*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_**Follow us@facebook, kundin hikima writers association*
*_DOCTOR ZAHRAH🏥👩⚕️💉_*
*_Written by fateeyzah_*😍😍
*follow me on wattpad@Fateeyzah**_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad_* ❤
_Wannan page din nawane fateema zahrah Muhammad sani(fateeyzah)_
_I am +1, happy birthday to me, Allah ya biyamini bukatuna na Alkhairi, ya bani abunda nake nema duniya da lahira, ya tabbatar mun da Alkhairi acikin rayuwata, ya kara shiryatar dani hanya madaidaiciya, ameen._
*_Bismillahir rahmanir rahim_*
*_Page 06 to 10_*
Ajiye bag dinta tayi da jakar laptop dinta akan table din, sannan ta cire labcoat dinta tare da rataye ta a jikin hanger, tukunna ta nufi kujerar dake gaban table din ta zauna tare da jawo jakar laptop dinta, hakan yayi dai² da karar telephone din dake kan table din, sai da taja tsaki tukunnan ta yi receiving tare da sawa a speaker, daga cikin telephone dinne wata murya mai taushi tace "good morning Doctor, you are speaking with sister Ganiyat, (ina kwana likita, kina magana ne da sister Ganiyat)".
Cikin zakakkiyar muryar ta ta amsa da "morning, how can i help u?, ( lafiya, dame zan iya taimakonki?)"
"Please Doctor we need you urgent in emergency ward, one of our patient is in crital condition, (don Allah likita muna bukatanki da sauri a emergency ward, daya daga cikin majinyacinmu ne yake cikin matsala)" Ganiyat ta amsa ta cikin muryarta mai taushi.
Cikin alamun damuwar wanda fuskarta ta nuna tace" when is he admitted?,(yaushe aka kwantar dashi?)".
"He was admitted last night (an kwantar dashi jiya da daddare)"
"I am coming, give me few minutes,(ina zuwa, ki bani dan mintoci)" tana gama fadin haka ta katse kiran batare da ta jira amsawar Sister Ganiyat ba.
Nan danan ta mike ta fara hada wasu kayayyaki sannan ta saka labcoat ta fice daga office.
Emergency ward ta nufa, inda tana shiga ta nufi gadon da ta hango nurses hudu a tsaye suna kokarin ba ma mara lafiya kulawa, ganin tawowarta dasuka yi yasa suka matsa daga jikin gadon don bata space.
Kallon majinyancin datayi yasa fuskarta ta sauya cikin bacin rai, sannan ta fara magana cikin sassarfa"who admitted this bloody idiot into my hospital(waya kwantar da wannan dan iskar a cikin asibitina)?" .
Cikin sauri tare da hada baki sukace "sorry doctor,he was admitted by Doctor Kamal(kiyi hakuri likita, Doctor kamal ne ya kwantar dashi)".
Cikin tsananin bacin rai ta nuna wani cleaner da yatsa tare da fadin"go and call 3 securities for me, i don't want to see him here( je ka kiramin masu tsaro guda uku, bansan ganinshi a wurinan)"
Haka suka tsaya jiran securities wanda baka jin motsin kowa sai na patient din dake ta sauke numfashin wahala.
Kusan minti uku sai gasu sun shigo su uku, cikin tamkewar fuska doctor Zahra ta nuna musu patient din da hannu tare da fadin"please take this man out of my hospital quickly( don Allah ku fitar da mutumin nan daga asibitina da sauri)".
Jin wannan umurnin nata yasa gaba daya wadanda ke ward din daga nurses, securities, har patients jikkunansu suka yi sanyi, don duk wanda ya kalli mutuminnan yasan yana bukatar taimakon gaggawa.
Cikin tsananin fushi da hargagi ta kuma kallon securities din tare da fadin "you are wasting my time( kuna bata min lokaci)".
Wannan yasa suka yunkura don daukar shi, wanda yayi dai² da shigowar wani magidanci wanda bazai wuce shekara talatin da biyu ba, cikin tashin hankali yace" where are u taking my dad, or are going to change room for him?(ina zaku kaimin dad dina, ko zaku canza mai daki ne?)".wannan yasa securities suka dakata da daukar patient din daza suyi.
YOU ARE READING
Doctor zahra
General FictionDoctor Zahra littafine da yake dauke da darussa da dama, sannan ya kunci, jajircewa, zuminci, cin Amana, daukar fansa, bakin ciki, da rikici tsakanin 'yan uwa .