*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_**Follow us:*
*kundin hikima writers association @facebook*
*Hikima writers novels@facebook**_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩⚕️💉
*_Written by fateeyzah_*😍😍
*Follows:*
*_Fateeyzah@facebook_*
*_Fateeyzah@wattpad_**_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*
*_Innah sheriff, wannan page din kine dake da unborn baby, Allah ya saukeki lafiya._*
*_Bismillahir rahmanir rahim_*
____________________________________
*_Page 26 to 30_*Take ta wartsake daga ragowan baccin dayake idona, hakika so uku kenan Aunty basma tana sanar da ita irin wannan sakon mutuwar, amma yanda taji wannan ya banbanta dana baya, don jitayi kirjinta ya dsu zafi, zuciyarta kamar zata faso kirji ta fito, hakan yasa bata san sanda wayar ta sulale daga hannun taba, ta dau tsawon lokaci zaune dafe da kirjinta, tana cikin tunani da alhini, dakyar ta iya bude bakinta da yayi mata nauyi ta ambaci kalmar inalillahi wa'ina illaihir raji'un, haka tayi ta maimaitatawa tukunna ta samu natsuwa a cikin zuciyarta.
Kiran wayarta da aka kuma yine yasa ta dawo daga guntin tunanin da ta shiga, picking din call din tayi tare da fadin" good morning yaya,(pause), eh ta kirani,(pause), yanxu xan shirya sai in biyo ta asibiti kafin in wuce chan din,( pause), ok sai na zo"
Tashi tayi ta nufi toilet tayi wanka hade da dauro alwala, sannan tayi sallar asubahi, cikin sauri ta shirya cikin atamfarta chiganvy, wacce akama dinkin riga da skirt, sannan ta dauko katan veil ta rufe jikinta, hand bag ta dauka wadda kalarta ta dace da kayan jikinta, daga nan ta nufi shoe rag ta dauki wani plat shoe ta saka, daukar key din motarta tayi, sannan ta fice daga dakin.
Direct Asibitinta ta nufa, wanda tana shiga ta wuce dakin da aka kwantar da little, anan ta sami yaya Abdul, bayan gaisuwa, ta duba jikin little, sannan ta fice ta dauki hanyar Abuja.
Yau ma as usual, mutanen nata na Binta a baya, amma ko ta kansu batayiba, don abunda ke damunta yasa bata da lokacinsu.
*TUSHEN LABARI*
Garin Kagarko, garine dake karkashin jahar kaduna, yawancin mutanen garin fulani ne, wanda suka kafa garin shekaru da yawa baya.
Alhaji Mamuda Galadima, wanda shine Galadiman kagarko a wannan lokacin ,matarshi daya inna Ramatu, da yaransu biyu Abdulrahman da Abdulaziz.
Abdulrahman da Abdulaziz sun taso cikin kulawa hade da soyayya da suke samu daga wurin iyayensa da mutanen gari saboda yarane masu farin jini, ga ladabi da biyayya, ba karamar soyayya bace da shakuwa tsakaninsu duk da suna da tazaran haihuwa, don akalla Abdulrahman yaba ma Abdulaziz shekara sha hudu tsakaninsu, sunyi karatun addini dai² gwargwado.
A lokacin da Abdulrahman ya cika shekara ashirin da daya, aka masa auren fari, wanda aka hadashi da 'yar limamin garin mai suna fatima, yarinyace mai ilimi, kunya da kawaici, ga uwa uba hakuri, bayan an daura aure suka tare a gidansu da Galadima ya gina masa.
Suna matukar son junansu, wanda cikinsu babu mai son bata ma dan uwansa, watansu uku da aure Allah ya karbi ran galadima, ba karamar kaduwa sukayiba, don mutuwar ta shigesu sosai.
Bayan anyi sadakar uku aka nada Abdulrahman Galadima, a haka ya ci gaba da kula da inna da 'yan uwansa Abdulaziz.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya hat suka shekara biyar da aure amma fatima ko batan wata bata taba yiba, hakan ya tada ma inna hankali tace sai Abdulrahman ya kara aure don tana bukatar ganin jikokinta kafin kasa ta rufe mata ido, an kai ruwa rana kafin Abdulrahman ya amince da batunta na kara aure, anan dai inna ta shiga ta fita ta nemo masa auren ladiyo diyar sarkin garin.
Ladiyo macece fitinanniya ta karshe, bata da hakuri ko kadan, ga kishi, ga hassada, ga kyashi, wannan yasa cikin karamin lokaci ta fitini mutanen gidan, ciki kuwa har da inna, Abdulaziz ne kawai bata ma wa don shi bai daukar nosense hakan yasa basa shan inuwa daya, fatima ba karamin hakuri take yi da ladiyo ba, don ma Galadima yana tsawatar ma ladiyo.
Watan ladiyo uku a gidan Galadima ta samu ciki, zo kuga murna wurin ahalin nan, ciki kuwa har da fateema, amma ladiyo tace murnar munafunci takeyi, randa ko ta haife cikin inna kamar ta zuba ruwa a kasa tasha, don har kyautar bajimin sa tabama yaron da aka haifa wanda yaci sunan marigayi Galadima wato mahmud, a takaice acikin shekara biyar da aure sai da ladiyo tayi haihuwa uku duk kuma maza,Muhammad, Abubakar, sannan cikon na ukun mahmud, nan fa ladiyo ta kara girman kai don ita a ganinta ta cinye gida, don kullun sai ta sakar ma fateema habaici duk ko da kusan ita take kula da yaron.
Kwatsam sai ga fateema ta ciki, ba karamar murna ahalin gidannan sukayi ba musammam Galadima da Abdulaziz, haka aka hadu harda innah aka ci gaba da rainon cikin, wanda ladiyo zuciyarta ke kunshe ta bacin rai don ganin yanda kowa yake lallaba fatima tamkar kwai.
Cikin fateema wata shidda, itama ladiyo ta samu wani cikin, nan feleke ya karu,don kullun saita yada ma fateema magana akan tadai fita ko yanxu Galadima ya rasu ita keda gida.
Cikin fateema nacika wata tara ta haifo sankadeden danta wato Daddyna, zo kaga murna gurin masoyan fateema, ranar suna na zagayowa aka rada ma yaro Aliyu, nan ko inna tabama mutane mamaki don kyautar danmariki biyu tabama Aliyu don acewarta wannan shine asalin maigidanta, hakan ko ba karamin bakanta ran ladiyo yayi ba inda wanda hakan ya kara haddasa wutar tsanar Aliyu a zuciyarta.
Watan Aliyu biyar da haihuwa, ladiyo ta haifo danta mai kama da ita,wanda aka saka ma suna usman,daga kan usman aka rufe haihuwa a gidan Galadima.
Rayuwar Gidan Galadima rayuwace mai cike da jin dadi sai dai ladiyo datake kawo musu cikas, don gaba daya ta gama koya ma 'ya'yanta halinta, saboda tsakaninsu ma suna ma junansu hassada, hakan yasa kullun dakinta cikin fada ake.
Aliyu yaro ne natsatse, domin ko ya samu tarbiya mai kyau wurin Adda(fateema) da kawu( Abdulaziz), yayi makarantar primary dinsa anan kagarko tare da 'yan uwansa, sannan suka yisecondary a Birnin gwari boys secondary schoo, bayan nan duk sauran basu ci gaba ba ,sai shi da ya tafi jami'ar Ahmadu bello dake Zariya inda ya karanci public Administration.
A lokacin da Daddyna(Aliyu) yake level one ne kawu Abdulaziz yayi aure, inda ya tare da matarsa (karime) anan Gidan Galadima, nan suka hada kai da Adda don in kagansu zaka dauka yaya da kanwane, ba karamar shakuwa bace a tsakaninsu hakan yasa Ladiyo(Dada) ta kuma tsanar Adda don gani take duk munafuncinta ne yasa duk wanda ya shigo Gidan sai dai yace.
Kwatsam aka wayi gari innah ta amsa kiran ubangiji, hakika ba karamin girgiza sukayi ba, don inna wata babbar bangoce ta wannan Ahali.
Lokaci ya ja, inda har Daddy ya gama degree dinsa yaje service ya dawo, wanda har wannan lokacin matar kawu Abdulaziz bata taba ko bari ba, hakan yaja mata gori wurin Dada, kusan kullun sai tasata kuka,saukin tama Daddyna dakinta yake wanda in ta kallesa take samun farin ciki don ko bata haihu ba tasan tana da Aliyu.
Wata babbar offer aka bama maigari na yakawo mutum daya daga garinsa mai takaddar degree don a sama masa aikin soja, nan suka yanke hukuncin kai Daddyna.
Zo kaga murna wurin Daddy, Galadima, kawu Abdulaziz, Adda, baba karime, sabanin da ladiyo har yaji tayi wai Galadima bayason yaranta yafi son Aliyu tunda har ya nemo masa Aikin soja, bai nemon ma yarantaba, rashin sani bata son babanta ya bama Aliyu offer ba.
*More comment,more typing*
*Comment*
*Like*
*Share*
*Follow**Fateeyzah*✍
YOU ARE READING
Doctor zahra
General FictionDoctor Zahra littafine da yake dauke da darussa da dama, sannan ya kunci, jajircewa, zuminci, cin Amana, daukar fansa, bakin ciki, da rikici tsakanin 'yan uwa .