BABI NA DAYA

1.5K 75 9
                                    

*EXQUISITE WRITERS ASSO*

*_ZAI JAGORANCI SHIRIN LABARIN ME TAKE A KASA WANDA ZA'ANA GABATAR DASHI A GRPS GUDA UKU. MASARAUTAN MATA 1 da 2. SBL TSK zai na zuwa muku a duk mako sau daya Insha Allah shirin zai na kawo muku wasu abubuwan da suka shafi Rayuwar mu ta yau da kullum labarin ba kamar irin wanda muke yi bane yau da kullum zai zo da nisan zangon_*

GIDAN AURE NA
🎪🎪

Mai_Dambu

Labarin Sameerah.
Babi na ɗaya

"Amir sai naci kutumar kaniyarka, dan banza shegen Yaro mara tarbiyya an gurbata mana halinka da mugun halin yan boko. Shege da ramtalellen kanka a gurin" inji matar kanin Baban Amir,

Had'iye kukan da yazo min nayi, tare da cigaba da aikin abincin da nake yi, wanda na zama kamar farilla ce yinta, domin dole zan tafi aiki idan na gama.
 "Aunty Meerah! Manja yana konewa" da sauri na zuba kayan miyar, ina fadin.
"Sorry Yanasu."

"Ina zata damu, tunda ba Ubanta bane yake niman kudin D'ana ne yake nima. Dole ta mishi asara mana, ban san a ina Faruq ya dauko wannan abin ba." Inji Babar mijina,  ban d'ago kai na kalle ta ba, asalima cigaba nayi da aikina.  Ihun Amir naji, kamar zuciyata zata kwace haka na d'ago kai ina kallon Fatih tana rike da fatar hannun shi kamar zata cire zunzurutun cizo.

  Dauke kai nayi ina cigaba da aikina, shi kuwa sai tsalla ihu yake, ban d'ago ba amma kuma har cikin ruhina nake jin kukan shi da shidewar shi.

  "Shika mishi hannu, ai ko yanzun ya san akwai banbanci tsakanin Ƴaƴan da suka ci tuwo miyar kuka da wanda aka basu madara," inji Uwar Yarinyar, murmushi nayi sannan na cigaba da aikina, da gudu yaron yazo tare da fadawa jikina.
 Yana wani irin kuka da iya uwa ce take iya fahimtar daga inda kukan yake fitowa, daga kasar zuciyar shi yake kukan.

 Muryan Gwaggo ya sani yakince shi a jikina domin sunce wai na cika jarabar son Yarana, Amir shine d'ana na uku, kuma karami dake bani haihuwa a kai akai, ina tazara. Babban Y'ata Nuratu shekarar ta bakwai, sai Wacce take Binta Nimrah shekara hudu sai Amir me shekara biyu cif..
Watanni mu biyar kenan da Uwar mijina ta sashi dawo damu gidan Gandun ko nace Family House, otoke, gidan gado. Matan da suke cikin gidan sun kai ashirin da daya, matan wa da kani kawai, ban da y'ay'an su. Ban san yadda akayi Baban Nuratu ya dawo damu gidan ba, amma bani manta wani zuwan shi  hutun karshen mako ya saka ni a gaba mu dawo gidan.

. Suna na Sameerah Abdullahi Anchau taka lafiya na jahar Kaduna, mahaifina tsohon likita ne, Mahaifiyata kuwa musulunta tayi a hannun Baban mu, sannan ta aure shi. Nayi karatun Alkur'ani da na boko, har na hada matsayin MBs a nursing,  na maida hankali kuwa akan abinda nake yi, domin ina shekarar karshe muka hadu da Faruq, wanda yake aikin koyarwa a jami'ar kasu, duk dai ban rasa manema ba, amma zuwan Faruq ya tsayar min da kome, haka na gabatar da shi a cikin gidan mu, babu b'ata lokaci manyan suka shiga maganar aka yi bikin mu.
 Da farko bani da matsala da Uwar mijina kasancewar, muna Kaduna ne su kuma suna Zari'a. A farkon auren mu gwaggo tana zuwa mana kwana biyu, ta koma idan zata koma shatara na arziki muke had'a mata, har zuwa lokacin da na Haifi Nuratu. 
     Ina goyon Nimrah na fara fuskarta matsala da Uwar mijina, domin a lokacin suna zuwa amma bana samun zama sosai.  Ina aiki yana aiki. Ba zan tab'a Mantawa ba, matar kanin shi me suna Laminu tazo biki Kaduna. Sai ta sauka a gidan mu, sosai na karɓe ta tare da mata hidima. Har aka gama bikin ta koma.  Ban san me ya faru ba, sai ga Gwaggon Faruq  tazo mana, duk yadda na karb'e ta bata sake ba. Da dare bayan ya dawo naji tana cewa.
"Wato dan kaine me dukiyar banza matar ka har tasan ta kwashi abincin ka ta bada wasu banza ni ba zata bani ba, har kayan yara da na sawanta ta kwashe ta bawa Basirah. Wato kai yan uwanka ba zasu more ka ba, sai yan uwan ka da kuke uban daya, ina laifin ta musu kyautar dan dai-dai, dai ta hada kaya himili guda ta basu."

    Haka tayi ta faɗa tare da nuna bata ji dadi ba, bayan yayi mata sai da safe yazo ya saka Ni a gaba da tambaya nayi kyauta da kaya ne,. Zuba mishi ido nayi domin ni dai ban yi kyauta ba.

 Yadda ya dage da maganar ne ya sani mik'ewa, na duba kayana kusan sha'anin ma'aikaci, wallahi ban san yadda aka yi matar nan ta shiga dakina ta min sata ba, ta kwashe min kaya da na Yarana, idan na gaya mishi sata ce ban san inda zancen zai tsaya ba, dan haka na nuna mishi yayi hakuri na manta ne. Ya ce min.
"Kin san halin gwaggo sai ki bata ya kaiwa Yar autarta."
          Haka dai muka bar zancen da ta kwana biyu zata koma na hada mata itama ta kai wa yarta da jikokinta.

Nasamu na kashe wannan rigimar, sai ga matar Fatihu,  tun da nasan basu da hankali. Sai na shiga rufe kofar d'akina, idan xan fita amma bai hana matar nan tafiya dani ba, wai tunda tazo bana zaman gida, idan na zauna bana sakewa da ita, abubuwa kala kala amma  nan ma gwaggo ta niko gari tazo,  haka ta sani a gaba da fada da rigima. 
A hankali abubuwa suka sauya bai saka gwaggo ta fahimci makircin matan gidan nan ba, bayan D'anta suke son gani ba, sai da muka tattaro gab zan yayye Amir muka dawo gidan..
 ....

Wani abinda na Fahimta a cikin gidan da muke shine basu damu da ibada ba, sannan basu da kamun kai, Ash'aria kamar maguzawan karshen karni.  Da farko da muka dawo abubuwan da sauki, domin idan kayan abincin mu yayi kasa ni ke cefane, mu taru mu rufawa juna asiri. Sai suka dauka ai kudin shine kai akwai zuwan da yayi gwaggo ta saka shi a gaba sai ya bata abinda yake kawo mana, wallahi babu kome, dan haka ya daina sayo kome yana kawowa, abinda yake kawowa bushashen kifi, sai kayan abinci miya kuwa ina da katon firiza a cikin shi nake ajiye miya idan nayi.  Sabida yarana suna Islamiyya yasa nake barin key a gida idan xan tafi aiki ashe ban tsira ba domin diban kayan abincin mu ake, shi yasa nan da nan abinci ya kare.

    Da sauri na raba abincin na zubawa gwaggo nata, sannan na zuba na cikin gida a ture, na mika musu gindin bishiyar maina, ina jin Safiya tana cewa.
"Dole a girka a bamu, arzikin Yayan mijin mu ne muci musha yadda muke so. Mace idan ta ki tafita a gidan kome kuka ce"
Dariya suka saka tare da shewa, sannan suka shiga zagina, bayan na gama aka ɗauki na mazan gidan aka kai kofar gidan. A gurguje nayi wanka ma shirya sannan na kira yar aikina. Yahanasu na ce mata.
"Ki zauna kina kula da su, Kinga aka ta mana sata. Ba zai yiwu na bar gida babu babba ba."
     Wayata ce tayi kara na duba, Honey.
Dauka nayi sannan nace mishi.
"Assalamu alaikum Honey"
"Kinga akan me zaki yi abincin nan kad'an? Gashi sai kirana ake wai kinyi abincin dan kaɗan idan kin san ba zaki nutsu kiyi girki ba, zaki ajiye aikin nan naki? Me kike bukata wanda bana miki? Kowa sai gaya min yake baki zaman gida, kina yawo da sunan aiki. Please bana son haka idan aikin zai shafi zamanin lafiyar mu ki ajiye ba gaji da kananun magana."
Wani abu ne ya tokare min kirjina, a hankali nace mishi.
"Kayi hakuri, Insha Allah zan kula kuma dama abincin ya kare, kuma na turo maka sakon baka gani bane nake ganin"
"Ya kike son nayi dake ne? Ke kenan kullum babu kullum ya kare, ina albashinki?"  A matukar gajiye da matsalar gidan Aurena yasani cewa.
" Yana nan"
"Toh daga yau zamu fara 50/50" ya fada min a hasale.
"Faruq, kasan ina da iyali da yan uwa. Akwai kanena da nake daukar nauyin karatun su, fa Baba da duk karshen wata nake kai shi asibiti don Allah karka min haka"
    "Na gama magana, na gaji da almubazzaranci" ya kashe wayar tare da jan tsaki.
     Had'iye kukan da yazo min nayi domin ban iya rama fada ba, shi yasa kullum nake kusantar bakin cikin gidan aure na. Haka na shiryar tare da kwashe kayan abincin na saka a daki har can ƙasar gado sannan na rufe gidan na fita. A kofar da zata fitar dani daga cikin gidan naji yan uwan shi maza suna faɗin.
"Ya samu mace me hakuri Mahaukacin banza duk abinda muka gaya mishi dauka yake, itama yarinyar duk abinda zaka mata bata tab'a gaya mishi, ga." Ganin na fito a hankali ban kalli inda suke ba, ina dauke da Amir yasa jikin su yayi masifar sanyi...

*Mu tattauna! Shin mata nawa suke fuskar irin wannan yanayin idan Allah ya kawo ki cikin jahilai! Gidan Aure Na ba kamar sauran Novels bane labari ne me nisan zango zaku iya bada gudummawar ku ta hanyar shawarwari da irin wannan lamarin yake faruwa dasu! Sannan zaku iya turo sakon ku ta wandanann Number domin labarin ba iya nan ya tsaya ba*

+234 708 416 1619 

Billy Galadanci
+234 703 809 7759

Aunty Safiya Jos
+234 906 528 2817

Maman Nana Insha Allah sakon ku zai iso...
Allah ya hadu wani makon cigaban labarin Sameerah

GIDAN Aure Na..!!?Where stories live. Discover now