BABI NA BAKWAI

492 55 9
                                    

https://www.wattpad.com/1144299818?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AfricanQueen300&wp_originator=RMXxwZzgiCAsUTo5Q%2FII%2BvA52dvn12SlY7m4ZQIa4yuCr5IzNxwsg5D0XVyipwj25AfVrinQlbkO3uB4MWrclS669a8K%2FZJb%2Bb8e7E6PPadZIfvnVSNco4pSCTX%2Fppjr

*EWF*
GIDAN AURE NA
🎪🎪

*Ƙarƙashin jagorancin Grps guda Huɗu! masarautan Mata 1/2. SBL TSK! EXQUISITE WRITERS FORUM.... Zai cigaba da zuwa muku kullum Insha Allah*

*Wannan shafin godiya ce ga mutanen da suka sadaukar da lokacin da kome nasu suka bibiye Shafin labarin baki daya nagode!*
    *Of course, every time you are challenged to look after your own interests in the community, God will sprinkle. Thank you.*

Labarin Sameerah.
Season 1
BABI NA BAKWAI.

Fitowa nayi da keken tare da wasu abokan aikana biyu,muna nufi motar shi, fitowa yayi ya fara kallona, sanan ya bude motar ya ciro Gwaggo.
"Subhanallahi! Meye ya same ta?"
"Ku kai ta ciki tukun" ya fada, ban iya motsi ba, na kafe shi da ido,
"Lafiya meye ya same ta?"
"Ban sani ba, sai dai ina wurin aiki aka kira ni"
"Toh yanzun me zan mata?" Na tambaye shi.
"Ki duba ta" ya fada tare da shafa kan shi.
"Hm! Haka zan duba ta kawai?"
"Toh wallahi ban fito da kudi ba, da na fito da shi ba zanzo nan na kawo miki ita ba"
Murmushi nayi domin ya bani dariya, kafin nace mishi.
"Na rantse da Allah,kamar yadda ka kawo ya, haka zan mai da ita gida, na gaya maka gaskiyar abin da zan aikata ne, bani da kudi. Kuma bani da wanda zai dauke min nawa hidimar balle na dauki na Mahaifiyar ka, dan haka duk abin da ka ga yayi maka kayi amma wallahi ba zan kula da ita ba, bani da shi."

"Ikon Allah! Meerah yaushe kika zama mara imani? Toh nagode ai ko dan albarkancin Yaran da ke tsakanin mu zaki amshi Mahaifiyata, balle kuma akwai aure da zumuncin, Ni kika tozarta" Ya nuna kan shi.. ban wani damu ba, na dauke kaina ina kallon kasa, shiga motarshi yayi sai gashi da dubu biyar ya mika min.
"Nawa ne?"
"5k"
"Hmm! Jeka dauki Mahaifiyarka" na gaya mishi, kamar zai karamin hauka, haka ya shiga motar ya ciro kudin ya kara min naki karb'a tare da cakka mishi bakar magana.
"Mahaifiyar ka ce ba tawa ba, idan ka barta haka zan barta" karshe haka ya koma ya ciko dubu goma akan sha biyar din sannan na amsa na ce mishi.
"Allah ya kyauta, idan kudin bai isa ba, kwandala ba zan kara maka ba" na juya abu na. Mamaki ne ya kama shi yaushe Sameerah ta zama mara mutunci haka? Lallai zai ji da ita.

    Ko sallama ban mishi ba na dawo cikin asibitin muka shiga dawainiya da ita, karku manta kawai maganin da drip din da za a saka mata Wallahi ya kare a dubu goma sha biyar ban da allurai da sauran su, haka na tab'a na hannuna, dama da ciwon a jikinta ban san me ya kuma tadda shi ba, amma akwai damuwa sosai wanda shi yayi sanadin hawan jininta sosai. Sai ciwon suga da aka gano, can asibitin da aka fara kaita basu kai da saka mata ruwa ba,aka kawo ta nan. Badan akwai likita ba da yace a duba ta tukun kafin a saka mata drip da tabbas abinda zai faru Allah kaɗai ya sani.

  Bayan na gama na koma gida, na nufi tsakar gidan inda suke ajiye chamber su, nace musu.
"Toh Gwaggo tana asibiti, ko zaku kira Hadiza tazo ta zauna" ina fadar haka na wuce abin na,
"Ikon Allah! Yaushe ta dawo daga Kadunar?"
Ina nasan lokacin da zan basu amsa na Barsu a wurin suna lugudan lebe.

     Abinci nayi tare da Yarana, na zuba mana a tire guda, muka fara ci. Ina gamawa na nufi ban daki nayi wanka kasancewar ina Off, bayan na idar na shiga cikin Yarana na musu home work. Abu daya da na Fahimta, shine naki ma sake haukar namiji ya hanani bawa Yarana kulawa, naki bada wannan damar da zan saka damuwar shi ta hana yarana samun damar nutsuwa, shi yasa na rike su hannu bibbiyu, sune farin cikina.
"Ammyn yaushe Abba zai zo? Kullum sai kice yana aiki yana aiki gashi ya daina zuwa weekend?" Inji Nimrah da ta fi Nuratu yawan magana.
"Zai zo mana, kawai yana wani aiki ne idan ya gama zai zo"
"Toh".ta faɗa na zata maganar ta kare a'a ashe wani tambayar ta kuma hado min ta ce min.
*Me yasa baya kiranki a wayarki?"

GIDAN Aure Na..!!?Where stories live. Discover now