MAR'ADAMS EPISODE 1

1.2K 38 13
                                    

💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Book one
Free page

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page1

......." Katanfarin   company    ne  da  tsayawa fadar   iyakarsa  bata lokacin ne   domin   mutun  bai Isa  ya  fadi  adadin  girmansa ba , hatta  shi   Karan  kanshi  mamallakin  company     bazai  ce   ga  iya   adadin girmansa   ba adalilin    kullum  sake   siyan wasu    bangaren  yake yana   hadewa  da company .
"mutane    kimanin   million   biyu da wani abu    ne   ke  aiki   a karkashin  wannan   maikatar  daake  sarrafa   karafuna   sanye da  kayan  aiki ."
mamallakin wannan company ya mallaki companies masu yawa sai dai akwai guda daya wanda ya kasance hadin gwiwa ne tun mahaifinsa na raye suke kula dashi tare da ya'yan 'yanuwa ."haka ma bayan babu ran mahaifinsa bai wuftar da al'amarin wannan company ba ya cigaba da kula dashi saboda yana matukar qaunar  company a cikin zuciyarsa dan ba  qaramin wahala mahaifinsa ya sha akansa ba kafin ya samu daukaka da kar'buwa a duniya gabadaya ba ."

A.G.C"wato Abdullahi group's company,company ne daya amsa sunansa, company né da suke da duk wani nau'in kayan sakawa ajiki ,kama daga na sarakuna ,manya attajirai ,shuwagabanin na duniya , kayanmu na gargajiya har ma dana turawa wato  suit  da kowani irin design's  na tsarkoki ,daga ko wacce kasa ka bukaci kayansu zaka samu cikin sauki sannan kuma suna zana duk irin design's din kaya da  tsarkokin da kake so har ma da zanen kanfanunnuka ,zanen  hotuna kai duk wani nau'in na zane  suna da kwararun masu zanawa  wuyarta  ka  zaba  desing's    zasu   yi maka  ."
daya  daga  cikin maaikatan   gurin  ya  dago  yana  kallon  shugaban    da aka d'aurawa  halakin  kula da ma'aikatar  karafuna wanda   isowarsa   kenan    "barka  yallabai   "barka  dai malam  mashkur  fatan komai   dai  yana tafiya  kamar  yadda  aka tsara  ?  dan  sam  bana son a samu wata  matsala  sannan  bana son a samu  sa'banin akan  karafen  can ka tabbatar  an  cigaba da samun   irin  wadan can,  sannan  wadan can kayan  Ina  son  akawo su  da  wuri  dan  mai gida  zai  .... "bai  kai ga  karasa maganarsa ba  sautin    qarar  jet  din mai gidansa ya  katseshi  hakan   yasa   a hankali   manager  malik  ya d'aga  idanunshi  dake manne  da  bakin glass  zuwa   sararin  samaniyya  cikin sauri yace     "shikenan  kaje  ka cigaba da  kula da duk masu aiki  ga mai gida nan  ya  iso ."

ADAM  TARIQ  ABDULLAH  kenan, shugaban  kafanunnunka  ATA companies ...... matashin    dan  kasuwan  da  yafi  kowani   dan kasuwan   bahaushe   kudi a  Duniya kallo daya zaka masa ka fahimci matakin   shekarunsa, bazaka kirashi da yaro ba haka zalika bazaka kirashi da dattijo ba shi din matashi ne me kimanin shekaru talatin da  bakwai a duniya fuskar shi babu yabo babu fallasa kasancewar haka yanayinsa yake, kullum haka zaka ganshi fuskar nan tashi a hade tamkar hadari sai dai na wannan lokacin ya zarta na sauran lokutan baya wanda hakan ya faru ne akan abinda ke dawainiyya da rayuwarsa."

.Adam Tariq abdullahi  wanda ake kira da (mr ATA) a  duk fadin duniya kyakkyawa ne ajin farko mai tsantsar  kamala da kamewa tattare da haiba sai dai sam bai da faraa komai cikin zafin rai da zuciya yake aiwatar wa , " rayuwarsa rayuwa ce dake da bambamci data sauran mutane , shi din mutun ne miskili mara  saukin Kai  dan idan  kayi Kuskuren shiga track dinsa zaka gane baka da wayo dan ya iya duk wani nau'i na tozarci da rashin mutunci tare da disga mutun sabanin mahaifinsa da mahaifiyarsa da sauran yanuwnasa da suka kasance masu tsanani saukin kai tausayin mutane  tare da tallafawa bayi mabukata ,fari ne sol dan babu digo tabo ko daya ajikinsa  hatta bakin kwayar idanunshi gauraye yake da fari ,dogo  ne sosai mai matsakaicin  jiki , da kyakkyawar fuska da  idanuwa , fatar jikinsa na ya'yan masu kudi  sai sheiki yake daga samansa har kasansa babu makusa  sannan babu alamun babu a tattare dashi yana da matakin karatu na Phd akan kasuwanci kuma har lokacin yana kan karatu bai ajiye ba ,shine ya tattara gabadaya  kyawun   mahaifiyarsa  hajiya zulaiheart da mahaifinsa marigayi  barrister Kuma shararen dan kasuwa Alhaji Tariq Abdullah ."

MAR'ADAMSWhere stories live. Discover now