*EWF*
GIDAN AURE NA
🎪🎪*Ƙarƙashin jagorancin Grps guda Huɗu! masarautan Mata 1/2. SBL TSK! EXQUISITE WRITERS FORUM.... Zai cigaba da zuwa muku kullum Insha Allah*
Labarin Sameerah.
Season 1
BABI NA UKUMai_Dambu.
_TAMBAYA SUKE WAI ZAI FARU KUWA? TAMBAYA SUKE WAI DA GASKE NE? HMMM! KOWANI GIDAN AURE YANA FAMA DA TASHI WUTAR IDAN ZAKA LEKA GIDA GOMA GUDA TAKWAS YANA CI DA WUTA! BIYU ZAKA SAMU DAYA BA LAIFI DAYA MANEJI AKE YI! IDAN NACE ZAN CIRO IRE-IREN WAƊANNAN ABUBUWAN WALLHI DAYAWA BA ZASU KUMA KARANTA LABARIN BA! JIYA NASO NA KARA PAGE D'AYA AMMA KASAWA NAYI DAYA DAGA CIKIN MASU BIN LABARIN TA BANI LABARIN DA YA SANYA NI KASA TABUKA KOME! WALLAHI KARSHE TINDA NA SAUKA A ONLINE ZAZZAƁI YA RUFE NI! BANA CE BABU MAZAN KWARAI BANE AMMA WHY! MACE TA GAMA SADAUKARWA DA RAYUWAR TA. TA GAMA BAKA KOME NATA TA GAMA YARDA DA KAI LOKACIN DA YA DACE TA HUTA A JIKIN TA ZAKA CE BATA ISA BA! TAYA MACE ZATA GAMA FAFFUKAR RAYIWA KAN KA KACE BATA ISA TA MORE KA BA, SAI WATA? BA WAI FADA NAKE AKAN KISHIYA BA, AMMA MAFIYA AKASARI SAI MACE TA GAMA CIN WAHALA DA NAMIJI SAKAMAKON DA ZAI MATA LOKACIN SHINE KISHIYA... HMMM MUJE ZUWA MAHAUKACI YA HAU KURA_
Sake kayan Hannuna nayi tare da zubawa yaron ido yana nishi. Daga abin da yayi cikin shi zuwa cinyoyin shi, ya sabule kamar kazar da aka wurgata cikin ruwan zafi iya gwiwar shi ce bata tabu ba,yayi goho yana nishi.
Sannan an barshi a tsakar gida,yara sai zagaye shi suke suna faɗin.
"Ai Salele kai ka tura shi a ruwan zafi kuma iyar ka tana gani."
"Aunty" yahanasu ta kira ni, binta nayi da ido, ina kallonta.
"Muje ciki" ta kwashe kayan ta shiga da shi. Ina tsaye akan Yaron.
"Ki rufe kofar kizo muje"
"Su Nimrah da Nuratu da?"
"Asibiti zamu" na bata amsa bayan na shiga cikin dakina na dauko babban ledar. Na dauke shi cak na daura a ledan sannan muka fita. Muna zuwa asibiti. Aka rufe ni da fada, sai lokacin na samu damar fashewa da kuka.Ina nawa kukan akan yaro na,gefe na fada ake da wani mutum. Ban san lokacin da na had'iye kuka na ba, ina kallon su.
"Ai nace karta kuma ɗaukar ciki! Sannan wannan shine karo na biyu da take haihuwa ace sai na bada jini na, gaskiya ba zan bada jinin ba" kallon shi nake.Dr Muddam cikin jin haushi yace mishi.
"Idan baka son ta haihu ai sai ka zo a datse hanyar da yake zuba maniyyin a cikin ta, ai akwai family plan na maza. Tunda kai baka son haihuwa." Aikuwa yayi tsaye ya dira. Tare da cewa.
"Me? Wallahi bata saɓuwa akan me? Ba zai yiwu ba, haihuwarta shida ba zan lamunci karin da daga gare ta ba, dan ina da wata matar da bata haihuwa. Dan bakin ciki sai tara yara take tana min fatar na mutu su ci gadona, haka mata na ta gaya min shi yasa bata gajiya da ɗaukar ciki."Mik'ewa nayi tare da barin wurin, kar bakin cikin maza ya kashe ni, a bakin Sister Lubna naji labarin karshe bai ba da jinin ba sai yan uwan matar ne suka bada, tare da cewa sai sun kai shi kotu ta raba auren. Amma kusan me matar tace? Cewa tayi ita don Allah kar a raba ta da mijinta tana son shi. Sannan idan suka rabu ina zata kai Yaran ta, sannan ita kawai zata yi zaman Yaranta. Sunkuyar da kai nace a raina.
*Kamar ni itama tana son mijinta, tana son yaranta kuma tana bukatar Yanci! Amma mun yi tarayya akan son da namiji shi zai kashe mu*(Ban ce mazan arewa basu da tausayi da imani ba, amma maganar Gaskiya yana faruwa fa. Ba wai karya ne ko kirkiran labari ba kawai dai daidaiton ra'ayi aka samu... Allah kasa mu dace)
YOU ARE READING
GIDAN Aure Na..!!?
General FictionLabari ne da ya faru a gaske labari ne ta ya tab'a kowani shashi na rayuwar matan aure yan mata zawarawa, da sauran su( BASE OF TRUE LIFE STORY) KUMA SERIES NOVEL NE