MARADAMS EPISODE 9

153 11 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Book one
Free page

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page9

"Cike da kulawa  mami ta tsiyaya masa ruwa a glass cup ta Kai bakinsa "sorry dear kabi ahankali ya kur'bi kad'an yana furzar da numfashi mai zafi  ya dafe goshinsa  kusan minti goma yana dafe da goshinsa yana jin wani zallar 'bacin rai ,da zai iya daya saka mata kuka a yadda yake jin zuciyarsa dame take son yaji ? mami kuwa zuba masa idanuwanta tayi tana faman jero masa  sannu  har sai dataga ya dawo daidai sai dai  bai iya cigaba da cin abinci ba ya d'an zame jikinsa kad'an akan kujera  yayi  rigingine  ya runtse lumtsatsun idanunshi  gam yana  jin   radadi." muryarta a sanyaye tace "ka qarasa cin abinci  "am okay sweetheart ! ya fad'a atakaice batare daya bude idanunshi ba .
"Numfasawa tayi ta kira daya daga cikin masu aiki ta tattara kayan abinci  sannan  ta mike ta shiga bedroom dinta tana tunanin yadda zata bullowa ATA  sosai kwakwaluwarta  tashiga neman mafuta dan dole tasan abun yi matukar ya nemi ya zuba mata kasa a ido zai ga bacin ranta ."

     Mr ATA ya cigaba da zama yana kallon tashar CNN ".Kusan awa daya da wasu mintuna yana zaune yana nazarin maganar mami "shine zai kira yarinyar da sunan zance ?"no no !! it can be possible koda  zai iya hakan sai dai  ba daita ba domin bata kai wannan matsayin ba ."a natse  ya mike ya shiga bedroom dinsa yayi taku cikin falon wanda babu motsin komai sai na'urori  sanyaya wuri kai tsaye bedroom dinsa ya nufa yana furzar da hucin iska mai zafi daga bakinsa wai kamar shi ne zai kira yarinyar zance wannan lamari na sake bata masa rai da daga masa hankali amman ya tabbatarwa kanshi bazai ta'ba iyawa ba yana da raayin shi sannan ga  karfin iko da yake dashi  dan  haka bai ga abinda zai sa shi kiranta da sunan zance ba  koda kuwa zasu shekara dubu ne hakazalika ko  auren sukai a haka zata qare rayuwarta  batare da samun farinciki ba ."

ahankali tamkar mara lafiya ya qarasa bakin gado ya soma  cire kayan  jikinsa yana  mamakin mami "hakika tana qaunar  yarinyar dayawa wanda hakan yasa tsanar yarinyar yake sake ninkuwa a zuciyars a hankali ya shiga wanka  ya fito ya sanya wasu hadaddun kayan bacci wando da riga farare sol  ya feshe ilahirin jikinsa da turaruka masu sanyin kamshi ya kashe wayoyinsa guda biyu  ya bar na business dinsa  sannan ya kashe tv ya haye gadonsa ya lullu'be rabin jikinsa da bargo mai taushi yana runtse idanuwanshi da princess dinsa ya soma cin karo sanye cikin fararen kaya sol tana sakar masa murmushinta mai rikitarwa ya tsura mata Ido."
duk da idanunshi a runtse suke amman shi ganinsu yake abude " ya za'a yi na gaki ? ya furta yana tsareta da lumtsatsun idanunshi  sai daya fesar da iska ya sake motsa lip's dinsa "da zanganki da kin fahimci Ina sonki fiyye da komai , me kike so nayi ki yarda Ina sonki ki bayyana min kanki , ina son ki fada min inda zangaki please, zanyi komai akanki ko cewa kikayi na mutu a yanzu zanyi ya Kai hannunsa yana shafa beautiful face dinta ."

idanunta na kallonsa ta sauko ta jingina da bangon daki ya mike ya tsaya a gabanta suna fuskantar juna tana kokarin juya masa baya da sauri ya rikota ya matsota sosai kmr zai shige jikinta har dukiyar fulaninta  na gogan qirjinsa " ina son ki kasance tare dani ki bari na ganki azahiri Koda sau daya ne ya karasa maganar suna fuskanta  juna " idan Ina kallonki sai naga kin fi kowace mace kyau a duniya idanunki , lip's dinki you look so beautiful....."
ya ware hannuwansa duka yana k'okarin rungumeta jin ya rungumi iska ya bude idanunshi fesss yana kallon d'akin kamekame da jikinsa, baya felling din kowace mace sai ita ,baya son kowace mace sai ita, da zai mallaketa tabbas da shi kadai yasan irin rikon da zai mata, zai yi mata riko mai karfi  ta yadda babu abinda zai rabasu."

MAR'ADAMSWhere stories live. Discover now