💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Book one
Free page*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
Arewabooks username
Ayshabagudo
bismillahirrahmanirrahimWannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page5
" da misalin karfe tara na daren ranar
Juma'a mr ATA ya fito daga bathroom jikinsa
sanye da rigar wanka iya gwiwarsa yayinda hannunsa d'aya ke rike da white towel yana goge kanshi zuwa wuyansa ,ahankali ya qarasa gaban mirrow ya tsaya yana kallon kyakkyawar fuskarsa yana qoqarin zare rigar jikinsa ."shiru yayi yana kallon faffad'an qirjinsa dake kwance da laulausan suma tamkar na jariri sabuwar haihuwa ga Kan nipple's dinsa a tsaye makale da qirjinsa sai sheki suke, babu lafiyayyar macen da zata gansa a haka bataji sha'awarta ta motsa ba saboda kyawun cikar halittar da allah yayi masa ."kusan minti goma ya dauka tsaye yana qarewa kansa kallo kafin daga bisani ya juya a natse ya koma bathroom ." ko cikakken second uku bai yi ba ya fito ya d'auki kwalbar bodyspry ya feshe ilahirin jikinsa ya saka white singlet boxer's sannan ya shirya cikin wasu hadaddun kananan kaya t shirt fari sol da dogon wando baki , ya kai hannu inda tsadadden Turarensa (Reed ) yake ya d'auka ya feshe kayan jikinsa , ta koina a sansar jikinsa kamshi yake tashi mai sanyi da tada tsumin shaawa." ya ajiye kwalbar turaren a mazauninsa yasa hannun ya kwashe wayoyin business dinsa guda biyu ya juya ya fito daga cikin dakin tare da janyo kofa ."
a natse yake saukowa daga Kan matattakala bene hannunsa daya soke cikin aljihun wondonsa kai tsaye yana gama saukowa ya qarasa dining area ya zauna akan d'aya daga cikin kujerun dining yana sauke numfashi kana ya ajiye wayoyinsa akan table ."ahankali sanyin ac dake aiki a parlour'n ya dinga ratsa sansar jikinsa ,lumshe lumtsatsun idanunshi yayi yana ciza gefen lip's dinsa , cikin haka mami ta fito daga kitchen ta soma hidimar zuba masa abinci ,dan shi baya son masu aiki na shiga huruminsa saboda Allah yayi shi mai tsananin tsabta da kyakyami , shiyasa ba koina yake cin abinci ba, ko fuskar abinci ya kalla yaga yayi wani iri to komai za'a yi bazai ci ba shiyasa duk sanda zai ci wani abu mahaifiyarsa ce kadai ke masa hidima abinci wannan halin kuwa ya samo ne daga gurin kankansa alhaji abdallah dan shima ba abincin kowa yake ci ba sai wanda yayi masa ."
bayan ta zuba masa jollof din shikafa yar waje wacce taji pepper chicken ta hada masa coffee dinsa na gado ta ajiye masa a gabansa sannan ta koma ta zauna a kujerar dake fuskantarsa tana dubansa a tsanake tace "kasan wani abu my love ? ta tambayesa idanunta na kanshi ya d'an girgiza mata kansa batare da yace komai ba sai ma lumshe lumtsatsun idanunshi da yayi yana jiran yaji me zatace .Allah Allah !!nake kayi aure na huta da yi maka hidima "shiru yayi bai yi magana ba yana jiran yaji spoon din abinci bakinsa amman yaji shiru har tsawon second goma sai ma maganar aure da yaji ta cigaba dayi masa wanda hakan Ke mugun bata masa rai tare da dagula masa lissafi dan a halin yanzu idan akwai abinda yafi tsana bai wuce maganar auren da take bukatar yayi ba gashi burinta ba abu bane dake cikin lissafinsa ."
shiru yay har wata second biyar tazo ta wuce bai ga alamun tana da niyyar bashi abinci ba dan haka ya bud'e lumtsatsun idanuwanshi a hankali ya tsura mata yana kallonta fuskarsa a shagwabe kamar koda yaushe idan yana gabanta "kana wani kallona da wad'an nan idanuwan naka masu firgita mutane ai gsky na fad'a ina bukatar na huta da maka hidima ." muryarsa a kasalance ta fito tamkar mai koyon magana "haba my sweetheart ki daina fadar haka mana yanzu baki jin tsoron wani yaji kina cewa kin gaji dani ?ni bance na gaji da kai ba karka canza min magana hidima nace ta fad'a tana hararasa wanda da gani na soyayya ce." ya sauke naunayen ajiyar zuciya still kwayar idanunshi na kanta sai daya numfasa sannan ya sake motsa lip's dinsa "sweetheart ! ya kira sunanta a shagwabe ta kalleshi kawai tana jiran taji abinda zai ce " ai ko na yi aure bazan daina cin abinci daga hannunki ba domin dashi na saba ."
YOU ARE READING
MAR'ADAMS
Romancelabari ne Mai dauke da soyayya , ilimantarwa, fadakarwa, nishantarwa jajicewar rayuwa .