💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS
AYSHABAGUDO
bismillahirrahmanirrahimWannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 12
Aunty tayi shiru tana duban maryama yanayinta kamar kazar da'aka tsamo cikin ruwa gaba daya alamu sun nuna gajiya a tattare daita amman dan karfin halin irin nata take boye mata damuwarta , hawayen da suka cicciko acikin kwarnin idanunta tayi qoqarin maidawa tana danne damuwarta saboda farinciki diyarta ."
ahankali ta dauke kwayar idanunta aKan tilon diyarta zuwa wani bangare dabam tana tunanin rayuwa da abubuwan da sukai ta faruwa daita ta sha wahala arayuwarta shiyasa batason maryama ta sha wahala irin wanda ta sha ,wannan aikin da aunty salma kesata yana matukar ta'ba zuciyarta domin ko ita da tayi sanadiyyar zuwanta duniya bata sakata aiki haka koda tace zatayi ma bata yarda ta bar mata tayi ita kadai sai dai suyi a tare amman bata da yadda zatayi da rayuwata dan bazata iya hanawa ba "tabbas bata da yadda zatayi kuma bata isa ta hanata ba tunda zaman gidan ya zame mata dole dan bata son rasa yaranta kuma bata son ta koma ga danginta ." tayi maganar a kasan ranta .maryama ta kalli mahaifiyarta duk da bata san me ya canza yanayinta ba amman tasan meke yawo acikin kwakwaluwarta ta matsota sosai tana jijiga Aunty wacce tayi nisa cikin tunanin rayuwa "meke damunki Aunty ?firgigib ta dawo haiyacinta tana dubanta duba mai tattare da damuwa tana cewa " babu abinda Ke damuna princess " ta fad'a tana mai jin tausayinta domin dai duk halin da suka tsinci kansu aciki itace sila, itace silar janyowa ya'yanta rayuwar wahala wacce bata kamacesu ba duk wani abu daya faru da ya'yanta itace ta janyo masu adalilin zunzurutun Kaunar data nunawa mahaifinsu ya janyo mata rasa komai domin ta zabi
Mahaifinsu ta bar danginta wanda yasa kowa acikin danginta yaji babu dadi akanta.""me yasa kowa ya tsanemu acikin gidan nan ?" bayan mahaifinmu da granny da umma da abba babu mai qaunarmu acikin gidan nan gashi abba ya rasu ya barmu kamar yadda mahaifinmu ya barmu why Aunty ?me yasa basa qaunarmu ? "Me yasa suka tsanemu ko kin yi masu wani laifi ne ?ina son nasan abinda ya kawo wannan kiyayyar ?shiru kawai Aunty tayi tana dubanta dan bata da abinda zata fad'a mata domin kare kanta maryama yarinya ce da bata wuce shekara ashirin a duniya ba but she's smart in ance smart ana nufin mutun wanda ya kasance mai tsananin hankalin da kwakwaluwa tare da kaifin baseera sannan yarinya ce mai fadar gsky komai d'acinta zata fad'a she's very shap akan komai dan wani lokaci har mamaki take bata idan tayi wani abu kanta naja sosai fiyye da yadda take tunanin tasan muddin taji ta zabi mahaifinta ne akan iyayenta yasa dangita suka juya mata baya tabbas zata fad'a mata gskyr data kasa amsa daga ahlinta "Ina danginki suke Aunty ?ta jeho mata tambayar data nemi bugar mata da zuciya tana mai d'aura kanta a saman cinyarta ."
tsura mata ido tayi tana kallonta kafin daga bisani tace "suna nan ! "suna nan amman me yasa bakya zuwa inda suke kamar yadda Aunty salma keyi ?"babu komai "ta bata amsa atakaice tana jin wani tuttukin bakinciki acikin ranta mai tattare da damuwa "Aunty karki ce babu komai lallai akwai dalili akwai abinda yasa bakya son zuwa inda suke har yasa bamu sansu ba ,mahaifiya mahaifi yan'uwa duk ba abun wasa bane domin suna da matukar mahimanci arayuwar mutun ."
Naunayen ajiyar zuciya aunty ta sauke tana sake tsura mata ido "dan baki san abinda suka aikata gareni bane maryama shiyasa zaki fadi haka ta fad'a hk a zuciyarta " ahlinki suna da matukar mahimanci sannan suna da hakki akanki most especially iyaye yana da kyau a dinga basu hakinsu domin hakan zai samarwa mai yi kwanciyar hankali ,meye acikin duniyar da babu albarka iyaye acikinta ?yadda kike iya hakurin rashin zuwa ga iyayenki bazan iya barinki daidai da second daya batare dana daura kwayar idanuna akanki ba saboda qaunar da nake miki ina sonki aunty fiyye da komai dake cikin duniyar nan dan haka Kiyi qoqarin kije garesu nasan suma zuciyoyinsu na cike da kewarki da qaunarki tunda kika haifeni na girma na kai wannan shekarun ban ta'ba ganin ranar da kika shirya kika ce zakije ga ahlinki ba , kullum muna cikin dangin dady cikin kaskanci da wulakanci ya kamata ko sau daya ne muje domin nima ina son ganinsu ina son ganin danginki zaki je ga ahlinki ? tayi mata tmbyr tana mai tsura mata kyawawan idanunta masu matukar kyau ."
YOU ARE READING
MAR'ADAMS
Romancelabari ne Mai dauke da soyayya , ilimantarwa, fadakarwa, nishantarwa jajicewar rayuwa .