17-18

430 10 0
                                    



_it's 500 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 ga ƴan Niger suyi mgn ta nan 84506476_

🆓P 
EPISODE 1️⃣7️⃣-1️⃣8️⃣

Da sauri yarinyar ta dakatar da shi ta hanyar faɗin "Yumba rukuna" (Am so tired), murmushinsu na manya Barrister yayi mata yana ƙarewa ƙyakkyawar fuskarta kallo wacce ta ƙara tafiya da zuciyarsa bai taɓa tunanin zan samu kansa da zazzafar soyayyar ƙaramar yarinyar like her ba, sai gashi in one time dukkan ƙofofin zuciyarsa sun kamu da son yarinyar. Shafa fuskarsa yayi kafin yace "let me introduce myself to u" Shiru yayi sbd ganin idanunta ya cicciko da ƙwalla ta marai-raice fuska kamar zatai kuka, a nan ya fahimci zallar shagwaɓar yarinyar ɗaurawa yayi da faɗin "My name is Barrister Hamdan Balarabe, but abokan aiki da kuma ƴan uwa na faɗa min Barrister, am the second born of my parents, ina da big bro but he's passed away shekaru masu yawa kenan, Mahaifina sunansa Balarabe Mumtah ya daɗe da rasuwa shi ma ina tare da mamana , we call her Granny, seriously i love her soo much more than anything, bayan ita sai first son ɗina yafi komai muhimmanci a gare ni, yara uku gare ni da babban ɗana Sheikh sai Fareeq mai bin Sheikh sai Auta Bahaiyya but duk suna school soon zasu dawo after holiday, ina da mata her name is Saudat but we call her Mami, nayi karatu mai yawa akan Shari'a, now am working with Sharia Court Of Appeal, sannan ina manyan contract da masu ƙasar Nigeria am the richer old man, Zaki yi farin ciki sosai zan shagwaɓa ki da kalar soyayyar manyan mutane" zuwa lokacin tuni idanunta sun kawo ruwa wanda ya sauka saman kuncinta, ware idanunsa yayi yace "Ohh my God, what exactly make you cry beauty?" Kamar zatai kuka tace "Dan Allah am going za'a min faɗa" Jinjina kai yayi yace "Ok you can go amma kimin mgn da mahaifinki please" bata ce komai ba tai gaba abinta, bayanta yabi har zuwa ƙofar gidansu tana zuwa ta shige gida, a parlour ta samu  Yakura (yayar Mama) zaune tana cin abinci brabisko da miyan yakuwa wanda ya ji nama  manya-manya, zama tayi saman kujera tana lumshe idanunta a hankali kuma ta zare airpies ɗin kunanta, ɗan tsaki taja kaɗan tana zamewa akan kujerar idanunta cike da hawaye wanda ita kanta bata san na menene ba, Yakura ce tace "Wushe(sannu)" buɗe ido tayi kafin ta miƙe tsaye tana jin zuciyarta duk ba daɗi tace "ina su Yaya Falta da Yana?" Kai tsaye Yakura tace "suna cikin ɗaki" hanyar cikin ɗakin tayi da ido kawai Yakura ta bita saboda yanayin ta da ta ga ya sauya, bata da tambaya sosai shiyasa ta ja bakinta tai shiru.

A cikin ɗaki ta samu Yana da Yaya Falta suna turara kayansu  da wani tureren ice mai ƙamshi AL'AJABU, ƙarasa shiga ciki tayi da sauri Yana tace "kin daɗe da yawa" murmushi kawai tayi masu tace "Kunyi kyau" tashi Ya Falta tayi tace "duk ƙyan mu ai bamu kama ƙafar ƙaramar ƙanwar mu Fannah ba" kwaɓe fuska tayi tace "ni duk isa ta kuke da wani kyau? Ƙyan da bashi da wani amfani" dafa shoulder ta Ya Falta tayi tace "babu wanda bai san cewa kaf family kinfi kowa kyau ba ke dai kawai wani dalili naki ya hana bawa wanda suke sonki da Aure damar masu dama ba" Yana ce tace "Abinda kike so is complicated Fannah, kowa nada tasa ƙaddarar amma haƙuri da juriyar mutum ke sawa, ƙaddarar ta zama mai sauƙi, look dani da Ya Falta mun isa good example to you, we're your sisters Ya Falta babba then me sai ke duk muna gida zaune Allah bai kawo mana mijin Aure ba, dukkan sa'aninmu suna ɗakin mazajansu, do u think we're happy?? No! Muna fatan wata rana ace muma muna ɗakin mazajan mu, amma ai bamu nuna wata alama ta damuwa ba, takura damuwa bata taɓa sawa Ubangiji ya bamu Mijin Aure"  Ya Falta tace "Muna farin ciki kin samu masu sonki zamu ragu a gaban iyayen mu amma kina wasa da damar ki? Wallahi kina cutar kanki zuciyarki na yaudarar ki, how wannan mutum zai san da zamanki? Uhm ki ɗauka ya sanki amma bazai taɓa  ko love dake ba bare Aure abeg my friend do what is right  is not is easy" kuka Fanna tasa tace "Wallahi zuciyata ba zata taɓa Yaudara ta a kansa ba, kuma insha Allah zai na samu farin ciki na da kuma muradin zuciya ta just watch and see" da kallo kawai suke bin ta domin da alama ƙanwar tasu tayi nisa bata jin kira..

SIRRIN MUWhere stories live. Discover now