*EWF*
GIDAN AURE NA
🎪🎪*Ƙarƙashin jagorancin Grps guda Huɗu! masarautan Mata 1/2. SBL TSK! EXQUISITE WRITERS FORUM.... Zai cigaba da zuwa muku kullum Insha Allah*
Labarin Sameerah.
Season 1
KARSHEN LABARIN SAMEERAH
BABI NA GOMABan san me ta gaya mishi ba, amma na ga ta dawo tana share kwalla, sosai ban takura kaina na ji meke damun ta ba, domin a tunanina matsalar ta ya dawo kamar da ne, bayan kuma ita tayi sanadin da ya koma haka, idan har dae uwa ta gari ce ba zata b'ata alakar mu dashi ba, amma haka tayi ta cusa mishi k'iyayyata da shima kan shi bakin shi ba kanin kafar shi ba.
Haka dai rayuwar ta cigaba, gaskiya na fara gajiya da zaman Faruq, domin zuwa lokacin ina samu sosai. Toh girma nake lokacin da ya dace na sami mijina babu wannan damar a tare dani, dan haka ban boye mata ba. Na same ta a d'akinta. Bayan na gaishe ta. Shiru ne ya ratsa tsakanin mu, kafin na kalle ta na ce mata.
"Gwaggo dama akan Baban su Nuratu ne nazo nan niman Alfarma. Don Allah" tashi tayi zaune tare da kura min ido, kafin tace min.
"Ba dai wani abu kike nima ba?"
"Eh Gwaggo saki nake bukata, a kwai cutarwa a zamantakewar mu, ina tsoron fushin Allah akan shi, idan bani da aure zai fi min sauki na rayu cikin sallama da ace ina da aure babu kwanciyar hankali,don Allah ki mishi magana a matsayin ki na Uwa ya turo min da takardan sakina."Ta zata wasa nake mata, sai da taga na kafe lallai sai ya rabu dani. Domin kusan kwana biyu na dauka tare da had'a kayana, ban tab'a yaji ba, amma wannan karon na shirya rabuwa da Faruq, baki daya gidan suma sai da suka sha jinin jikin su. Abin da Mommy ta gaya min kenan lokacin da na gaya mata abin da Faruq yake min,. Ta ce min.
"Yanzun kin zo ne na kashe miki aure ko me? Abin da kike bukata a sassantaki da mijinki shine abin da yake ranki, ba wai kin gaji da halin shi ba, lokacin da zaki gaji da halin shi ba zaki iya sauraron kowa ba, domin ita mace ba a koya mata yadda zata rabu da mijinta.Ita tasan hanyar da zata bi ta rabu dashi."Dan haka duk wanda yayi min magana, idan na gaya mishi na bakina bana kuma bin takan shi. Mota na nima wanda zai kai ni har gida da Yarana dama sun gama exam. Ganin haka sai gashi yazo min a yadda nake bukata,baki daya yan uwan shi da sauran makotar mu sun yi mamakin yadda na kafe, dan haka suka kira shi bayan mun bar zari'a, aka gaya mishi.
Da farko ya fusata ya ce.
"Ta tafi sai me, zan tura mata sakinta nima na gaji da halinta" kuji fa wai ya gaji da halinta, kuma babu wani abin da tayi mishi kawai zunzurutun mugun hali ne.*
Tunda na koma gida Baba da kan shi yaje har wurin aikin shi yayi mishi magana. Babu kunya Faruq ya ce zai zo min da sakina ya gaji shima.
Ina zaune Baba ya dawo ta gaya min abin da ya faru a tsakanin mu, sai da nayi kuka domin na kara fahimtar Faruq ya rena min iyaye ne, dan haka Baba da kan shi ya tafi ya nima min canjin wurin aikina zuwa kaduna, Yarana kuma ya nima musu makaranta na cigaba da kula da su,. Ina zaune har bayan wata biyu sannan Faruq ya aiko min da takardan sakina.Ban yi mamaki ba, amma kuma nayi kuka kamar zan mutu, haka na rike ƙaddarata hannu bibbiyu, na kuma yi hakuri na rungume Yarana, ina kula dasu, haka rayuwa ta cigaba har Nuratu ta gama Primary school zata secondry school, Nimrah na Class six, Amir yana primary one,
Rayuwa da ayyukata na saka a gaba na, bani da lokacin kowa sai na kaina,abu biyu dama ya hana Ni rabuwa da Faruq na farko ina tsoron kar na rabu da shi na kama zawarci,na biyu ina son shi da Yayana, haka yasa ni kasa rabuwa da shi,sai gashi yadda na kalli Fuskar zawarci ba haka yake ba.
Yadda na kame kaina da mutuncina yasa Allah ya dube ni da idanun rahama ya had'a ni da Dr Abdulkarim Funtua, likitan a asibitin da nake aiki yake shima, ya addabi rayuwata, ya dame ni ya kuma hanani sakat, amma kunsan me? Har yau zuciyata tana gurin Faruq, koda ya rabu dani ina jiran shi ko zai juyo gare ni.
YOU ARE READING
GIDAN Aure Na..!!?
General FictionLabari ne da ya faru a gaske labari ne ta ya tab'a kowani shashi na rayuwar matan aure yan mata zawarawa, da sauran su( BASE OF TRUE LIFE STORY) KUMA SERIES NOVEL NE