MARADAM EPISODE 2

291 12 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
   MAR'ADAMS
   💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Book one
Free page

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page2
....Da misalin karfe goma na safiyar ranar asabar mr ATA ya sauko daga saman dakinsa jikinsa sanye da bakin riga da wondo baki yayinda kafafunsa ke sanye cikin wasu hadaddun silifas masu matukar kyau suma black kana gani kasan masu tsada ne haka idanunshi suna makale da farin glass wanda ya zame masa tamkar na gado, ko bacci wani lokacin dashi yake sai idan Mahaifiyarsa ta shigo ta gansa dashi ta cire masa ,yayi kyau sosai acikin shigar kasancewarsa fari ."ya qaraso ya dauki jarida daily trust da'aka ajiye masa ya samu wuri ya zauna akan doguwar kujera mai zaman mutun uku ya daura kafarsa daya a kan daya ya shiga duba jarida "
yana zaune nana da maryam suka fito suna magana akan inda mai decoration zatai decorate din birthday din maryam dana hanan diyar Aunty zabiba kanwar mr ATA da zaa gabatar a ranar ." suna gama qarasowa parlour'n suka gansa zaune Kmr an dasashi a gurin ."suka bishi da kallo suna jin faduwar gaba babu yadda zaka ga mr ATA gabanka bai fadi ba ko kai waye kuwa saboda tsananin tsare gida  , ya gansu amman yayi tamkar bai san da wasu halitta tsaye a wurin ba ,nan take kowacce ta shiga taitayinta jiki a sanyaye suka hada baki wurin gaishesa "good morning ya adam" ? sai daya dauki second goma batare daya amsa ba har sun cire rai da zai amsa suka jiyo sautin muryarsa daga can kasan makoshi "morning ! ya amsa batare daya dago ya dubesu ba ."

Naunayen ajiyar zuciya maryam ta sauke dan tasan darajar sister taci yasa har ya amsa gaisuwar dan da ita kadai ta gaisheshi bazai ta'ba amsawa ba Kai tsaye hanyar kitchen suka nufa domin bawa masu aiki umarnin  abinda zasuyi na birthday duk da sauran abubuwa masu wuya tun jiya a kammala  ,duk abinda suke hankalin maryam na kan mr ATA bini bini ta kallesa taja tsaki acikin ranta dan hakan nan kwanaki take jin matsanancin tsanarsa a ranta dan tasha alwashin tunda bai qaunarta itama bazata qaunacesa ba mai qaunarsa ma baso ."

Sai dai duk da wannan tsanar da tayi masa ta kasa dauke kwayar danunta akanshi har sanda ya mike ya isa dining table ya dauki cup din coffee dinsa baki mai shegen kyau da gani daga wata kasar yazo dashi , a natse ya sake dawowa mazauninsa ya zauna fuskar nan tashi a hade tamkar wanda ake masa wahayi da bacin rai."
"tunda aka haifeta ta bude idanunta akansa bata ta'ba ganin dariyarsa ba ,kuma haka kowa yake fad'a acikin family's ,komai zaayi na dariya sai dai ya bata rai yaja tsaki tare da cewa nonsense ko rubbish ga shegen miskilanci wani lokaci halinsa na dan burgeta Irin mijin da take so kenan mai matukar kamewa da sanin ciwon kai, dan gsky ita dai nmj mai yawon surutu ko shiga abinda bai shafesa ba yawon fara'a matsala ne agurinta bata so sai dai  nashi yayi yawa ko dan murmushin nan ba yayi matukar kaga fuskarsa a d'an sake to yana tare da mami ne shima wani lokacin bata gane kansa kome zatayi bazai sakar mata fuska ba ."

byn ya sha kad'an ya ajiye cup ya cigaba da abinda yake har sanda hjy Zulaihat ta fito itama ta shiga kitchen yana nan zaune ya tsurawa jarida idanunshi , al'ameen daya daga cikin securities na bakin get
ya shigo bakinsa dauke da sallama sannan cike da girmamawa hannunsa rike da white lailon da box blue and white ,mr ATA ya amsa sallamar aciki yana mai d'ago kansa ahankali ya zubawa al'ameen lumtsatsun idanunshi "Alameen ya qaraso gabansa kad'an ya rusuna "barka da safiya yalla'bai "mr ATA ya gyada masa kai kawai batare daya amsa ba .
" amm ga sako wai inji Ana's" mr ATA ya d'an kankace lumtsatsun idanushi yana bukatar qarin bayani daga bakin al'ameen,alameen yayi sauri yace "sakon hjy maryam ne ita yace abawa "shiru mr ATA yayi yana kallonsa da sakon hannunsa kamar bazai ce komai ba sai kuma ya nuna masa kan table din dake gabansa yana jan tsaki a fili al'ameen ya ajiye ya juya ya fice da sauri ya kama gabansa."

MAR'ADAMSWhere stories live. Discover now