yasa yatsun hanunsa guda huɗu ya fara cin meat shawarma bayan ya gama cin abincinsa Granny ta kawo karamin bowl ya wanke hanunsa ya goge da tissue kana yay hamada.

SIRRIN MUWhere stories live. Discover now