MARADAMS EPISODE 3

230 11 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
   MAR'ADAMS
   💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Book one
Free page

*AYSHA A BAGUDO*
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page3

......da wani irin sauri mr ATA  yayi saurin d'auke kwayar idanunshi akansu yana  juya baya tare da jin wani zafi mai tattare da bakin ciki, gabadaya ya rasa me Ke masa dadi arayuwarsa a halin yanzu babu fuskar daya tsani gani  kamar fuskarta ."daga  Inda maryam take bata sake yunkurin qara taku daya ba ta cigaba da tsayuwa a waje daya qirjinta na bugawa da matsanancin karfin gaske  sbd tsananin tsoronsa ."wannan dalili   yasa  dole shima muhd bello ya tsaya anan  suka qarasa maganarsu ta juya  da  sauri ta koma ciki ranta duk babu dadi kallonta nana hauwa'u tayi tace " ba dai har kin dawo ba ? ta fad'a haka ne sanin da tayi duk lokacin da suka ke'be da ya muhd bello suna daukar lokaci suna tautaunawa dan jininsu ya had'u sosai dashi ."

maryam bata ce mata uffan ba tsabar bakinciki dake kunshe acikin  zuciyarta nana hauwa'u ta cigaba da magana tana dubanta a tsanake "halan ya adam na waje ne  naga kin shigo fuskarki wani iri ? ta'be lip's dinta tayi tana cewa " ai kema kinsani idan ba ganinsa ba me zai sa fuskata tayi haka ta sauke naunayen ajiyar zuciya " sister na rasa dalilin wannan tsana da ya adam yayi min ,wannan abu na matukar ci min rai ina jin kamar na tattara na bar gidan nan na huta da ganin irin kallon tsanar da yake   min kamar ni kadai ce acikin gidan  nan ? " tsana kamar ya kashe ni."

"haba haba !! sister dan me zaki  fadi  haka?" ai ba ke kadai yakewa haka ba , ki daukeni misali ma kawai ya isa ki kwantar da hankalinki ,  ba ke kadai ya adam yakewa haka ba shifa tsanarsa kowa yake  wa "maryam ta sake tabe lip's dinta "kowa yake wa amman wallahi nawa yafi na kowa nifa ko kallona baya qaunar yayi  na rasa  me na tsare masa  arayuwa kamar fa ya kasheni haka nake gani acikin kwayar idanunshi nana hauwa'u tai murmushi kawai "kisan ma  abinda ya qara kona min rai ne ?nana hauwa ta girgiza mata kai "alamun a'a " wai yana hangomu nida ya muhd bello mutumin nan ya juya mana baya da sauri kamar yaga wani mugun abu ,wallahi bakiji yadda na muzanta ba gabadaya kasa cigaba da tafiya nayi " nana hauwa'u ta kamota zuwa Kan kujerar da take zaune ta zaunar daita  tana murmushi a hankali  ta shiga kwantar mata da hankali tana kawo mata misalai iri iri dan bata son abinda zai sa maryam ta bar gidan dan ko babu komai abubuwanta na social media na sakata nishadi shiru kawai maryam tayi tana sauraronta ."

muhd bello ya k'araso Inda Mr ATA yake tsaye ya Kai hannunsa d'aya ya dafa kafad'arsa ya juyo dashi a hankali ya tsura masa idanunshi fuskarsa kwance da murnushi yace "why ATA ? "me yasa kake quntatawa rayuwarka ?"me maryam ta rasa ? "me yasa bazaka bi zabin mahaifiyarka da yan'uwanka ba ? ya lumshe lumtsatsun idanunshi  yana furzar da iska me zafi daga bakinsa "kasan komai  akaina m.b  tun daga farkon rayuwata har zuwa yanzu da nake tsaye a gabanka babu abinda baka sani ba ..."
Na sani ATA ! ya fad'a yana sake matsoshi sosai " Amman at least ka duba lamarin mahaifiyarka  da yan'uwanka  sun dauki tsawon lokaci da  baka dama amman shiru babu wani bayani amman yanzu tunda suna sonka da maryam ka amince masu ka sota ."

shiru mr ATA yayi yana masa wani irin kallon up and down "ka amince masu ka sota " kwalkwa
luwarsa ta maimaita masa abinda ya fad'a yanzu kafin a hankali ya kai hannunsa daidai saitin zuciyarsa da yaji bugawarsa yana qaruwa sakamakon furucin muhd bello ,bai an kara ba yaji sautin muryar muhd bello ya cigaba da magana " itama maryam din bata san da maganar ba a yanayin yadda mami ke maganar zaka fahimci hukuncinta ne ta yanke akanka kuma ina da tabbacin ko tasani bazata ki ba, biyyawa kawai zatayi ta aureka koda ranta bai so "shawarata ka amince da aurenta yarinyar nan tana da natsuwa da hankali sosai bazata baka matsala ba ,sannan tana da ilimi tana da kirki daidai nata uwa Uba jininku daya daita abinda yayi ka shi yayita, shi abinda kake gani acikin rayuwarka ba lallai ya zamo gaskiya ba dan ba kowani mafar......"

MAR'ADAMSWhere stories live. Discover now