*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_**Follow us@facebook, kundin hikima writers association*
*_DOCTOR ZAHRAH🏥👩⚕️💉_*
*_Written by fateeyzah_*😍😍
*follow me on wattpad@Fateeyzah**_Dedicated to Hauwa .A. Abba and Sophie .H. Muhammad_* ❤
_Wannan page dinkune_ *Fateeyzah novel fans* , _da fatan anyi sallah lafiya, Allah ya karfi ibadunmu._
*_Bismillahir rahmanir rahim_*
*_Page 10 to 15_*
Kallo daya zaka masa ka gano tsantsar kaman dasuke yi da doctor, kakkaura ne, giant sanye yake da wandonsa na kakin soja,sai wata army green silk shirt, wadda ta matse masa kirji duk ta fito da da cikakkiyar kirar shi ta da namiji.
Daukar ta yayi kamar jaririya ya shimfideta a saman gado, sannan ya fara tattara kwalaben dake wajan, haka yabi sako² na dakin duk kwalbar da ya gani yana hadasu wuri daya, hatta kwayar maganin da bai yadda da ingancinta ba sai da ya daukota, sannan yazo ya ringa iban su yana fitar dasu.
Bata farkaba sai misalin karfe shidda na yamma, mika tayi hade da karanto addu'ar tashi daga bacci, wanda a dai² lokacin wayarta dake yashe akan gado ta fara ringing, cikin mutuwar jiki ta dauko wayar tare da receiving din call din sannan ta danna speaker, daga cikin wayar wata zakakkiyar murya tace" hello habibty"
Cikin sanyin murya ta amsa da" na'am Aunty Basma, ina wuni"
"Lafiya habibty, kar kicemin wannan birthday ma bazaki yi attending ba,don muryarki ta nuna
min kamar ma daga bacci kika tashi" Aunty basma tayi magana cikin sanyin murya."Don Allah Aunty kiyi hakuri, tunda na dawo wurin karfe biyu daga Asibiti nake bacci sai yanxu ma na farka"
"Cikin kakkausar murya Aunty basma tace"wai har yanxu Habibty baza kiyi ma kanki fada ba, ki rungumi maraicinki, kinje kinyi shaye shayanki ba dole kiyi ta bacci ba"
"Aunty nakasa controlling din kaina ne, abubuwan dasuka faru a baya, su suka dawo mun ayau, Aunty Doctor Shareef fa aka kawo Asibitina yana fama da heart problem"
Muryarta dauke da mamaki da bacin rai tace" Doctor Shareef kuma a Asibitinki, Kai zahrah anya ko shi kika gani, mutumin da ya koma kasar Egypt mai zai kawo shi Nigerian, yana ciwo bama yazo ziyara ba"
"Wallahi Aunty shine, saboda da danshi ma suka zo, kuma dan ya tabbatar mun dashine".
"To wani hukuncin kika yanke masa?, karki cemin kin masa treatment, don in haka ta faru sai nayi takakkiya nazo na shemeki wallahi"tayi magana cikin zakuwa da bacin rai.
"Haba Aunty, aini nafiku kullatan shi, ni da komai ya faru a gabana, ai korar kare na masa shi da dansa, kuma wallahi inkika gansa yana jin jiki" ta fadi so proud.
Cikin murya mai cike da jin dadi tace"ai kin min dai² habibty ,Allah ya biyaki".
Ta amsa da" Amin, wai ina Aunty Naina ne, ko bata karaso bane?".
Tana can garden tana gyara decorations, wallahi habibty ni ji nake kamar kar ayi birthday dinnan, sai inga kamar abunda ya faru a baya zai faru da fawas shima" tayi magana cikin karayar zuciya.
"Haba Aunty ki kwantar da hankalinki, duk abunda kikaga ya faru yana cikin kaddarar mutum, kinga tunda mummy ta nace sai anyi, ki saki ranki kawai, kuma kafin ki fita ki tofe shi da ayatul kursiyyu, da qul'a'uzai".
YOU ARE READING
Doctor zahra
General FictionDoctor Zahra littafine da yake dauke da darussa da dama, sannan ya kunci, jajircewa, zuminci, cin Amana, daukar fansa, bakin ciki, da rikici tsakanin 'yan uwa .