*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_**Follow us kundun hikima* *writers* *association@facebook*
*_DOCTOR ZAHRAH🏥👩⚕️💉_*
*_Written by fateeyzah_* 😍😍
*Follow me on wattpad@Fateeyzah**_Dedicated to Hauwa . A . Abba and Sophie H Muhammad❤_*
_Assalamu alaikum fans, da fatan an gama azumi lafiya, Allah ya karbi ibadunmu, na dawo da sabon novel dina mai suna *DOCTOR* *ZAHRAH* , ina rokon Allah yasa na fara a sa'a, sannan ina godiya gareku da irin kaunar da kuka nuna ma novel dina *GIDAN* *NAGOGGO* , naji dadin comment dinku ,Allah ya saka da Alkhairi yabar kauna._
_Wannan labarin nawa kirkirarren labari ne, ban yadda a juya min shi ta wata hanyar ko ayi editing ba sai da izinina._
_Wannan page din_ _nakune_ *HIKIMA WRITERS,* _da fatan anyi_ _sallah lafiya,Allah ya kara basira da zakin hanna._
*Doctor Zahra kirkirarren labarine dayake magana akan zumunci, daukar fansa, cin amana, rikici tsakanin 'yan uwa, karku bari a baku labari, just follow me from first page to last page.*
*_Bismillahir rahmanir rahim_*
*_01 to 05_*
Da gudu motar kirar Mercedes Benz ta shigo harabar Asibitin, wanda hakan yaja hankulan mutanen dake wurin, direct parking space motar ta nufa wanda ke dauke da allon da aka rubuta *SENIOR* *CONSULTANT* da manyan baki tayi parking a wurin, saida aka dauki kamar minti biyar tukunnan tabude kofar motar, kyakkyawa ce fara sol da ita, wanda kallo daya zaka mata kasan Allah yayi halitta a wurin ,zan iya cewa komai nata is perfect baiyi yawa ba sannan bai yi kadan ba, daka ganta kasan tahada dangi da shuwa arabs, *DOCTOR ZAHRA* Aliyu AbdulRahman kenan, wadda akema lakani da young doctor, shekarunta ashirin da hudu a duniya, itace mamallakiyar Asibitin A.A. Rahman memorial hospital, asibitin dayayi fice a fadin kasarnan, wanda sukayi specializing akan abunda ya shafi zuciya.
sanye take da wata baby pink gown wanda tadaura labcoat a sama, sannan tayi rolling da wani pink squeeze veil, wanda Hannunta na dama take dauke da wata baby pink cingum bag, hannun hagunta kuma dauke da jakar laptop, kafarta sanye take da wani pink toms me dauke da touch din white, cikin hanzari ta rufe motar tare da jefa key din cikin bag dinta sannan ta nufi upstairs building din wurin tana takunta cikin kasaita, upstairs ne hawa uku wanda aka masa painting green and white, duk inda ta gifta mutane ne ke kawo gaisuwa wanda ita kuma take amsawa cikin kulawa hade da murmushi kwance a fuskarta.
Daidai zata shiga lifter, wani tsoho dake sanye da wani army green din yadi wanda dakaga yanayin dinkin kasan uniform ne na security ya tawo cikin hanzari tare da fadin "barka da zuwa diyar albarka, an tashi lafiya".
Nan danan fara'ar fuskarta ta karu, cikin sweet voice dinta tace "lafiya lau babana ya iyali".
Fuskarshi dauke da mirmushi yace "suna lafiya diyar albarka, yau dai kin kusa latti, don tun dazu nake ta jiranki" ya karashe magana cikin kulawa.
Sai da tayi mirmushi sannan tace "wallahi kuwa babana, jiya ban kwanta da wuri bane saboda dan wani research danakeyi, dafatan dai ba matsala" ta karashe magana tare da jefomai tambaya.
"Ba wata matsala diyata, dama maganar Doctor sulaim ne don jiya da daddare sunzo wurina shida mahaifinshi akan inbaki hakuri ki dawo dashi bakin aiki, bazai sake aikata abunda ya aikata ba" yayi magana fuskarshi dauke da damuwa.
Nan danan ta hade fuska kamar ba ita yanxu ta gama murmushiba tace" babana ka fita daga wannan batun don gaskiya inajin kunyarka, girman laifin da Doctor Sulaim ya aikata yasa bazan iya dawo dashi bakin aikiba, asibitina na gina shine don taimako, wannan dalilin yasa bana so ana nuna banbanci tsakanin masu kudi da talakawa, amma duk da haka Doctor Sulaim yasan haka ya karya dokata, baba bari kaji abinda ya faru, wata yarinya aka kawo bata da lafiya,sai ya zamana tana bukatar jini,hakan yasa aka diba jinin babanta dayayi dai² danata za a kara mata,kafin a karan ne Doctor Sulaim ya dauki jinin ya kara ma 'yar chairman na local government, saboda mahaifiyarta ta kawota kuma aka rasa jinin daza a samata, shinefa aka kira babanta dake London aka sanar dashi, shikuma ya turama Doctor Sulaim 200k yace yanemi jini ko a inane a sama yarinyar, wannan dalilin ne yasa yaje ya dauki jikin daza a sama waccan ya gwada yaga yayi dai² da jinin 'yar chairman yasa mata, wanda da abun yazo da karar kwana yarinyar ta rasa ranta, baba wannan ba zalinci bane, salary danake basa ne bai isheshiba harsai ya hada da cin hanci wanda yayi sanadiyar rai" ta karshe magana cikin bacin rai.
Cikin sanyin jiki yace" hakane diyar albarka, wallahi ni bansan abunda ya faruba kenan, daban shiga wannan magana ba, amma don Allah kiyi hakuri"
Sai da ta goge zufar data feso mata a fuska tace" babana ya wuce, amma don Allah karka kuma zo mun da magana irin wannan don ba karamin miki take tadomin ba" ta karashe magana tana kokarin danna mabudin lifter.
Cikin rawar baki ya amsa da" insha Allahu hakan bazai kara faruwa ba"
Nan ta shige tabarshi a tsaye.
Direct office ta nufa wanda daga samanshi aka rubuta *SENIOR* *CONSULTANT* *OFFICE*, danna wata na'ura tayi mai kama da calculator a jikin wata kofa, sannan ta saka wasu numbers sai ga kofar ta bude, cikin takunta na kasaita ta shiga office din,sannan kofar ta rufe batare da ta tabata ba, babban office ne wanda aka shirayashi da ingatattun furnitures, tsaya wa badin haduwarsa bata lokacinne, direct side din dake dauke da tables da chair ta nufa,
YOU ARE READING
Doctor zahra
General FictionDoctor Zahra littafine da yake dauke da darussa da dama, sannan ya kunci, jajircewa, zuminci, cin Amana, daukar fansa, bakin ciki, da rikici tsakanin 'yan uwa .