chapter 16,17,18,19,20.

5 0 0
                                    

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_*

*Follow us:*
*kundin hikima writers association@facebook*
*Hikima writers novels@facebook*

  *_DOCTOR ZAHRAH_*🏥👩‍⚕️💉

*_Written by fateeyzah_*😍😍

*Follows:*
*_Fateeyzah@facebook_*
*_Fateeyzah@wattpad_*

*_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad❤_*

*_This is your page sharifat niamey, Allah bada sa'ar jarabawa._*

*_Bismillahir rahmanir rahim_*

____________________________________
      
          *_Page 16 to 20_*

   Cikin tashin hankali tace" what!!, yaya da gaske kakeyi, koko kunne nane baiji da kyau ba"

"Hmm hakan ne habibty nima kaina na dade ina mamakin hakan, da farko dai kinsan basma da naina suka bani shawarar kara aure Saboda matsalolin da nake ta fuskanta nida hafsat, na yanda tafi bama aikinta muhimmanci akan mu familynta".

Cikin bacin rai ta kada kai tare da fadin" hakane yaya nikuma nace maka ka auri 'yar talakawa ne saboda sunfi iya kula da miji".

" habibty tunda kafin na auri Aisha sai da mukayi yarjejeniya akan baza tayi wani aiki ba,saboda inason ta ringa kula dasu little hakan yasa na yanka mata sadaki naira dubu hamsin duk wata, kuma ta amince, Amma kuma tunda akayi auren sai itama tabi layin hafsat suka daura ma mai aiki alhakin kula dasu little".

"Amma yaya ni banga laifinta ba, tunda uwar da ta haifesu ma ta kasa basu kula, kana tunanin wacce batason zafinsu ba zata kula dasu ne, don Allah yaya ka fadamin yaya abin ya faru" tayi magana cikin zakuwa.

"Kinsan 2months back Aisha ta tada mun da hankali sai na bata jari zata je dubai ta saro kaya zata fara business, hakan yasa na bata 2millions taje ta saro kayan, to after 3weeks sai ta kuma tambayata wata 2millions din wai tanaso ta saro kitchen equipment kuma wanda suka siya wadancan kayan basu riga sun hada mata kudin ba, nan nikuma nace bazan bada ba, nan fa tayita tada mun da hankali acikin gida ranar har ta kureni nayi mata duka, kawai jiya around 12 kuma sai ga 'yan fashi a gida, nan hankalina ya tashi don ba karamin bindigogi bane a hannunsu, da farko su kusan bakwai suka shigo nan suka kulleni sannan suka tankado keyar Aisha da hafsat zuwa falona, yin haka da 5minutes sai ga ogansu ya shigo da mutum biyu, nidai dana ganshi sai naga kamar na san fuskar amma na manta, sai da naji ya ambato sunan lieutenant A.A .Galadima, sannan na kuma dago kai".

Cikin kidima tace" yaya badai kunsan juna ba?"

"Tabbas habibty, don shekara daya data wuce na taba bugeshi da mota a Ahmadu bello way, wanda ni nakaishi Asibitin mu na sojoji aka yimasa medication".

"Chab di jab, to yaya akayi kasan Aisha ce ta aiko a kasheka"tayi magana fuskarta dauke da mamaki.

Sai daya gyara zama sannan yace" bayan yasa yaransa sun kwanceni sai ya nemi kebewa dani, nan ya fadamin daya daga cikin matana ta bashi contract din kasheni bayan sun karfi miliyan hamsin a wurina, dana tambayeshi wacce a ciki, sai yace a waya suka hada contract din amma tace masa sunanta hafsat amma data tashi yi masa transfer na kudi sai akayi da account din Aisha, nan kwakwalwata ta tunkushe, amma duk tunanina su biyu suka hada baki don a kasheni, nan dai ya nemi gafarata tare da kwashe yaransa sukayi gaba bayan sun kwance  su sergeant dasuke gadi".

"Amma yaya kana soja kabar kasunguman 'yanfashi suka tafi batare da ka dau wani mataki ba"

"Habibty lokacin nan batasu nake ba, gaba daya hankalina ya dugunzuma ya tashi, tunani na mai na ragesu dashi, especially hafsat me zatayi da dukiya, ga gadon mahaifinta, ga salary dinta a matsayinta na ma'aikaciyar C.B.N (kaduna branch), ita kuma Aisha a ganina duk kudin danake bata basu ishe taba".

Pls manage ban da ishasshen time.

Ko yaya lieutenant A. A. Galadima zai warware wannan sarkakiya tsakanin matansa sai mun hadu next page.

Kuyi hakuri da error, banyi Editing ba.

*Comment*
*Like*
*Share*
*Follow*

*Fateeyzah* ✍

Doctor zahraDonde viven las historias. Descúbrelo ahora