BABI NA BIYU

701 67 2
                                    

https://www.wattpad.com/1141965583?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
*EWF*
GIDAN AURE NA
              🎪🎪

*Ƙarƙashin jagorancin Grps guda Huɗu! masarautan Mata 1/2. SBL TSK! EXQUISITE WRITERS FORUM.... Zai cigaba da zuwa muku kullum Insha Allah*

Labarin Sameerah.
Season 1
BABI NA BIYU

Had'iye b'acin rai na nayi tare da kallon su ina mamakin yadda suka zama munafukai, duk da ban san me yasa suke son ganin sun shiga tsakanin mu ba. Dan haka na tsaya sai da na tari napep na fada mishi sunan asibitin da nake aiki.

    Ina shiga na dauke kaina, sai lokacin kwalla ya cika min idanuna. Had'iye kukan nayi domin har Amir ya fara kallona yana faɗin.
"Ammy kuka ne?"
Girgiza mishi kai nayi sannan nace mishi.
"Idanuna ne ke ciwo"
Ajiyar zuciya ya sauke yana wasa da hannun shi a bakin shi. Duk da ni din ba wata kyakyawa bace kasancewar ruwa biyu suka samar dani amma Alhamdulillahi ina da kiran jiki me kyau da ɗaukar hankali. Lokacin kafin nayi aure har saka nikkab nake sabida maza da suke damuna.

        "Hajiya mun iso" me napep ya katse min tunanina, a hankali na fito tare da bashi kudin shi sannan na dauki Amir.
"Ammy doki" ya fada yana juyawa saboda ganin doki ya wuce mu, murmushi nayi domin nasan yara ba a rabasu da son irin wannan abubuwan.

     Ina shiga na hadu da abokan aikin mu da suka gama aikin safe.
"Sister Sameerah, mun barki lafiya"
"Kai Aaliyah babu tayi ne kamar jira kuke nazo?"
"Hmm! Tun safe muke nan dan rashin kirki kice wai ba tayi na rantse ina komawa gida fadawa gado zan yi sai nayi barci na tashi sannan zan ci abinci."

"Ayya saboda baku da iyali ne shi yasa." Murmushi suka min tare da cewa.
"sister Sameerah kema ki dan nake ce kika gayawa mutane kina da Nuratu da Nimrah ba, wallhi kowa ya ganki Amir kawai zai dauka shine baby"

   Dariya nayi sannan na zauna ina duba abubuwan da suka bari.
"Ko zaku min bayani akan marasa lafiyan?"
"Ok!" Suka ce sannan suka shiga min bayani har suka kai ni dakunan kafin na dawo na cigaba da abinda nake su kuma suka tafi.  Ina ƙoƙarin hana zuciyata karaya akan Baban Nuratu, amma na kasa hakuri taya zai sauke min hakkin shi bayan wanda ya sauke. Dan haka na had'iye kukan da nake ji. Na cigaba da kiran Allah ya kawo min ɗauki.

  Kaduna.

Kallon shi Muktar yayi tare da sake baki.
"Ban gane dawa kake magana ba?" Ya fada cikin rud'ani,
Cikin takaici kamar ya bangaje Muktar din yace mishi.
"Waye ban da Sameerah, ban tab'a ganin almubazzaran mace irinta ba, kasan yadda take min barna da abinci, yanzun ma."

"Look young Man! Matar kace almubazzara? Wai Sameerah Abdullahi Anchau ce kake zagi da almubazzaranci? Yarinyar da ka shiga ka fita ka aureta? Ko ba uwar Yaran ka uku ba? Toh yayi kyau." Inji Muktar,
Zai bude baki wayar Faruq tai kara, dubawa yayi yaga Jafar kanin shi da suke Uba daya.
"Lafiya Jafar?"
"Lafiya lau! Yanzun don Allah yaya a matsayin ka na me rufin asiri meye yasa zaka bar Sameerah zata yi aiki? Ai wannan rashin godiyar Ubangiji ne da nuna mana cewa ita din kabila ce, musu nima ana zagin mazajen su." Magana marasa dad'i da ma'ana yayi ta gaya mishi. Shi kuwa ya cika fam, sai wuce yake.

    Nan masoyin shi na gaskiya ya yaba da kokarin shi,  sai da ya bari Jafar ya gama magana sannan ya fara da cewa.
"Dole ya ajiye aikinta, domin ni ba sakarai bane. Ina aiki matana tana aiki cikin isa da gadara"

       Sai da ya gama kumfar bakin shi sannan ya kashe wayar ya shiga bawa Muktar labarin da Jafar ya gaya mishi.
"Kuma kasan har night duty tana yi, waye yasan me suke aikatawa a.."
"A'a Faruq! Karka fara karka lalata auren ku, tsakaninka da Allah baka same ta da mutuncinta ba?" Sunkuyar da kai yayi tare da sosai goshinsa.
"Amma dai Muktar ai kasan"

GIDAN Aure Na..!!?Where stories live. Discover now