chapter 36,27,38,39,40

8 0 0
                                    

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

(home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)

  *_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉

*_Written by fateeyzah_*😍😍
*_Fateeyzah@wattpad_*

*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*


*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________
      
          *_Page 36 to 40_*

         Abin mamaki harda Aunty Basma ta yarda da batun mijinta, nan fa malam  yasa asamo rushin wuta, batare da bata lokaci ba sai ga rushi an kawo, nan dai ya gama tsibace tsibacenshi, sannan yace a kullo gate din gidan.

Saukar maganarta naji akaina kamar saukar aradu, daga kai nayi domin inga mai magana, wata hamshakiyar mace ce a tsaye 'yar duma², kallo daya zaka mata kasan naira ta zauna, cikin gadara da isa take magana.

"Wai Najib mai yasa baku da dangana ne, nace ku Mika lamuranku ga Allah, ku yadda shiyake karban ran yaran nan, saboda ban isa da kaiba shine zaka je ka kawo wannan dirty witch din da sunan malam, idan kura na maganin zawo tayi ma kanta mana, don haka indai ni na tsugunna na haifeka ina so ka tattara wannan shirmen kayi dashi waje tun kafin in saba maka" ta karashe magana hade da juyawa tabar wurin ba tare da ta kalli kowa ba.

Hajiya Sailuba Kasim kenan Mahaifiyar Najib mijin Aunty Basma, cikakkiyar 'yar siyasace tun bayan rasuwar mijinta daya rike mikamin senator da minister kafin Allah ya mai rasuwa, danta daya Najib, shi yasa ba karamin sonsa takeyi ba, macece mai fuska biyu, wanda a zahiri take nuna ma mutane ita ta kwarai ce, amma a ba'ini kuma, Allah kadai yasan iyakar abunda take aikatawa, sannan macece mara yadda, don ita kanta bata yadda da kantaba, ballantana ta yadda da wani, a yanxu haka tana rike da mukamin mai bawa shugaban kasa shawara akan harka mata da kananan yara.

Jin haka yasa malam ya tattara kayansa ya fita, nan ma Yaya Najib ya bi bayansa, ganin haka yasa Aunty basma ta fashe da wani irin marayan kuka, gaba daya ta fita hayyacinta sai sumbatu takeyi wanda baka iya jin mai take cewa, ganin haka yasa Doctor Zahra wadda  tun zuwanta take tsaye a wurin karasawa wurinta tare da tada ita takaita daki ta zaunar bakin gado.

Anan na samu damar zagayawa gidan, Gidane hadadde wanda aka ginashi kamar ba a san zafin nema ba, koko ince kamar masu shi ba sa tunanin mutuwa, tsayawa fasalta muku gidan bata bakine, don ko a Abuja mallakar Gidan nan sai wanda yaci ya tada kai.

Dakin Aunty Basma na ko ma, nan na tarar dasu su uku, Aunty basma, zahrah da wata katuwar mace, wanda kallo daya zaka mata ka gano kammaninta dasu Zahrah.

Fuskarta dauke da hawaye tace" wani irin hakurine banyi ba,haba Naina dole fa inyi kuka yara uku suna mutuwa kuma duk ranar dasuka cika shekara biyu a duniya, kinsan wannan ai dakwai alamar tambaya aciki, Wallahi akan rasuwar fawas na kuma tabbatar akwai abu akasa, lafiya lau fa muka kwanta dashi, wurin karfe uku kawai sai naji ya tashi yana kuka yana ta fizge²,wallahi cikin kannanin lokaci sai ga jini na fitowa ta bakinsa, nan danan kanshi ya karye, kuma adai dai lokacin naji motsi a bayan window na, nayi kokarin tashi in duba, amm ganin yanayin da fawas ke ciki na kasa tashi in barshi" ta karashe magana cikin shashsheka"

Idonta dauke da kwalla tace"Basma duk da haka hakuri zakiyi, ki tattara komai ki bar ma Allah ikonsa, ki karbi kaddara a yanda take, mun rasa iyayenmu ma gaba daya,  amma mun hakura mun barma Allah, sannan kafin fawas kin rasa biyu, don haka don Allah kiyi hakuri muyita addu'a, Allah sa masu  ceton mune".

"Wallahi abunda yasa nafi damuwar da mutuwar Fawas, saboda irin Mutuwar mummy yayi da yanda take fizge², har yanda jini ya gangaro ta bakinta wallahi duk daya".

Zahrah ne taja dogon numfashi tare da fadin" gaskiyane Aunty Basma Mutuwar su Fawas akwai alamar tambaya especially fawas dinki na biyu, don dana dubashi babu alamar jini gareshi, shi yasa lokacin har na tambayeki ko yayi rashin lafiyane kafin birthday din kikace a'ah, ko dazu kafin a rufe fawas nayi kokarin ganin gawarshi amma hajiya tace an ruga an masa wanka bazan iya ganin saba".

Cikin firgice tace"kin gani ko Naina ai na fada miki akwai rina acikin kaba"

Naina ce ta kalli zahrah hade da watsa mata harara sannan tace" wai meye hakane habibty , maimakon ki kwantar mata da hankali, amma ke kike tada mata dashi, wallahi kar in kuma jin wannan maganar ta fito daga bakinki, don baki da hujjar fadin haka".

A takaice dai, nan aka bar magananr, inda aka ci gaba da karban gaisuwa amma ba karamin sa ido takeyi akan Hajiya sailuba da Yaya Najib ba, don  tana ji a jikinta akwai wani babbab al'amari a tsakanin su biyun don yanda suke behaving kwata² kamar mutuwar bata damesu ba, don sigma Najib din duk dauko mai maganin da yayi a ganinta duk burgane.

A rana ta biyu Yaya Abdul yazo gaisuwa ya tafi, don shima kwata² jininsa bai hadu da Najeeb ba ballantana uwarsa Hajiya Sailuba, wanda suma ta bangaren su kusan haka ne, don kallon mage da bera suke ma juna.

Ranar da akayi uku da rasuwar, a ranar zahrah take shirin dawowa kaduna don tana da surgery din da zatayi ranar monday.


Tana cikin hada kaya, wayarta tadau ringing, ganin mai kiran yasata ta saki wani lallausan murmushi tare da daukar wayar sannan tace " Hello besty kin manta dani"

Daga can aka amsa" da ba haka bane besty, I am busy ne this days, amma ba lokacin bayani, ki duba IG ko facebook kiga videon dayake yawo" kit ta kashe waya ba tare da ta jira amsawartaba.

Cikin rawar jiki ta kunna data tare da shiga IG don tasan nan zai fi mata saurin dubawa, cikin mintuna kadan sai ga video a inbox dinta mzz huwailat( besty) ta turo mata, cikin sauri ta shiga videon, fuskarta ce ta bayyana aciki tana ta zuba masifa, nan da nan  ranar ta dawo mata, ba kowacce rana bane illa ranar data kori doctor Shareef a Asibitinta, amma abun duba shine, gaba daya an yanke video, sai akabar inda take ma nurses masifa kan Doctor Shareef, da inda ta umurci securities su fita dashi,  fuskarta dauke da  mamaki  don tama kasa furta komai.

Cikin jarumta ta fara duba news feed inda nan ta tsince videon hade da dubban comment wanda duka kusan na zagine tare da aibantawa, ganin haka yasa ta saki wayar ba tare da ta sani ba.




Is just the start of the battle, follow don't miss.




*Comment*
*Share*
*Follow*



*Fateeyzah*✍

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 02, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Doctor zahraWhere stories live. Discover now