chapter 21,22,23,24,25

4 0 0
                                    

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

*_(home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_*

*Follow us:*
  *kundin hikima writers association @facebook*
*Hikima writers novels@facebook*

  *_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉

*_Written by fateeyzah_*😍😍

*Follows:*
*_Fateeyzah@facebook_*
*_Fateeyzah@wattpad_*

*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*

*_Inalillahi wa'ina ilaihir raji'un, Allah ya jikanki Aunty Ummy(hauwa'u), ya gafarta miki, ya amshi shahadarki, ya raya abinda kika bari, Ameen.😭😭_*

*_Hakika mutuwarki ta girgiza kowa, Allah ya bamu hakurin rashinki.😭😭_*

*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________
      
          *_Page_* *_21 to 25_*

            "Tunda na nufi falo, naga basanan na tabbatar da kowacce ta nufi side dinta, nan na zube a kan kujera, don abun ba karamin kada ni yayi ba, matan ka wanda kullum kake kokarin faranta musu, su suke son su kawar dakai a doron kasa, ina nan zaune narasa abunyi don kwata², I am out of speech, nan wata dabara tazo mun, natashi na nufi dakin hafsat, as usual tana nan gaban laptop, yanayin yanda naganta batare da fargaba ko wani abubu ba yasa na fara shakka akanta, don duk wanda ya aikata wannan abun, kuma ya tabbatar da asirinsa ya tonu bazai kasance haka ba, nan na bar side dinta, don har na shiga, na kuma fita bata sani ba hankalinta nakan laptop"ya karashe magana fuskarsa dauke da damuwa.

Wani siririn tsaki doctor Zahrah taja tare da fadin" wallahi ban taba ganin mata irin Aunty Hafsat ba, gaba daya rayuwarta ta ta'allarata akan aiki, sai kace in taje lahirar aikin za a  tambayeta".

Ya  lumshe idonshi cikin bacin rai sannan ya bude tare da cewa" ina shiga part din Aisha na tarad da ita tana ta kuka, gani na datayi yasa ta kuma fashewa da wani marayan kuka tare da fadin ( don girman Allah kayi hakuri na tuba bazan sakeba, sharrin shedan ne da kawaye, su suka ban shawarar kashe....) jin wannan statement din nata yasa naji wani karfi yazomin ban bari ta karasa magana na hambareta, na shiga dukanta, wallahi habibty dukan danayi ma Aisha, ko wani sojan aka mawa shi sai yaji jiki, don harsai data sume, Asuba nayi  naba masu sergeant ita nace su kaita jaji su samin ita a guardroom".

Nan danan hawaye ya wanke mata fuska tare da fadin" yaya mai ka ragi Aisha da shi da har zata maka haka?".

"Hmm  habibty kenan, Aisha really break my heart, sannan tasa na dena yadda da kowa, saboda abun duniya kisa a kashe mutum, mutumin ma mijinki, kinga kuwa ai tunda matarka ta maka, kowa ma zai iya maka, aranar nayi kukan rashin iyayenmu, kukan da rabo na da inyishi tun ina yaro, abun bakin ciki hafsat ko ta ta dubani don nasan duk tanajin abunda ya faru tsakanina da Aisha, amma sai turo min text messages tayi akan tana da meeting karfe bakwai ta wuce wurin aiki, wallahi Habibty indai haka halin ko wacce mace yake bazan kuma aureba, 'yar talakawar banji dadi ba, yar masu kudin itama gashinan, nidai haka tawa kaddarar ta ta zomin na rashin dace da matan kirki" ya karashe magana yana share kwallar data zubo masa a fuska.

Cikin kuka tace "yaya yanxu wani  mataki na ka dauka akanta"

"Zuwa can jaji nayi na hadata da fushin recruit shine take fadamin wai a Facebook group ta hadu da wata kawa, saboda tayi posting tana neman a bata shawara akan na hanata teaching amma nabar kishiyarta na aikin banki, shine waccen tabita private tabata shawarar ta nemi kudi a wurina ta fara business, daga nan suka sata a group dinsu na manyan mata, don tare dasuma taje dubai saro kaya, acan ne take fada musu Doctor yace bata da Eggs na haihuwa, shine fa suka bata shawarar ta ringa tatsa na kudi masu yawa, don ko na mutu tumunin takaba kawai za a bata, bayan na hanata wannan kudinne har na mata duka, shine taje ta basu labari, su kuma suka zugata akan ta kasheni kawai bayan tasa an karbar mata 50million sannan suka hadata da higher killers tare da hadama hafsat makirci ko da alamari ya baci, ace hafsat ne, mistake din dasukayi shine transfer kudi data masa na 1million a account dinshi da ya nemi deposit, kinji yanda suka tsara abun".

_( wallahi mata ku shiga taitayinku, kowacce sai ta tafi facebook tana tona sirrin aurenta,wanda yawanci in ba ayi dace ba anan ake haduwa da baragurbin mata, wanda wata baza ma tayi comment ba saidai tabiki private ta baki shawarar banza ke kuma da yake kin zama doluwa,wawiya sai ki dauka baki da wata masoyiya sai ita, in abin gaskiyace ta baki shawara cikin mutane mana inda kowa zai gani, saboda tasan Admins da sauran mutanen kirkin dake group din zasuyi blistering din shawararta, su nuna miki hakan ba dai² bane, wallahi ku kiyaye shawarwarin da ake baku)._

_(Sannan wallahi mata mu rage buri, wasu sun riga da sun yi ma aure mummunar fahimta, kowacce dai ita tayi aure ta zama mai kudi, ko ta fara business tana kama kudi ta zama babbar hajiya, wai da kudi zamu lahira ne, bama tunanin zamu mutu mubarsu a duniya,especially yanda yanxu zakiga mata masu karancin shekaru suke mutuwa, haihuwa daya, biyu, uku, ace mace ta rasu amma duk da haka mun kasa hankalta, mu dai burinmu kawai mu samu kudi, don Allah mu rage dogon buri don duk mu gama da farin kyalle za a mana sutura a birnemu, sai wanda ya ga dama zai maka addu'a, sai wanda yaga dama zai shafa kan danki ko 'yarki, Allah yasa mu dace)_

"Lallai yaya kaga jarabta, kuma shine dazaka je jajin ko ka kirani mu tafi tare, ni nama manta, me yasamu little ne?"

"Ita kuma na dawo daga jaji na sameta ta kone cinyoyi da ruwan zafi" ya bata amsa yana zuba coke a glass cup.

Cikin razana tace "inalillahi wa'ina illaihir raji'un, garin yaya ta kone"

Kafa cup din yayi a bakinsa sai da ya shanye tukunna ya sauke tare da fadin"wai sun dawo daga school suna jin yunwa, kuma sun tashi salaha tace karsu dameta ta gaji, shine fa taje ta kunna hot plate ta daura ruwan tea, bayan ya tafasa garin juyewa ta juye a cinyoyinta, nan na sameta tana ta ihu ita kadai a kitchen Aiman na ta faman jera mata sorry, ita kuwa salaha na kwance  tanajinsu, don ko dana shiga dakin samunta nayi tana chatting".

Lallai yaya gidanka akwai gyara, Allah dai shi kyauta gobe insha Allahu zan shiga da wuri in dubata".ta karashe magana tana mirza ido.

Mikewa yayi tare da fadin "Allah ya kaimu bari in wuce gida nabar Aiman wurinsu sergeant, nasan yanxu yayi bacci"

Cike da son karin bayani tace "wurinsu sergeant kuma, ina Aunty hafsat?"

"Na yi mata message da sakinta daya nace kuma karta dawo mun gida indai bazata ajiye aikin bank ba in samo mata a ministry of finance ko NDIC".

"Inalillahi wa'ina illaihir raji'un, gaskiya yaya baka kyautaba  da ka saketa da dai ka turata gida ne kace kabarta ta dan jima"ta fadi fuskarta cike da alhini

"Hakan shine ya kamaceta habibty, don na tabbata hafsat bazata taba canzawa ba, kedai kiyita tayani da addu'a".

"Insha Allahu yaya, Allah ya zaba maka mafi Alkhairi a rayuwarka gaba ki daya"

"Amin habibty ni na tafi, ki tabbatar dakin saka security gaba daya gidan kafin ki kwanta" yayi magana fuskarsa so serious.

Ta amsa da "insha Allahu yaya, goodnight".

Ya fice yana mai amsa mata da" goodnight habibty, sweet dreams".

Tadau tsawon lokaci a zaune a wurin daya batta hannunta dafe da habarta, kafin ta sauke doguwar ajiyar zuciya tare da mikewa ta shiga kitchen, few minutes ta fito hannunta dauke da cup din coffee dayan hannun kuma rike da dan karamin plastic plate mai dauke da cupcakes a kai, nan ta hau dinning ta fara shan coffee dinta hade da cake.

Karfe sha biyu dai² ta gama, ta dauki cup da plate din takai kitchen ta wankesu ta ajiyesu a mazauninsu.

Tana fitowa ta nufi main door na parlourn tare da saka wasu numbobi mai hade da securities, sannan ta nufi dakinta dake upstairs, brush kawai tayi tare da sa night gown tabi lafiyar gadonta. *GOOD NIGHT DOCTOR ZAHRAH.* /

Karar wayarta ya tasheta daga nannauyar baccin daya dauketa, wanda agogon dakin ya nuna karfe shidda na safe, cikin magagin bacci tayi picking din call din tare da sawa a speaker, muryar Aunty basma ce tana kuka tana fadin "inalillahi wa'ina illaihir raji'un,zahrah fawas shima ya mutu ya barni....... "

*Tofa🤔, ana wata ga wa ta.*

*Wai kamar yanda Aunty basma tayima  Doctor zahrah complain meye sanadiyar rasuwar da 'ya'yanta maza keyi a duk ranar da suka cika shekara biyu da haihuwa?*

*Ku biyoni daki² cikin littafin Doctor Zahrah don jin amsar tambayoyinku.*

*pls magana daya tak akan Aisha da Hafsat*

*Comment*
*Like*
*Share*
*Follow*

*_Fateeyzah_* ✍

Doctor zahraWhere stories live. Discover now