chapter 31,32,33,34,35.

0 0 0
                                    

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

(home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our reader)

  *_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉
*_Written by fateeyzah_*😍😍

*_Fateeyzah@wattpad_*

*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*

*Wannan page dinkune:*
*Aunty Aisha Ashir*
*Haseenert Muhammad*
   *Umulkhairi*
*'yar Asalee*
*Thanks for your love and support.*

*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________
      
          *_Page 31 to 35_*

        Ba karamin rikici akayi da ladiyo ba, don har sai da tayi kikirarin ko da zatayi yawo tsirara sai taga karshen Adda da Aliyu, jin wannan furucin datayi yasa mahaifiyarta cewa  Indai tayi ma Adda  wani abun  mara kyau bata yafe mata ba kuma ta cireta cikin 'ya'yanta.


Shi kuwa sarki jin abunda ladiyo ta fadi yasa  yace usman ya kawo takardarshi na secondary a saman masa ko recruitment ne, duk da dai takardun nasa basuyi kyau ba haka aka hada data Daddy aka kai.


Cikin hukuncin Allah suka tafi jarabawa, inda Daddy yayi a jaji, kawu Usman yayi a Zaria,  wanda duk suka fito da sakamako mai kyau, daga nan kuma suka tafi training.


bayan wata tara akayi passing out inda Daddy ya fito a second lieutenant, daga nan kuma aka hada shi acikin special force, inda suka tafi peace keeping a kasar libiya.


Kawu usman shima anyi passing out shi kuma akayi posting dinsa Benue.


Haka dai rayuwa ta ci gaba da tafiya yau da dadi gobe akasin haka.


Bayan sheka biyu abubuwa da yawa sun faru, ciki har da rasuwar Adda da samun girman da Daddy yayi bayan sun dawo daga peace keeping, da kuma rasuwar sarki wato mahaifin ladiyo, da auran dasu  kawu mahmud, kawu Muhammad, kawu Abubakar sukayi, wanda duk suka tare da matansu duk a gidan Galadima.




A wannan lokacinne aka yi posting din Daddy jahar yobe inda anan ya hadu da momyna.


Garin garzarma, garine dayake karkashin karamar hukuma damaturu dake jahar yobe, garin ya kunshi yaruka biyu wato fulani da shuwa, wanda yawancin fulani sunfi yawa.



Aishatu wato mummyna diyace ta sha hudu a cikin jerin 'ya'yan hakimin garin,  waddata ta kasance diya ta uku a wurin amaryarshi mai suna salamatu, ta kasance kyakyawace wanda daka ganta sak balarabiya, macece mai matsifar kishi ga saurin fushi amma kuma tana da saurin sauka, ta kasance 'ya mafi soyuwa a wurin Hakimi kasancewa an haifeta da matsalar ciwon zuciya, hakan yasa duk ahalin gidan suke bata kulawa sosai saboda gujewa tashin ciwontaa.



Ta hadu da mahaifina ne a lokacin da sukaje biki danmaturu, cikin kankanin lokaci soyayya ta kullu a tsakaninsu, har manya suka shigo ciki aka saka rana, cikin  wata shida akasha biki inda Daddy ya biya sadaki da sulallen gwal, nan aka dauki Amarya daga garzarma aka kawota kadarko, dakin Adda aka gyara aka saka Amarya.

Zaman nasu dai sai godiyar Allah, don gaba daya matan gidan sun hade mata kai, inna karime ne kawai me janta a jiki, duk da haka bata sa damuwa a cikin ranta ba saboda tasan yanayin ciwonta.

Watanta biyu a Gidan ta samu ciki, zokaga murna wurin daddy, lokacin haihuwa nayi ta haifo kyakyawan danta wanda yaci sunan Galadima wato Abdulrahman,  tsakanin yaya Abdul da Aunty Basma shekara daya da rabi, sannan tsakanin Aunty Basma da Aunty Naina shekara biyu da wata daya.

Kwasam bayan haihuwar Aunty Naina sai ga inna karime da ciki ba karamar murna baba Abdulaziz da Galadima suka yi ba, don har ya riga ya cire rai da samun haihuwa, duk wani matsoyinsu sai daya taya su murna badda Dada Ladiyo da Ahalinta, don gaba daya ta gama koya musu bakin halinta.

Wata tara na cika ta haifo kyakkyawar 'yarta wacce aka rada ma suna ni'eematullah, don acewar baba Abdulaziz babbar ni'ima ce wannan Allah ya basu, don a lokacin yana da shekara sittin da uku a duniya, inna karime kuma nada hamsin cif cif.

A wannan lokacinne kuma aka dawo da Daddy kaduna nan cikin jaji, nan ya tattaro mummy da su yaya Abdul suka dawo, wannan shine silar dawowar mu kaduna.

Makaranta mai kyau da tsada ya sasu both islamiya da boko don yace babban burinshi yaba 'ya'yanshi nagartattan ilimi.

Bayan shekaru hudu, a lokacin inkaga su mummy baza kace sunyi zaman kadarko ba, sun yi kyau ga wayewa, saboda Allah ya kuma daga Daddy har ya sayi fili ya fara Gini a Unguwar Rimi, adaidai wannan lokacinne mummy ta samu cikina, zo kaga murna wurinsu especially yaya Abdul don acewarsa mummy zata haifar masa dan uwa, haka suka ci gaba da tattalin cikina har ya kai wata tara, sannan na fito duniya, ba karamar murna sukayi ba, don yaya Abdul ma cewa yayi gwara da mummy bata haifo namiji ba, ranar suna aka rada min sunan Kakata wato fateema zahrah, amma gaba daya gidan tun daga kan Daddy har yaya Naina da Habibty suke kirana ba karamin soyayya suke nuna min ba.

Shakarata biyu, muka tare a katon mansion din Daddy ya gina mana, don gidane na kece raini saboda duk unguwar babu gida irin namu.

Bayan shakara sha hudu, abubuwa daya wa sun faru masu dadi da akasin haka, rasuwar galadima da samun karin girman da daddy yayi.

Alokacinne yaya Abdul ya tafi aikin soja, wanda Daddy yace sai yayi dole badon son ransa ba, da shirin bikin Aunty basma da akeyi wanda zata auri dan minister, sai Aunty Naina data tafi bautar kasa, a shekaran ni kuma na gama secondary school inda akemin processing din tafiya kasar India domin karatun medicine.

Biki akayi na kece raini don ba karamar dukiya Abba ya kasheba, don dai ya kankaro ma Aunty Basma girma awurin dangin miji don da farko uwar mijin taki yadda sai da tazo taga Aunty basman tukunna ta yadda da auren, nan dai aka kaita gidan mijinta dake maitama.

Bayan passing out din su yaya Abdul ne, shima akayi  bikinsa da  Aunty Hafsat wacce itama Babanta Aminin Daddy ne.

Bayan bikinne ni kuma na tattara na tafi india, nabar Nigeria cike da kewan iyayena da 'yan uwana.


Karar hon din da tajine ya dawo da ita daga duniyar tunanin data shiga, cikin sauri ta taka burki don da ta buga ma wani mai mota, saida ta samu relief sannan ta ci gaba da tuki.

Isarta Gidan Aunty Basma ne kuma ta samu wani Tashin hankali, don mijinta ya dauko mai magani akan zai turare gidan da magani, duk wani mai hannu a mutuwar 'ya'yansa zai yi composing(tona ma kai Asiri) da kansa.

Tofa yanxu xa a fara game din, kar ku yadda kuyi missing.

_Shin yazata kaya a gidan Aunty basma tsakanin mai magani da mutanen gidan?_

_Kar ku manta bamu gama jin tarihin Doctor Zahra ba_

_Duk ku biyoni cikin Littafin_ *DOCTOR* *ZAHRAH*

*More comment, more posting*

*Comment*
*Share*
*Follow*

*Fateeyzah* ✍✍
*08161734851* *whatsapp only*

Doctor zahraWhere stories live. Discover now